HUKUMCIN SHIRYA WASAN KWAIKWAYO DA FINA FINAI NA SINIMA
T932. Shin ya halatta ayi amfani da kayan malamai ko alkalai cikin finafinan sinima? Kuma ya halatta a kwaikwayi fina finan addini da na manyan bayin Allah wanda suka wuce da kuma wadanda ake zamani da su tare da kiyaye matsayinsu da matsayin addini da nufin fito da martabar addini ko ci gabansa ko bayanin irin abin da ake nufi, da karantarwa da kuma kyawawan dabi'u da kuma halaye na addinin Musulunci da kuma yin raddi kan gurbataccen ci gaba, da kuma rashin tarbiyya?
A: Idan aka yi duba da cewa sinima wani tsari ne na wayar da kai to sai mu ga dukkannin wani shirye shirye ko nuna hoto wanda za'a iya samun amfanin tarbiyyantar da matasa da wasunsu ko watsa ci gaban Musulunci ta hanyar nuna sifar wani malami tare da kayan jikinsa ko wasu manyan magabata to duk haka ba laifi, sai dai yana zamowa dole a kare matsayinsu da tufafinsu kada azo da abin da zai iya janyo musu zubewan mutunci kuma dole ne a lura da cewa ba a yi shiri da ya saba wa Musulunci ba.
T933. Mene ne hukumcin namiji ya saka kayan mata ko mace ta saka kayan maza, domin shirya wasa ko fim? Kana kuma mene ne hukumcin mace ta kwaikwayi muryar maza, ko kuma maza su kwaikwayi muryar mata?
A: Sanya kaya ko kwaikwayon murya a matsayin wasa ba laifi ba ne a yayin kamanta yanayin shi wanda ake kwaikwaya idan hakan bai zama yadda zai kawo barna ba.
T934. Mene ne hukumcin mace ta yi amfani da mai ko kayan ado domin yin ado cikin shirya fim wanda wasu mazan daban za su gani?
A: Idan har mace da kanta ne za ta yi adon ko kuma mata ne za su yi mata ko muharraminta kuma idan babu abin da yake barna a ciki to ya halatta, in ko ba haka ba haram ne.