T912. Shin ya halatta a yi rawa ta al'ada a wuraren biki, mene ne kuma hukumcin halartar irin wannan wurin?
A: Yin rawa ta yanda ba za ta motsa sha'awa ba ko ba za ta janyo fasadi ba, ba kuma za ta kawo aikata haram ba to ba laifi da irin wannan rawar. Amma halartar wuraren rawa in har zai karfafa wasu don su aikata haram ko kuma ya zan yana tattare da haram to bai halatta ba, idan kuwa ba haka ba ya halatta.
T913. Mene ne hukumcin rawa ta al'ada ga maza a tsakaninsu ko kuma ga mata a tsakaninsu ko kuma namiji a tsakanin mata, ko kuma mace a tsakanin maza?
A: Idan har ya kasance yadda zai motsa sha'awa ne ko zai janyo aikata haram ko barna ko kuma mace tsakanin mazan da ba maharramanta ba, hakan bai halatta ba, haramun ne.
T914. Shin mace ta yi wa mijinta rawa ko kuma miji ya yi wa matarsa rawa ya halatta?
A: Mace ta yi wa mijinta rawa ko miji ya yi wa matarsa rawa halas ne muddun dai babu aikin haram a ciki.
T915. Mene ne hukumcin rawar yaron da bai balaga ba ko yarinyar da ba ta balaga ba cikin maza ko mata?
A: Duk wanda bai balaga ba ba shi da takalifi sai dai bai kamata ba ga wanda suka balaga su karfafa shi ko ita kan yin rawa.
T916. Mene ne hukumcin gina cibiyar koyar da rawa?
A: Gina cibiyar koyar da rawa da yada ta abu ne wanda ya saba wa tsarin hukumar Musulunci.