BABIN UMURNI DA AIKI MAI KYAU DA KUMA HANI KAN MUMMUNAN AIKI
T872: Idan har umurni da aiki mai kyau da kuma hani da mummuna zai kai ga dukan mai aikata mummunar aiki ko kuma takura rayuwarsa, ko kuma amfani da dukiyarsa, ko halakar da ita shin hakan yana halatta ba tare da izinin waliyul Amri ba ko kuma izinin Marja'i ba?
A: Wannan al'amari yana da matakai dadan-daban, to a sura ta gaba daya dai, idan dai har umurni da mai kyau da kuma hani kan mummunan aiki bai ta'allaka da jiki ko kuma sanya hannu akan dukiyar mai aikaita munkarin ba, to bai bukatar izinin wani mutum, face ma dai wannan alamari ne da ya wajaba kan dukkan mukallafai, amma a matakin da yake bukatar fiye da amfani da harshe to idan har hakan a guri ne da ake kula da tsari irin na addinin Musulunci, wanda ake lura da wajibin nan na amr bil ma'aruf to al'amarin yana bukatan izinin jagora Waliyul amr, ko kuma hakan aiki ne da ya hau kan hukuma.
T873: Idan har gudanar da umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna da ya shafi aiki mai muhimmancin gaske kamar kare rai ya zan bai yiwuwa sai da amfani da hannu wanda zai kai ga jin ciwo ko kuma ga kisan kai a wasu lokuta, to shin hakan ma yana bukatar izinin jagora ko Marja'i?
A: Idan har kiyaye rai da kuma kare afkuwar kisan kai ya ta'allaka ne ga daukan mataki na gaggawa, kuma kai tsaye to ya halatta, kana hakan ma wajibi ne saboda la'akari da kariya ga rai, hakan bai ta'allaka da izinin jagora ba ko umarninsa sai dai idan har kare rai zai rataya ga zubar da jinin wanda ya kawo harin, to hakan yana da halaye daban-daban yana yiwuwa hukuncin nasa ya bambanta.
T874: Shin wajibi ne yayin da mutum yake so ya yi umurni da alheri da kuma hani da mummunan aiki ya kasance yana da karfin yin hakan? Sannan yaushe ne yake wajaba mutum ya yi umurni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna?
A: Dole ne mai umurni da kyakkyawa da kuma hani ga munanan aiki ya kasance ya san kyakkawa da mummunan aikin, kana kuma ya tabbatar cewa mai aikata wannan (mummunan aikin) shi ma yana da masaniya kan hakan, amma duk da haka yake aikatawa da gangan ba tare da wani uzuri na shari'a ba.
Sannan umurni da kyakkawa da kuma hani da mummunan yana wajaba a gare shi ne idan har yana tsammanin umarnin ko hanin da zai yi yana da tasiri ga mutumin da ke aikata mummunan ko wanda ya bar kyakkyawan kana kuma shi kansa zai tsira daga cutarwa, wato sai ya auna ya gani cewa cutarwar da zai samu nawa take kana wane irin muhimmanci ne abin da zai hana din yake da shi ko kuma abin da zai yi umurni a aikata din, to bayan ya auna ya gani cewa sun dace sai ya aikata amma idan ba haka ba to ba wajibi ba ne.
T875: Shin ya halatta mutum ya ki kula da umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna saboda tsoron kora daga wajen aiki? (Kamar misalin shugaban ma'aikatar da yake aiki a ciki yana aikata wasu munanan ayyuka ko kuma ya ba da daman aikatawa).
A: A shakali na gaba daya, idan har mutum yana tsoron afkuwar cutarwa gare shi yayin gudanar da umurni da kyawawan aiki da kuma hani da munana, to hakan ba wajibi ba ne a gare shi.
T876: Wasu direbobi su kan sanya kasetocin da haramun ne jin su, duk kuwa da nasihohin da aka musu to amma su kan ki ya cirewa dan haka muke so ka yi mana bayanin abin da ya kamata mu aikata a irin wannan hali?
A: Ba ya wajaba a gare ku da ku yi fiye da abin da ya wuce hani da baki hakan ma sai dai idan har duk sharuddan hani ga mummunan aiki sun samu a gare ku, in kuwa hani da baki bai yi tasiri ba, to wajibi ne ku nesanci sauraron kida da waka na haram, idan kuwa har wannan sauti na haram ya isa gare ku ba tare da son ku ba to babu komai a gare ku.
T877: A wasu lokuta wasu mutane daga gidaje sukan sa wasu kasetoci na kida wanda ba mu san cewa shin halal ne ko haram ba sannan su kure sautin har ya dami mutane, to mene ne abin da ya hau kan mutane dangane da hakan?
A: Bai halatta mutum ya shiga gidan mutane (don yin hani ga mummunan aiki) ba dan kuwa umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna ya ta'allaka ne da gano kyakkyawan aiki da kuma mummunan kana da kuma mallakan sharuddansa.