A Nijeriya, dubun-dubatar magoya bayan Harkar Musulunci ne suka hau kwalta a cikin babban birnin Tarayya, Abuja suna masu kira ga Gwamnatin Buhari da ta gaggauta sakin Jagoran Harkar ta Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda take tsare da shi tun tsawon shekaru biyu da suka gabata.
Ministocin harkokin waje ashirin da biyu da ke wakiltar kasashen Larabawa sun nemi Amurka ta janye matakin da ta dauka na daukar Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya ja kunnen Amurka dangane da batun mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Qudus yana mai cewa wajibi ne kasashen musulmi su hada kansu waje guda don tinkarar wannan lamari.
Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin halitta tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi (s) da Iyalan Gidansa (as) tsarkaka. Yau Allah ya nuna mana ranar da muke tuna haihuwar malaminmu Sheikh Muhammad Turi dan haka ku kasance cikin wannan post.