BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Bayanin Jagora Dangane Da Wasiyyar Annabi Ga Imam Ali (a.s)
Shinfida: Abin da ke biye sharhi ne da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi wa daya daga cikin wasiyyoyin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wa Amirul Muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s). Jagoran ya yi hakan ne a lokacin da yake gabatar da darasin 'Bahasul Kharij' ga wasu daga cikin dalibansa a ranar lahadi 19, Satumban 1999:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Muhammadu tare da Alayensa tsarkaka, kuma la'anar Allah ta tabbata ga makiyansu gaba daya.
Da farko dai kamar yadda muka saba, bari mu karanto wani hadisi, saboda insha Allahu mu sami albarkacin da ke cikin koyarwar Ahlulbaiti, amincin Allah ya tabbata a gare su.
Daga cikin Wasiyyar Annabi ga Amirul Muminin, amincin Allah ya tabbata a gare su (yana cewa): "Ya Ali, hakika daga cikin yakini", wato daga cikin abubuwan da suke tabbatar da yakini shi ne "Kada ka taba yardar da wani (faranta wa wani rai) ta hanyar fusata Allah, sannan kuma kada ka taba gode wa wani mutum kan abin da Allah Ya ba ka". Wato lalle kada ka dinga daukan wani a matsayin wanda ya baka abin da Allah Ya ba ka shi, ballanta ma ka je ga batun gode masa. "haka nan kuma kada ka zargi wani saboda abin da Allah bai ba ka shi ba", wato dangane da abin da Allah bai ba ka shi ba, to kada ka sanya laifin hakan ga wuyan wani, sannan kuma kada ka dinga zargin wani cikin abin da Allah bai ba ka shi ba. "Don kuwa doki da kula ba sa janyo arziki", wato babu wani doki da kula daga wajen wani mutum da zai iya janyo masa arziki. "Sannan kuma kiyayyar wani makiyi ba za ta kawar masa da shi ba", wato haka nan kuma kiyayya da kyamar wani makiyi ba za su iya kawar wa wani mutum da arzikin (da Allah ya ba shi) ba. "Hakika Allah da hikima da falalarsa, Ya sanya farin ciki da kwanciyar hankali cikin yakini da yarda", wato Allah Madaukakin Sarki Ya sanya kwanciyar hankali da rayuwa da farin ciki cikin yakini da yarda ne. Idan har mutum ya sami nasarar tsamar da kansa daga yanayi na tsoro da shakku na ruhi da kuma bakin ciki cikin rayuwarsa sannan kuma ya kai ga matsayi na samun yarda da kwanciyar hankali, to kuwa Allah Madaukakin Sarki zai sanya masa ruhin farin ciki da kwanciyar hankali. "Sannan ya sanya damuwa da bakin ciki cikin shakku da rashin yarda" (Tuhaful Ukul, shafi na 6). Wato a bangare guda Allah Madaukakin Sarki Ya sanya damuwa da bakin ciki da makamantan hakan cikin shakku - wato kishiyar yakini da rashin tabbas - da kuma rashin yarda - wato fushi cikin dukkanin lamurra -. Irin wannan mutumin, idan ma Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi wani alheri, to kuwa zai ci gaba da zama cikin fushi yana cewa mai ya sa bai ba shi da yawa ba; idan kuwa wani mummunan abu ya same shi, zai yi fushi cewa mai ya sa hakan ya same shi. A saboda haka don samun farin ciki da kwanciyar hankali, wajibi ne mutum ya yi kokarin samun yakini da yarda da amincewa.
