Insane
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
Code:

Nesantar Son Zuciya

Ali Khamenei2

Manzon Allah (s.a.w.a) yana
cewa:-
ﻣﻦ ﺃﻛﻞ ﻣﺎ ﻳﺸﺘﻬﻲ ﻭﻟﺒﺲ ﻣﺎ ﻳﺸﺘﻬﻲ ﻭﺭﻛﺐ ﻣﺎ ﻳﺸﺘﻬﻲ ﻟﻢ ﻳﻨﻈﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻪ ﺣﺘﻰ
ﻳﻨﺰﻉ ﺃﻭ ﻳﺘﺮﻙ
"Mutumin da ya ci duk irin abincin da zuciyarsa ta riya masa, ya sanya duk irin tufar da zuciyarsa ta riya masa, ya hau duk irin abin hawar da zuciyarsa ta riya masa, Allah ba zai dube shi ba har sai ya tube tufar ko ya bar abincin ko abin hawar".
(Tuhaful-Ukul shafi na 38.)
*****************************
Mai yiyuwa ne jumlar 'ya hau duk
irin abin hawar da zuciyarsa ta
riya masa" tana nufin hakikanin
ma'anar kalmar ce. Wato mutum
ya hau duk irin abin hawar da
zuciyarsa ta karkata zuwa gare
shi. Har ila yau tana iya daukar
ma'anar kalmar ta wata
mahanga ta daban, wato mutum
ya aikata duk abin da zuciyarsa
ta riya masa. Ta kowace fuska
muka fahimci ma'anar kalmar
dai, za mu fahimci cewa shiriyar
Ubangiji ita ce tushen kowani
irin alheri, kuma ita ce za ta kai
mutum zuwa ga matsayin cika da
kamala a rayuwarsa ta duniya.
Amma da zarar mutum ya dauki
matakin aikata duk abin da
zuciyarsa ta riya masa, mai kyau
da mummuna, to shakka babu
za'a kwace wannan ni'ima daga
gare shi. Nisantar aikata
abubuwan son rai tare da kawar
da kai daga abubuwan jin dadin
da zuciya ta riya tana samuwa ne
bisa radin kai da zabi.
Wanda kuma ya zama ba zai iya
aikata abin da ransa ya riya masa
ba, to dole ya fahimci cewa
hakan babbar ni'ima ce gare shi
saboda ba shi da damar shiga
cikin fagen jarabawar yaki da
masifar son rai da aikata duk
abin da zuciyarsa ta riya masa na
jin dadi. Duk kuwa da cewa mutumin da yake da damar yaki da son ransa, yafi samun lada mai yawa a wajen Allah saboda gwagwarmayar da yayi da ita har yafi karfinta.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din