T860: Akwai wasu mutane da khumsi ya wajaba a kansu amma ba sa fitar da shi, inda a halin yanzu ba za su iya fitar da shi ba ko kuma fitar da shi zai yi musu wahala, to mene ne hukuncinsu?
A: Khumsi wajibi ba ya faduwa a kansu dan kawai fitar da shi zai yi musu wahala, face dai wajibi ne su fitar da shi ta duk wata hanyar da ta saukaka, ko da kuwa da yin mudawara ne tsakaninsu da majibincin khumsin ko kuma wakilinsa kan ya dinga bayarwa kadan kadan gwargwadon yadda zai iya.