T896. Mene ne bambancin kida wanda ya halarta da wanda bai halarta ba?
A: Dukkannin kidan da mutane ke - yi masa kallo irin na batsa da wasan da bai kamata ba ko kuma ake yin sa a wuraren wasanni da suka dace da wuri na wargi da kuma bata to irin wannan kida (waka) shi ne ya haramta kuma babu bambanci tsakanin na da ko kuma na zamani da sauransu - kuma gano wannan yana komawa ne ga shi mukallafin amma duk kidan da bai kasance irin wannan ba to ba haram ba ne.
T897. Mene ne hukumcin jin kaset wanda wata kungiya ta Musulunci take ganin ba laifi ba ne aji? kana kuma mene ne hukumcin sauraron abubuwan kida misalign Jita ko gurmi, ko kuma fiyano?
A: Halaccin jin irin wadannan kasa kasetoci yana dai dai da yadda mai jin nasu ya fahimci abin, idan yana ganin cewa abu ne wanda bai tattare da kide kide da wake wake na holewa wanda kuma a ke yin su a wuraren wargi da batsa to ba laifi ba ne ya saurari irin wannan, amma don kawai wata kungiyar watsa abubuwan Musulunci tana ganin cewa ba laifi ba ne ta watsa kide kide to bai zamo hujja ga mutum a shari'a ba kana ba ya halatta a yi amfani da kayan kidan cikin kidan batsa wanda ya dace da wuraren wargi da sabo, da kuwa za'a yi amfani na halal da irin wadannan kayan kidan kan manufofi na masu hankali to shari'a ba ta hana ba, gane hakan kuwa yana hannun mukallafi.
T898. Shin kida da kwarya ko kuwa da kwano da wasu ababen da ba na kida ba a yayin kai amarya dakinta ya halatta, mene ne kuma hukumcinsa lokacin da sauti ya fita har zuwa gurin da majaze suke ji?
A: Halaccin hakan yana dangane da yadda ake amfani da su ne, to idan ya zama irin yadda aka saba ne a bukukuwan aure na al'ada, to duk abin da ba a kira shi da sunan wargi ba, kana kuma bai kunshi abubuwan barna ba babu laifi cikin jin sa.
T899: Mene ne hukumcin mata su yi mandiri a lokacin bikin aure?
A: Bai halatta ayi amfani da kayan kide kide domin rera kida na wasa ba, amma babu laifi ayi amfani da shi cikin wakokin da ake yin su na kai amarya.
T900. Shin ya halatta ayi amfani da ababen kida a dararen angwanci. Idan kuma ya halatta mene ne iyakar halaccin ga mata da maza?
A: Ba laifi mata su rera waka a wuraren da suka kebanci bikin aure kuma ba laifi ba ne su yi amfani da kayan kide kide a lokacin rera wakar a irin wadannan wurare muddin dai bai ketare yadda aka saba ba, amma idan ba wadannan wurare ba to sam bai halatta ba.
T901. Shin ya halatta a saurari wakoki a wurin bikin aure ta hanyar rediyo ko kuma kaset?
A: Bubu laifi a saurari wakoki a bikin daukan amarya (matsawar babu abu na haram) a cikinsa.
T902. lna aiki a wurin da mai wurin kullumn yana sa kaset na kade kade da bai halatta ba don haka sai na ga ba yadda zan yi sai na ji, to shin ya halatta gare ni ko a'a?
A: In har a cikin kaset din akwai wasu wakoki na batsa da suka dace da guraren wargi ko bata ko sabo to bai halatta kai ka yi shiru domin ji ba sai dai in har ya zan cewar nan ne kadai wajen aikinka ba laifi ka je wajen aikinka kuma ka ci gaba da aikinka, illa kawai bai halatta ba ka yi shiru ka saurara dan jin wannan wakokin, ko da ya zo ga kunnenka ba da nufin saurara ba.
T903. Mene ne hukumcin jin wakoki na wargi na (rakashewa) wanda suka fito daga kasashen yamma? Kana mene ne hukumcin raba shi wa mutane?
A: Abin da bai halatta a saurare shi ko a yi amfani da shi ba na daga wakoki na wargi wadanda suka dace da guraren wargi da bata, to irin wadannan wakoki babu bambanci cikin haramcinsu shin da wane yare aka yi su kuma ko da daga wane kasa (ko gari) suka fito, saboda haka saye da sayar da su ko kuma yada su ko sauraransu dukkan haka bai halatta ba matsawar dai sun kunshi wakoki na wargi wanda suka haramta.
T904. Mene ne hukumcin jin sautin mace cikin wake ko makamantansa, tare da rerawa ta yanda yara da manya mata da maza ko wanda ba muharrami ba za su iya ji?
A: In har sautin macen ba ta karya shi zuwa ga wakar rakashewa ba kana wanda yake jin ba yana nufin jin dadi ko aukawa cikin haram ba ne sannan hakan bai zan abu ne da zai jawo wata barna ba, to babu laifi cikinsa.
T905. Shin wai gaskiya ne da ake cewa kida yana da asali a cikin Musulunci, kana wai ta hanyar kida za'a iya saduwa da falarar Allah (WATO KIDAN SUFANCI)?
A: Kida bai daga cikin hanyoyin samun saduwa da falarar Ubangiji, ko kuma ace da shi ne za'a gano girman halittar Ubangiji ko rabauta ta hanyar saninsa Mahalicci, hakan ba zai taba yiwuwa ba ta hanyar kida.
T906. Ya halatta a rera wakar rakashewa ba tare da kida ba?
A: Wakar rakashewa dai haramun ce ko da kuwa an yi ta ba tare da kida ba.
T907. Mene ne hukumcin cinikin kayan kida kana kuma a wane wuri ne ake yin amfani da shi?
A: Ba laifi a yi cinikin kayan kida wanda ba kawai ta hanyar batsa ake amfani da shi ba. To irin wannan kayan kidan ya halatta a yi cinikinsu don aiwatar da manufofi na halal, kuma ba laifi a saurare su.
T908. Ya halatta a karanta Alkur'ani ko addu'a ko kiran salla da irin sautin da a ke wakoki na rakashewa da shi?
A: lrin sautin da aka kebance shi domin wakoki na batsa da rakashewa, bai halatta a karanta Alkur'ani ko kiran salla ko addu'a da shi ba.
T909. A yanzu ana yin amfani da kida don maganin wasu cututtuka na rai kamar bakin ciki da faduwar gaba da abin da ya shafi sha'awa ko rashinsa, mene ne hukumcin haka?
A: Idan har likita kwararre, amintacce ya ce magance ciwon ya tsaya ne kan haka to ba matsala ga hakan amma gwargwadon yadda za a warkar da ciwon.
T910. Mene ne hukumcin yin amfani da kayan kida wanda daliban makaranta suke yi karkashin hukumar tarbiyya ta makaranta?
A: Kayan kidan da mutane ke ganin cewar za'a iya yin amfani da su wuraren da ya halatta to yana halatta a yi amfani da su, amma kuwa wanda ake ganin ba za'a iya yin amfani da su ba a wuraren da ya halatta to ba su halatta a yi amfani da su ba.
T911. Ya halatta a karbi ladan yin rukodin din kaset din da bai halatta a saurara ba?
A: Kaset din da bai halatta a ji ba to rikodin dinsa ko ladansa bai halatta ba.