T868: Mene ne hukuncin fara jihadi (jihadul Ibtida'i) a lokacin fakuwar lmamuz Zaman (a.s)? Kana kuma shin hakan yana halatta ga "waliyi amril muslimin" ya hukunta hakan?
A: Bai yi nisa ba ace hakan ya halatta ga mujtahidin da ya cika sharudda wanda ke gudanar da al'amurran musulmai idan har ya ga akwai maslaha ga hakan, kai wannan maganar ma ita ce karfaffa.
T869: Mene ne hukumcin kare Musulunci yayin da yake fuskantar hatsari ba tare da yardar iyaye ba?
A: Kariyar da ta wajaba ga Musulunci da kuma musulmai bai dogara kan izinin iyaye ba, to amma duk da haka yana da kyau a kokarta neman yardar tasu ta duk hanyar da ta saukaka.
T870: Da zamu dauka cewa kare addinin Musulunci na asali ya ta'allaka ne da zubar da jinin wani mutum, shin ya halatta gare mu mu aikata hakan?
A: Hakika zubar da jinin dan'Adam ba tare da hakki ba haramun ne kuma ya saba wa hukuncin addinin Musulunci na asali, don haka wannan kalami na cewa kare addinin Musulunci na asali ya ta'allaka ga zubar da jinin wata rai mara laifi ba shi da ma' ana, to amma idan har abin da ake nufi da hakan shi ne yin jihadi fi sabilillah da kuma kariya ga Musuluncin asali ta hanyar da watakila za'a iya kashe shi, to hakan yana da halaye kala-kala, idan har mutum da kansa ya gano cewa tushen addini yana fuskantar hatsari to wajibi ne gare shi ya kare Musulunci, ko da kuwa akwai tsoron cewa za'a iya kashe shi.