XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

SANA'OI DA KASUWANCIN DA BA SU HALATTA BA
Ali Khamenei4

T887. Shin ya halarta a sai da aladan jeji, wanda hukumar mafarauta ta farauto ko kuma manoma suka farauto shi domin kariya ga wajen kiwo ko kuma gonaki, to ya halarta a sai da shi domin ayi naman gwangwani da namansa a kai shi kasashen da ba na musulmi ba?

A: Ko kadan bai halarta a yi cinikin naman alade ba a matsayin abincin mutum ko da kuwa ba musulmi ba ne, sai dai da za a ce akwai wani amfani da masu hankali ke iya karba wanda kuma ya halarta wanda kuma ake iya dogaro a kai kamar amfani da shi dan yin abincin dabbobi, ko kuma dan yin man da a ke yin sabulu da shi ko makamancin haka, a wannan hali ba abin da zai hana a yi cinikinsa saye ko sayarwa.
T888. Shin ya halatta a yi aiki a ma'aikatar da ake yin naman gwangwani da alade, ko kuma yin aiki a gidajen disko da wurare na fasadi? Kana mene ne hukumcin kudin shiga da yake tattare da hakan?

A: Sam bai halarta a shari'a ba ya kasance al'amura na haram su ne aikin da mutum yake yi a matsayin sana'a, irin sai da naman alade ko giya ko gina gidan disko ko kula da shi ko gina dandalin fasadi da alfasha ko caca da shan giya da dai makamantansu.

Duk wadannan abubuwan bai halarta a mai da su sana'a ba, kana bai halarta a ci kudin ba a matsayin ladan aiki.

T889. Shin sayar da giya ko naman alade ko kuma wani abin da bai halarta a ci ba, ya inganta ga wanda ke ganin cewa ba haram ba ne ko kuma ya inganta a ba shi kyautarsa?
A: Kyauta ko sayar da abin da bai halarta a ci, ko a sha ba, in har da nufin ci ne ko kuma da nufin sha, ko kuwa ya san cewa mai sayan zai saya ne domin ya ci ko ya sha to yin haka bai halarta ba, ko da kuwa shi mai sayen yana ganin halaccin abin.
T890. Shin yana halarta a sai da jini ga mutumin da zai yi amfani da shi?

A: Babu laifi a sai da jini domin yin amfani da shi idan har manufa ce wanda masu hankali suka yarda da ita.
T891. Shin ya halarta aikin mutum ya kasance kone mutanen da suka mutu, wadanda ba musulmi ba, ya kuma karbi lada a kan wannan aikin?

A: Babu wata hanya wacce ta haramta kone gawar da ba musulmi ba, dan haka ba abin da zai hana ya zamo sana'ar mutum shi kone gawar da ba ta musulmi ba, kuma ya karbi ladan aikin konewar.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din