XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCIN YIN TAFIN HANNU
Ali Khamenei4

T917. Shin ya halatta mata su yi tafi wurin taron farin ciki kamar biki, ko suna idan ya halatta mene ne hukumcin su yi shi da karfi yanda wasu mazan za su ji?

A: Babu laifi cikin yin tafin da aka yi shi daidai gwargwado ko da kuwa ya kai wasu maza daban su ji shi muddun dai bai kunshi barna ba.
T918. Mene ne hukumcin tafin da ake yin sa a wuraren maulidi ko kuma tunawa da ranar haihuwar Ma'asumai don nuna farin ciki wanda ake gabatar da shi a cikin masallatai ko makarantu ko wuraren ibada?

A: Babu laifi cikin kowanne irin tafi a kan kansa muddun dai bai wuce hankali ba sai dai abin da ya fi shi ne a kawata wurin da salati ga Manzo da kabbara musamman ma wanda ake yi cikin masallatai da wuraren ibada ba don komai ba sai don samun ladan salati da kabbarar.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din