BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Yarda Da Abin Da Rabon Allah
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
ﻭﻟﻤﺎ ﻧـﺰﻟﺖ ﻋﻠﻴﻪ "ﻭﻻ ﺗﻤﺪّﻥ ﻋﻴﻨﻴﻚ
ﺇﻟﻰ ﻣﺎ ﻣﺘﻌﻨﺎ ﺑﻪ ﺃﺯﻭﺍﺟﺎً ﻣﻨﻬﻢ...
ﺇﻟﻰ ﺁﺧﺮ ﺍﻵﻳﺔ" ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺘﻌﺰّ
ﺑﻌﺰﺍﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻧﻘﻄﻌﺖ ﻧﻔﺴﻪ
ﺣﺴﺮﺍﺕٍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﻭﻣﻦ ﻣﺪّ
ﻋﻴﻨﻴﻪ ﺇﻟﻰ ﻣﺎ ﻓﻲ ﺃﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻣﻦ
ﺩﻧﻴﺎﻫﻢ ﻃﺎﻝ ﺣﺰﻧﻪ ﻭﺳﺨِﻂ ﻣﺎ
ﻗﺴّﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻪ ﻣﻦ ﺭﺯﻗﻪ ﻭﺗﻨﻐّﺺ
ﻋﻠﻴﻪ ﻋﻴﺸﻪ
"Yayin da ayar dake cewa:
"Kuma kada ka mikar da
idanuwanka zuwa ga abin
da muka jiyar da su dadi da
shi, nau'i-nau'i daga gare
su.....har zuwa karshen
ayar" ta sauko, Manzon
Allah (s.a.w.a) ya ce: Duk
wanda bai nutsu da rabon
Allah ba, ya fitar da rai daga
ni'imarsa yayi hasarar
duniya. Kuma wanda ya
sanya idonsa kan abin dake
hannun mutane na daga
duniyarsu, bakin cikinsa ya
tsawaita, kuma yayi fushi da
arzikin da Allah ya raba ya
mallaka masa, kuma yayi
sanadiyyar durkushewar
arzikinsa.
(Tuhaful Ukul shafi na 51)
Bayan saukar wannan aya
mai girma da muka ambata
a sama (wato: "Kuma kada
ka mikar da idanuwanka
zuwa ga abin da muka jiyar
da su dadi da shi, nau'i-
nau'i daga gare su) Manzon
Allah (s.a.w.a) ya bayyana
cewa: Dole ne mumini ya
nutsu da rabon Allah da ya
mallaka masa, sannan kuma
yayi farin ciki da yarda da
abubuwan da Allah Ya
tanadar masa na daga
rahamarsa da bata karewa
da tarin kyakkyawar
sakamakonsa da yake
baiwa muminai a ranar
kiyama. Amma idan ya
zamanto mai sanya ido ne
kan dukiya da matsayi da
wadansu suka samu, ko
kuma kullum ya kasance
cikin bakin ciki, bacin rai da
nadama tare da nuna
rashin amincewa da
kaddarar Ubangijinsa,
burinsa kawai yayi rayuwa
irin ta masu hali ko kuma ya
dauka wa kansa cewa dole
ne sai ya shiga cikin sahun
masu gwagwarmaya da
nufin samun duniya ta
kowace hanya, wato ya ki
halal ya ki haram don dai
kawai ya kai ga matsayin
sauran mutane masu hali
da sukuni. To a nan kamata
ya yi ku yi kokarin tseratar
da kanku da kuma nitsuwa
da rabon da Allah ya
mallaka muku domin ku
hutar da rayuwarku da
kuma nesantar konewa
cikin wutar rayuwar hasara
da nadawa ta wasu sannan
da fadawa cikin tarkon
fagen yakin da ba shi da
karshe.