MAJIBINCIN KHUMSI, WAKILANSA DA KUMA YADDA ZA' A SARRAFA SHI
T866: Idan mutum ya kasance yana taklidi wa wani marja'i ne ba jagora (waliyyi amr- il- Muslimin) ba, to ga wani daya daga cikin (maraja'an) ne ya wajaba ya ba da khumsinsa?
A: Wajibi ne a bayar da khumsi ga jagora, dan kuwa shi ne yake gudanar da al'amurran musulmai, sai dai idan fatawar mujtahidin da yake masa taklid ya saba wa hakan.
T867: Masu takalidi ga marigayi lmam Khumaini (r.a) ga wa za su ba da khumsin dukiyarsu?
A: Za ku iya aiko da ita ga ofishinmu da ke Tehran, ko kuma ku ba da ita ga wakilanmu da suke sauran garuruwa wanda muka ba su izini.