HUKUMCIN AMFANI DA KUDIN DA BA'A FITAR MUSU DA KHUMSI BA
T861: Shin khumsi ya hau kan gidan da aka gina shi da kudin da ba'a cire masa khumsi ba ? A bisa kasantuwan wajibci, to shin za'a fitar da khumsin ne gwargwadon kudinsa na wannan lokacin ko kuma dai-dai da kudin lokacin da aka gina?
A: Idan mutum ya gina gidan zamansa da ainihin kudin da ba'a cire masa khumsi ba wajen sayen kayayyakin ginin da kuma kudin masu aikin to zai fitar da khumsin ne gwargwadon kudin gidan a halin da ake ciki, to amma da ya gina gidan ne da kudin bashi kana sai ya biya bashin da kudin da ba' a cire masa khumsi ba, to babu komai a gare shi sai dai khumsin wannan kudi da ya biya ba shi da su.
T862: Ni na kasance saurayi ne da nake rayuwa da iyayena, to mahaifina ya kasance ba ya fitar da khumsi da zakkan da suka hau kansa, har ma ya gina gida da kudi na riba a hakikanin gaskiya haramcin abincin da nake ci a fili yake, to bisa la' akari da cewa ba zan iya rabuwa da shi ba, dan haka nake so ayi min bayani kan abin da ya hau kaina daga hukunci?
A: Idan har kana da yakinin cewa kudin mahaifin naka sun hadu da kudin riba (kudin ruwa), ko kuma kana da masaniyar cewa ba ya fitar da khumsi ko zakka da suka hau kansa to haka ba zai iya tabbatar maka da haramcin abin da kake amfani da shi na dukiyarsa ba, to matukar ba ka da tabbacin haramcin abin, ba haramun ba ne ka yi amfani da shi. Na'am da za ka samu yakinin haramcin abin da kake amfani da shi na dukiyar, to ba ya halatta a gare ka ka yi amfani da shi, sai dai idan rabuwa da mahaifin naka zai sanya ka cikin wani hali na kunci, to a wannan hali ya halatta ka yi amfani da dukiyar tasa, to amma wajibi ne ka dauki nauyin fitar da abin da ya hau wannan dukiya da kake amfani da ita na daga khumsi, zakka ko dukiyar wasu.
T863: Idan har na kasance ban yi lissafin khumsi ba har na tsawon shekaru ta yadda har uwar kudin nawa suka karu, to sai daga baya na fara fitar da khumsin sauran kudin da ba uwar kudin na da ba, shin akwai wata matsala ga hakan?
A: Idan har a farkon shekarar khumsi dukiyar taka wani abu na khumsi ya hau kanta, ko da kuwa kadan ne, matukar dai ba ka yi lissafin su ba kuma ba ka fitar da abin da ya hau kansu na daga khumsi ba, to ba ka da hakkin amfani da wannan dukiya, da za ka yi amfani da ita ta hanyar saye da sayarwa kafin ka fitar da khumsinta, to wannan amfani naka ya zamanto amfani da kayan wani wanda yake bukatar izinin ma'abucin khumsin tukun, a daidai gwargwadon kudin khumusin da ke ciki to bayan ba da izinin ma wajibi ne da farko ka fitar da khumsin dukkan kudin, kana ka fitar da khumsin ribar da ya karu a kan abubuwan masarufi da kake bukatuwa da shi na shekara.
T864: Mu mun kasance muna mu'amala da mutanen da ba sa fitar da khumsi, muna saye da sayarwa tsakaninmu kana kuma sauran mu'amaloli kamar ziyarar juna da cin abinci duk tare, to mene ne hukuncin wannan mas'ala.
A: Idan har kana da yakinin kasantuwar khumsi a cikin dukiyar da kake mu'amala da su na saye da sayarwa ko kuma kake amfanuwa da ita yayin da kuke tare, to ba ya halatta a gare ku ku yi amfani da ita, dan kuwa wannan mu'amala taku ta kasance amfani da abin wani ne wanda yake bukatar izinin ma'abucin khumsin ko kuma wakilinsa a daidai gwargwadon khumusin da ke ciki tilas, sai dai idan barin mu'amala da su zai haifar maka da kunci, to a irin wannan halin ya halarta ku yi amfani da ita, sai dai biyan khumsin dukiyarsu da ka yi amfani da shi yana kanka.
T865: Mene ne hukuncin jinkirta bayar da khumsin shekara (da ake ciki) har zuwa shekara ta gaba?
A: Bayar da khumsi na wajibi ko da yake yin haka kan iya zuwa bayan an riga an jinkirta shi har zuwa shekara ta gaba, sai dai ba ya halatta ya yi amfani da kudinsa da khumsi ya hau kansa matukar dai shekarar khumsinsa ta shiga, har sai idan ya fitar da khumusin, da kuwa zai yi amfani da shi kafin fitar da khumsi kamar wajen sayen wasu kayayyaki ko fili da sauransu to bayan samun izinin yin mu'amala da dukiyar daga wajen ma'abucin khumsin, wajibi ne ya lissafa wannan kaya ko kuma fili da kudinsa na wannan lokacin kana ya fitar da khumusinsa.