T935. Mene ne hukumcin yin ‘yar tsana da sassaka ko zanen abu mai rai kamar tsururruka ko dabbobi ko dan'adam? Mene ne kuma hukumcin cinikinta, mallakanta da kuma yin wasan kwaikwayo da su?
A: Babu laifi cikin daukan hoto ko sassaka abu ko zana shi, muddun dai ba abu mai ruhi ba ne, kana ma babu laifi cikin daukan hoto ko sassaka ko zana abu mai ruhi muddun dai ba a yi shi yadda zai zama mai gangan jiki (da inuwa) ba ko kuma ba a yi shi kammalalle ba, amma yin mutum-mutumi na dan adam ko na dabbobi bisa surarsu kamila tare da gangar jiki to wannan akwai matsala a cikinsa ko da me aka yi shi, to sai dai kuma babu laifi wajen yin ciniki ko mallakar hotuna da mutum-mutumi, kana babu laifi a yi wasan kwaikwayo da su.
T936. Mene ne hukumcin zana wasu wurare na kissoshin Alkur'ani ga yara kamar a nemi su zana kissar Ma'abuta giwaye, ko yanda kogi ya tsage ga Annabi Musa da wasunsu?
A: Ba laifi a kan hakan sai dai kuma wajibi ne duk abin da za su kawo shi ya zama gaskiya ne, kana kuma su nesanci yin bayanin abin da babu shi ko kuma abin da zai rage darajarsu.
T937. Mene ne hukumcin yin abubuwan ado bisa sura ta mutum-mutumi? Shin kuma abin da aka yi surar wannan abin da shi shi ma yana da tasiri a haramcin?
A: Bai halatta ayi mutum-mutumin wani abu mai ruhi ba, kana babu bambanci shin an yi shi da ababen yin mutum-mutumi ne ko kuwa da ababen yin kawa da wasunsu.
T938. Mene ne hukumcin tsage-tsagen da wasu mutane suke yi akan jikinsu ta yadda ba zai bace ba? Shin hakan za a kirga shi cikin garkuwa da yake kare fata ta sadu da ruwan wanka ko alwala?
A: Yin tsage tsage ba haram ba ne kana kuma alamarsa wacce take karkashin fata ba ta da wani tasiri na hana saduwar ruwan wanka ko alwala ga fata, don haka alwala da kuma wanka suna inganta tare da hakan.