YADDA AKE UMURNI DA KYAWAWAN AYYUKA DA KUMA HANI GA MUNANA
T878: Wace hanya ce ya kamata mutum ya bi dangane da iyayensa da ba sa kula da ayyukan shari'a da suka wajaba kansu saboda rashin cikakken i'itikadinsu ga wajiban?
A: Wajibi ne ya yi musu umurni da kyakkyawan aiki da kuma hani da mummuna cikin tattausan murya tare da kuma kiyaye girmama su a matsayinsu na iyaye.
T879: Dan uwana ba ya kula da ayyukan shari'a da kuma dabi'un kwarai, duk kuwa da nasihohin da nake masa amma ba su yi tasiri ba, to me ya kamata in aikata yayin da na gan shi yana aikata irin wadannan ayyuka?
A: Wajibi ne ka nuna rashin amincewarka ga irin wadannan ayyuka da suka sabawa shari'a, da kuma ci gaba da tunasar da shi ta duk wata hanya ta yan uwantaka da kake ga ta dace, to amma kada ka yanke zumuncinka da shi dan kuwa hakan ba ya halatta.
T880: Shin kin amsa sallamar wanda ke aikata mummunan aiki dan tsawata masa ya halatta?
A: Kin amsa sallama da nufin hani ga mummunan aiki ya halatta idan har haka din a wajen mutane ana ganin cewa tsawatarwa ne kana hani ne kan mummunan aiki.