BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
UWAR KUDI
T849: Shin Khumsi ya wajaba kan kudin da mutum yake kasuwanci da su ko kuma?
A: Idan har asalin uwar kudin ya kasance daga cikin riban kasuwanci ne to dole ne ya fitar da khumsinsa, to amma kudin da yake sarrafa shi daga uwar kudin wajen neman riba na daga ayyukan kula da kayan, kudin daukan kayan da kuma auna shi da sauransu to ana cire shi daga cikin riban kasuwanci, don haka babu khumsi a cikinsa.
T850: Shin khumsi yana wajaba kan na'urori ko kuma kayayyakin da ake yin amfani da su wajen kasuwancin?
A: Hukuncin na'urori da kuma kayayyakin kasuwanci dai-dai yake da hukuncin uwar kudi wajen wajibcin fitar da khumsinsa.
T851: Mene ne hukuncin kayayyakin da mutum kan saye su cikin shekararsa ta khumsi kana ya sayar da su bayan shigan shekararsa ta khumsi?
A: Idan har ya saye su ne dan ya sayar, to idan sayar da su din zai yiwu zuwa cikan shekarar khumsi, to wajibi ne ya fitar da khumsin ribarsu, in kuma ba haka ba to matsawar bai sayar ba, khumsi ba ya hawa kansa, idan kuwa ya sayar da su to ribar da ya samu ana kirga ta daga cikin ribar wannar shekarar da ya sayar a ciki ne.