pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCIN HOTO DA FINA FINAI
Ali Khamenei4

T919. Mene ne hukumcin kallon hoton wata mace daban mara lullubi? Mene ne kuma hukumcin kallon mace ta telabijin? Shin akwai banbanci tsakanin musulma da wadda ba musulma ba? Ko kuma tsakanin wanda aka kalla yayin da ake watsa shirin kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba.

A: Kallon hoton wata mace daban bai zamo daidai da kallon zatin ita macen ba, don haka babu laifi sai dai in da aka kalla da nufin yaudarar rai ko fadawa fitina ko ya kasance hoton na musulma ce wacce ya san ta, ihtiyadi na wajibi shi ne kar mutum ya kalli hoton wata mace daban ta telabijin wanda ake nunowa kai tsaye lokacin da ake shirin, amma ba laifi a kalle ta ba da nufin wani abu ba idan shirin ba na kai tsaye ba ne matsawar ba tsoron fadawa haram ko fitinuwa.

T920. Shin akwai laifi cikin kallo ko jin shirye shiryen abubuwan dariya ta hanyar rediyo ko telabijin?
A: Ba wani abu cikin kallo ko jin shirye shiryen ban dariya, amma kida wanda yake na wargi da ya dace da wuraren wasa da kuma sabo to bai halatta ba.
T921. Na dauki hotuna a wuraren biki ba tare da cikakken hijabi ba kuma wadannan hotunan a yanzu suna hannun abokaina da ‘yan'uwana, shin dole ne na karbo su?

A: In har zaman hotunan a hannunsu ba zai haifar da barna ba ko kuma ko da ya haifar amma ba ta hanyar ki ne aka ba su ba, ko kuwa dawo da su zai yi wahala to ba wani abu a kanki.
T922. Shin akwai laifi cikin yi wa hoton lmam ko shahidai sumba, bayan kuma ba muharramammu ba ne?

A: Hotunan ajnabai kowanne iri ne ba su zamo daidai da zatin su mutanen ba don haka babu wani laifi cikin yi wa hotunan, mazan da ba muharramai ba sumba da nufin girmamawa ko neman albarka ko baiyanar da kauna in har hakan bai tare da wata manufa daban da za ta haifar da fitina.

T923. Ya halatta a kalli hotunan matan da suke tsirara ko dab da tsirara wadanda ba'a san su ba ta hanyar fina finan sinima ko wasu daban?

A: Kallon fina finai ko hotunan wasu daban bai zamo dai dai da kallonsu kai tsaye ba don haka babu laifi a shari'a muddun dai ba da nufin sha'awa ba kuma hakan bai janyo wata barna ba, sai dai da yake cewa kallon hoto tsirara mai motsa sha'awa bai rabuwa da kallo mai motsa sha'awa mafi yawan lokaci don haka yana zamowa shimfida ne na daukar zunubi to saboda haka haram ne.
T924. Shin ya halatta mace ta kalli kokawa ta maza?

A: Idan kallon ya zamo ido-da-ido ne a filin kokawar ko kuma ta talabijin ne a lokacin da ake yin kokawar kai tsaye ko kuma tana kallo da nufin jin dadi, da tsoron fadawa haram ko kuma ana gudun fitina da barna cikin kallon to bai halatta ba, amma in ba haka ba ya halatta.
T925. Mene ne hukumcin mace ta dauki hoto ba da hijabi ba a tsakanin muharramanta bayan kuma cewa wasu daban za su iya ganin hoton a lokacin da ake wanke shi?

A: Idan har wanda zai dauke ta hoton muharraminta ne to ba laifi ya dauke ta kana kuma idan wanda zai wanke hoton bai san ta ba shi ma ba laifi.
T926. Mene ne hukumcin yin hotuna da sayar da su wadanda ake cewa na Ma'aiki ne ko kuma lmam Ali ko lmam Husain da nufin ajiye su a ofisoshi?

A: Hakan bai haramta ba a shari'a muddun dai ba su kunshi abubuwan da zai janyo wulakanci gare su ba, kana kuma bai saba wa matsayinsu ba.
T927. Mene ne hukumcin karanta littattafai da wakoki na batsa wadanda suke motsa sha'awa?

A: Wajibi ne a nesace su.

T928. Mene ne hukumcin kallon gashin kai ko kirjin mace ta hanyar talabijin?
A: Ba laifi in dai har kallo ne kawai wanda bai tattare da gudun fitina ba kuma barna muddun dai ba lokacin da ake shirin kai tsaye ake nuna ta ba.

T929. Shin ya halatta masu aure su kalli fim din da yake motsa sha'awa?
A: In har za a yi kallon da nufin motsa sha'awa ko kuma zai janyo sha'awa to bai halatta ba.
T930. Mene ne hukumcin ma'aurata su kalli fim din da yake koyar da yadda ake saduwa?

A: Bai halatta a kalli irin wannan fim din ba wanda bai rabuwa da kallo mai motsa sha'awa.
T931. Shin ya halatta a motsa sha‘awa ta hanyar kallon bidiyo?

A: Bai halatta a motsa sha'awa ba ta hanyar kallon bidiyo.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din