Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

KARBAN LADAN AIKI, KAN ABIN DA YAKE WAJIBI
Ali Khamenei4

T892. Mene ne hukumcin albashin malaman da suke koyar da (fikhu) ko usulu a cikin makarantun horar da alkalai?

A: Wajibcin koyar da wajibi na (kifaya) bai hana halaccin karban albashi ga wanda ya koyar da fikihu ko usulul fikihu ba, musamman idan albashin ya zama a sanadiyyar tahowa wurin koyarwar da kuma kula da ajin ne.
T893. Shin ya halarta a karbi albashi domin limancin sallah ko kuma wa'azi da shiryarwa na addini a karkashin wata mu'assasa?

A: Babu laifi a karbi ladan zuwa da dawowa da kuma wahalhalun da mutum ya yi wanda ba wajibi ba ne a shara'a ya yi shi.
T894. Shin ya halarta mutum ya karbi ladan wankin mamaci?

A: Bai halarta mutum ya karbi lada ba dan saboda shi wankin mamaci, domin kuwa shi wankin mamaci musulmi aiki ne na ibada wacce ta ke matsayin wajibi na (kifaya).

T895. Ya halatta a shara'a a karbi lada domin daura aure da mutum ya yi?
A: Babu laifi cikin hakan.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din