A yau kafin mu fara bahasin mu na fikihu, da yake wannan lokacin ya yi daidai da lokacin bude makarantun hauza da fara karatu a Kum da sauran makarantun hauza, don haka ina ga akwai bukatar in dan fadi wasu jumloli dangane da lamurra masu muhimmanci da suka shafi makarantar hauza da kuma yin ishara da abubuwan da ya shafe mu, mu dalibai:
Daga dukkan alamu gwargwadon yadda muhimmancin addini ya karu a duniya, to kuwa gwargwadon yadda muhimmancin makarantar hauza zai karu. A yau addini ya zamanto abin jan hankulan al'ummomin duniya. A yau addini ya zamanto abu mai jan hankulan 'yan siyasa, masana, kwararru a fagen ilmummukan zamantakewa da kuma mafi yawa daga cikin mutane musamman ma matasa a mafi yawa daga cikin kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi, wato addinin Musulunci da koyarwar sa mai tsarki. Ko shakka babu mafi yawa daga cikin lamurran da suka faru cikin shekarun goma zuwa ashirin na baya-bayan nan a bangarori daban-daban na duniya, wadanda kuma ba a taba tsammanin faruwarsu ba, suna da alaka ne da nasarar da addini da kuma Musulunci ya samu a wannan kasa da kuma kafa gwamnatin Musulunci da aka yi (a Iran). A saboda haka ne a yau dukkanin binciken da ake gudanarwa dangane da addini a dukkanin fadin duniya za a cewa suna da alaka ne da bangaren siyasa na addini; ba sa ganin addini a matsayin shi kadai ba tare da tasiri na siyasa ba sannan kuma dukkanin matsayar da suke dauka suna daukan su ne bisa wannan asasi. Kamar yadda kuma za a iya ganin cewa zukatan da suka koma ga bangaren addini - a matsayin misali matasan duniyar musulmi da sauran yankuna na daban na duniya - irin addinin nan da babu ruwansa da siyasa da zamantakewa ta al'umma ba ya burge su.
Ana iya cewa a yau mun kasance cibiyar da dukkanin duniya take kallon mu. Ana iya cewa Musulunci ko kuma a takaice Jamhuriyar Musulunci, sun zamanto tushen da aka sanya musu ido. Mai yiyuwa ne kun ji ko kuma kuna da labarin irin tarurrukan kara wa juna sani da masana masu akida da fahimta daban-daban suke gudanarwa a duniya - musamman ma a kasashen da ba sa dasawa da Musulunci da kuma Jamhuriyar Musulunci - saboda binciken wannan lamari. Hakan yana nuni da irin muhimmancin da wannan lamarin ya ke da shi ne.
Mu din nan a yau a matsayin mu na mutanen da suke da alaka da makarantar hauza, bisa la'akari da wannan lamari, wajibi ne mu sake dubi cikin halayenmu na ilimi cikin bahasi na Musulunci da muke gudanar da kuma gabatar da wasu sabbin tunani. A lokaci da muka ga irin yadda duniya ta ba wa wani ilimi - wato ilimi na Musulunci, ilimin akida da fikihu na Musulunci - wanda ya samar da wani sabon yanayi a fagen siyasa na duniya, to wajibi ne mu kara irin tunanin da muke yi; wajibi ne mu kara taka tsantsan, sannan kuma mu sake sabon lissafi cikin ayyukan mu a matsayin mu na ma'abota ra'ayi na addini sannan kuma malaman addini.
A yau ba lokaci ne da za mu bude bakunanmu da sunan addini da kuma harshe na addini mu dinga fadin wasu maganganu marasa tushe ba, ko kuma mu tsara wata manufa wacce ba za mu iya samunta cikin koyarwa ta Musulunci ba, ko kuma a daya bangaren mu zamanto 'yan ba ruwanmu cikin manufofi na addini da lamurra masu muhimmanci na fikihu da akida ba. Babu wata bukatar na mu damu kanmu da neman wannan sabuwar hanyar da babu ilimi cikin hakan ba. Idan har muka takaita da abin da kowane malami zai takaita da shi, da kishi na malanta cikin bahasi na Musulunci - baya ga akida, imani da sauke nauyin da ke wuya - da irin wannan kishi da kuma abubuwan da suka dace da ayyuka na ilimin da muka yarda da shi, sannan kuma muka ci gaba da riko da abubuwan da muka fahimta daga Musulunci da kuma yada shi da sunan Musulunci, to hakan ma ya wadatar.
Ko shakka babu cibiyar da za ta gudanar da wannan aiki ita ce makarantar hauza. Ba wai ana cewa ne mutanen da ba 'yan hauza ba, ba su da hakkin su yi tunani cikin lamurran da suka shafi Musulunci ba ne, a'a, bahasin ba na hakki ba ne; to sai dai abin da ake cewa shi ne babu wani wajen da za a iya samun abin da ake bukata wajen tabbatar da hakan idan ba makarantar hauza din ba. (A matsayin misali) Kowane mutum yana da hakkin ya zama likita, to amma don zama likita wajibi ne mutum ya tafi jami'ar da ake karantar da ilimin likitanci. Babu yadda za mu iya tafiya wani wajen da babu malami da kuma cibiyoyin gwaji sannan mu ce muna neman ilimin (likitanci) a can. A saboda haka wajen fahimtar addini, wajen gudanar da tunani na addini, wajen kutsawa cikin lamurra na addini, ita ce makarantar addini (hauza). Ko da yake mai yiyuwa ne kowane mutum ya iya samun wani matsayi na kasa-kasa na ilimin addini, to amma dangane da samun kwarewa kan, wajibi ne a tafi makarantar hauza da zama a gaban masana da kwararru na addini don a koya daga wajensu.
