BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
HANYAR KIRGEN KHUMSI
T852: Mene ne hukumcin jinkirta fitar da Khumusi har zuwa wata shekara ta daban.
A: Jinkirta fitar da Khumusi daga shekarar da ya kamata a fitar da ita zuwa wata shekara ta daban ba ya halalta. A duk lokacin da ya fitar da shi yana a matsayin biyan bashin da ake bin mutum ne. Matukar mukallafi bai fitar da khumusinsa a daidai lokacin fitarwar ba, to ba shi da hakkin sarrafa dukiyar. Matukar ya yi amfani da ita kafin fitar da Khumusin, to mikidarin khumusin lamuni ne, misalin ya sayi wani fili ne da makamancin hakan da kudin da ba a fitar masa da Khumusi ba, mu'amala da mikidarin khumusin ya ta'allaka ne da izinin waliyin khumusin. Bayan an sami izinin waliyin khumusin, wajibi ne a fitar da khumusin wannan kaya ko kuma wannna fili gwargwadon farashin lokacin.
T853: Ni na kasance ma'abucin shago ne, to kowace shekara na kan kirga abin da nake da shi na daga kudi da kuma sauran kayayyakin, to kasantuwan wasu daga cikin kayayyakin ba sa sayuwa har zuwa karshen shekarar khumusi, shin wajibi ne cire khumsin su karshen shekarar kafin a sayar da su ko kuma khumusi yana wajaba a kansu ne bayan sayar da su? Kana kuma idan na ba da khumsin kaya kana daga baya na sayar da shi to yaya zan yi lissafain khumsin shekara mai zuwa? Sannan kuma idan ban sayar da su ba har sai da farashinsu ya sake, to mene ne hukuncin hakan?
A: Duk kayan da ba ka sayar ba kana kuma ba ka samu mai sayan sa ba har zuwa farkon shekara, a wannan halin ba wajibi ba ne ka fitar da khumsin abin da ya karu na kudinsa, face dai za ka yi lissafin ribar da ka samu ne bayan sayar da su nan gaba kuma khumusinsu za a fitar ne a cikin shekara da aka sayar da su, to amma kayan da kudinsa ya tashi kana kuma ka sami wanda zai saya a cikin shekarar amma sai ba a sayar ba har zuwa karshen shekara dan neman kari, to wajibi ne ka ba da khumsin abin da ya karu na daga kudinsa lokacin da shekara ta cika.
T854: Shekaru uku da suka wuce na bude shago da kudin da aka fitar masa da khumsi, kuma farkon shekarar khumsina shi ne karshen shekarar hijira ta shamsiyya, to lokacin da shekara ta cika sai ya kasance dukkan uwar kudin nawa suna hannun mutane a matsayin bashi a daidai lokacin kuma ana bi na basussuka to ina so a min bayanin abin da ya hau kaina?
A: Idan har lokacin shigan shekarar babu komai a hannunka na daga uwar kudin ko kuma na daga ribar, ko kuma dukkan jimillar abin da ya saura na daga kudi da kayayyaki a cikin shagon dai-dai yake da uwar kudin da aka riga aka fitar masa da khumsi, to khumsi ba wajibi ba ne a gare ka, kana basussukanka da ke hannun mutane za su kasance riba ne ta shekarar da ka karbe su a cikinta.
T855: A karshen shekarar lissafin kudin kayayyakin da ke cikin shagonmu ya kan zama mana da tsananin wahala, to ta wace hanya za mu yi lissafinsu?
A: Wajibi ne a kayyade kudin kayyakin da ke cikin shagon ta duk wata hanyar da ta sauwaka ko da kuwa ta hanyar kintatawa ne dan lissafin ribar da aka samu a shekara domin a fitar musu da khumsi da ya wajaba.
T856: Muna so ayi mana bayanin hanya mafi sauki ga ma'abucin shago wajen fitar da khumsi?
A: Farko ya yi lissafi da kuma kimanta abubuwan da ke hannunsa na daga kudi da kuma kayayyaki a dai-dai shigar shekaran khumusinsa to sai ya kwatanta dukkan abin da ya lissafta da ainihin asalin uwar kudin, idan har akwai kari akan uwar kudin, to za'a lissafa ta a matsayin riba, dan haka khumsi ya hau kanta.
T857: Shin farkon shekarar mutum shi ne watan farkon da ya fara karbar albashinsa?
A: Farkon shekarar mai karban albashi da suka hada da leburori da ma'aikata da sauransu shi ne ranar farko da mutum ya fara karbar albashinsa ko kuma zai iya karbar.
T858: Ya ya ake ayyna farkon shekarar fitar da khumusi?
A: Farkon shekarar khumusi ba ya bukatar ayyanawa daga wajen mukallafi, face da shi da kansa ne ya ke ayyana kansa daga lokacin da mutum ya fara samun kudin shigarsa na shekara. A saboda haka farkon shekarar ma'aikaci shi ne daga ranar da ya zama zai iya karbar albashin nasa. Shekarar khumusin masu tizara da ‘yan kasuwa ita ce daga lokacin da ya fara saye da sayarwar. Su kuwa manoma ita ce daga lokacin da ya fara girbi amfanin gonarsa na wannan shekarar.