A bangare guda kuma wajibi ne makarantar hauza ta zamanto mai amsa bukatun mutane. A yau muhimmancin makarantar hauza bai tsaya kawai wajen isar da sakon addini ba - duk da cewa hakan daya ne daga cikin manyan ayyuka kuma masu muhimmanci na makarantar hauzar - face dai wani abin da ya fi hakan muhimmanci ko kuma alal akalla suke tafiya kafada da kafada shi ne karantar da ilimi da tushe da kuma koyarwa ta addini; da suka hada da fikihunsa, akidarsa ko falsafarsa da sauran ilummukan da suke bukatar a koye su. A saboda haka a kowace rana muhimmancin makarantar hauza da muhimmancin malaman addini da masu karantar da ilmummuka na addini da muhimmanci aiki da kokarin da daliban addini suke yi su na ci gaba da karuwa. Ko da yake dangane da cewa wani bahasi ne ya wajaba a ba shi muhimmanci a makarantar hauza, to mu dai a lokuta da dama mun sha fadin abubuwa; a yanzu ma zan kara fadi: tushe na asali a makarantar hauza da farko dai shi ne fikihu; na biyu shi ne akida sannan sai falsafa. Fikihu shi ne tushen makarantar hauza; ilimin akida, wani reshe ne na asasi na makarantar hauza, falsafa ma tana a matsayin wani bangare na wajibi na makarantar hauza. Wajibi ne kwararrun malamai da kuma dalibai su zamanto sun koyi wadannan bangarori uku na ilimi sannan kuma su ci gaba da gudanar da ayyukan su da kyau a wannan fagen. Ala kulli hal ba za a iya takaita da wadannan abubuwa kawai ba; wadannan dai su ne tushe na asali; a gefen su kuma akwai wadansu ilmummuka na daban wadanda wajibi ne a koye su. Wajibi ne a karanci ilimin tafsiri; ilimin Usul wanda zai zamanto a gefen fikihu, a matsayin wani matakin farko na wajibi, shi ma wajibi ne a kula da shi. Haka nan kuma wajibi ne a karanci ilmummuka daban-daban irin su hadisi da ilmul rijal da dukkanin abubuwan da za su taimaka wajen fahimtar Alkur'ani da hadisai. Baya ga wadannan kuma wajibi ne a fahimci fannoni daban-daban na isar da sakon Musulunci.
A yau isar da sakon addini, wani bangare ne na ilimi. Ilmummukan sadarwa wadanda a yau ake ta kokarin samar da su a jami'oi, a hakikanin gaskiya hanya ce ta sadarwar isar da sako. Mu dai muna da hanyoyin isar da sakon mu na gargajiya ta hanyar magana da kulla alaka da mutane wanda kuma hanya ce mai kyau; to sai dai kuma hakan ba ta wadatar ba. Ni dai ba ina kiran dalibai da su tafi su koyo ilmummukan sadarwa ba ne; face dai ina so ne in jaddada cewa masu gudanar da makarantun hauza, bisa la'akari da sakamako na ilmummukan sadarwa, su tsara ayyukansu sannan kuma su sanya wani bangare na bahasin da suke yi kan abubuwan da makarantar hauza take bukata sannan kuma su gabatar da hakan ga masu bukata - musamman mutanen da suke gudanar da ayyukan isar da sako.
Haka nan kuma fahimtar tunani da abubuwan da ke gudana a duniya, suna daga cikin abubuwan da suka zamanto wajibi a makarantar hauza; idan kuwa ba a sami hakan ba to ba mu da tabbas din cewa abubuwan da muke yi da kuma matsayar da muke dauka dangane da lamarin isar da sako, za su kai ga sakamakon da ake son cimmawa. Idan har ba mu zabi mutanen da za mu yi magana da su ba sannan kuma ba mu fahimce su ba haka nan kuma ba mu san irin yanayin tunanin su ba, to mai yiyuwa ne mu fadi wani abin da ba zai dace da kwakwalwarsu ba sannan kuma ba za su iya fahimtarsa ba. Wato za mu gudanar da aiki ne na baban giwa. Wajibi ne a fahimci wadanda ake magana da su sannan kuma a zabe su. Zai yi kyau idan wadansu mutane suka sami damar kulla alaka da masu saurare na musamman, wasu mutanen kuma su sami alaka da wata al'ummar ta daban. Wajibi ne a zabi wadanda ake magana da su; wajibi ne cibiyar gudanarwa ta makarantar hauza ta gudanar da ayyuka da kuma tsare-tsare a wannan fagen. Wajibi ne a fahimci wadanda ake magana da su da kuma irin tunaninsu. A yau dai akwai sabbin shubuhohi da matsaloli da ake gabatarwa a duniya; wasu daga cikinsu kuwa suna da tushe na ilimi ko kuma abin da ya yi kama da ilimin. Wadanda suke son su gudanar da aikin isar da sakon Musulunci, su yi bayanin ra'ayin addini ko kuma su kare addini - don kuwa ba a ko da yaushe ne ake kariya din ba; wasu lokutan bayani ake yi - to wajibi ne su san mene ne irin wadannan tunani da kuma wadannan sabbin maganganu da ake fadi. Wannan fahimta wajibi ne ga makarantar hauzar mu.
Ko da yake wajibi ne ma daliban mu su zamanto sun koyi rayayyun harsuna (yarurruka) na duniya, ko kuma alal akalla sanin daya daga cikin fitattun yarurrukan duniya yana daga cikin lamarin da ya ke a matsayin wajibi ga wani dalibi na addini sannan kuma wajibi na aikinsa. Wajibi ne a samar da hakan a makarantar hauza. Alhamdu lillahi mafi yawa daga cikin daliban (hauza) matasa ne, karfin koyon yare a wajen su yana da girman gaske. Wajibi ne insha Allahu a samar da hakan a makarantar hauza.
Bahasin abubuwan da suke kusata mutum da Allah shi ma bahasi ne mai muhimmancin gaske. Babban bambancin mu da masu ikirari na duniya shi ne cikin wannan manufa mai tsarki. Mu dai muna so ne mu yi kokari da gudanar da ayyukan mu saboda Allah, saboda addinin Allah, saboda neman yardar Allah da kuma daukaka kalmar Allah. Daga lokacin da muka fara karatu har zuwa ga lokacin da za mu tafi isar da sako, har zuwa ga lokacin da za mu dinga karantarwa, har zuwa ga lokacin da za mu rike wani nauyi a makarantar hauza ko kuma a wajen makarantar, to wajibi ne dukkanin ayyukan da za mu yi, shin ayyuka ne na siyasa ko na zamantakewa ko kuma na ilimi, wajibi ne manufarmu ta zamanto ita ce wannan. Wannan shi ne abin da zai sanya mu samun nasara, sannan kuma maganganun mu su zamanto masu tasiri da zama cikin zuciya. Wajibi ne mu dauki hakan a matsayin wata farilla a wajen mu.
Ko da yake a yau din nan da nake magana da ku, an aiwatar da ayyukan masu kyaun gaske a makarantar hauza a dukkanin wadannan fagagen da na fadi din - musamman a makarantar hauza mai albarka ta Kum - an gudanar da wadannan ayyuka. Tazarar da take tsakanin yau da shekarun da suka gabata; lalle tazara ce da za a iya ganinta; akwai darussa na kyawawan halaye, akwai darussa na tafsiri, akwai darussa na falsafa, akwai darasin isar da sako, haka na akida, akwai kuma mujallu na ilimi da suka shafi kwarewa. Wadannan abubuwa ne da muka kasance muna kira da a samar da su, muna gabatar da su a matsayin fatan da muke da shi, a hankali a hankali ana ci gaba da tabbatar da hakan. Hakan ma dalili ne da ke nuni da cewa abin da muke gabatar da shi a matsayin fata, ba fata ne da ba za a iya cimma shi ba; ayyuka ne da za a iya gudanar da su ba tare da wani kashe kudi na a zo a gani ba, sannan kuma ba tare da wani kokari sosai, ana bukatar himma ce ta wadansu mutane kawai da suke son yin himmar. Kamar yadda alhamdu lillahi a yau kuke ganin a garin Kum - a matakin farko - da sauran makarantun hauza na daban, an riga da an aiwatar da hakan. Dukkanin wadannan manyan ayyukan da muke tunanin cewa wajibi ne a samar da su a hauza, lamurra ne da za a iya aiwatar da su da kuma cimma su; amma da sharadin cewa akwai himma a tattare da ni da kuma ku.
Wassalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu.