T939. Mene ne hukumcin koyo ko koyarwa ko kallon rufa ido ko wasanni da suke da ban mamaki ta hanyar saurin hannu (zafin nama)?
A: Koyo ko koyar da rufa ido bai halatta ba, amma wasannin ban mamaki wanda ake yi da taimakon zafin nama ko saurin hannu kuma ba'a kidanya ta rufa ido babu laifi.
T940. Shin ya halatta a koyi ilimin hatimi ko bugun kasa ko makamantansu na daga ilmummukan da suke ba da labarin abubuwan da suke a boye?
A: Abin da ke hannun mutane na wadannan ilmummuka cikin wannan zamanin galibinsu ba ababen dogaro ba ne, ko kuma abin da rai zai nitsu da su na daga labarurrukan gaibun da suke fade, amma kuma ba laifi a nemi ilimin hatimi ko bugun kasa ta hanya ingantacciya amma da sharadin in barna ba ta shiga ba.
T941. Shin ya halatta a san sihiri a kuma yi aiki da shi, ko kuma a kirawo Aljani ko rauhani ko mala'ika?
A: Shi dai sihiri haram ne haka nan kuma saninsa, sai dai in ya kasance don wata bukata ce ta shari'a wacce masu hankali suka yarda da ita amma kiran rauhani, ko mala'ika, ko aljani, idan mun dauka yana inganta kana kuma gaskiya ne to yana sabawa da sabanin bukatu ko yanayi ko hanyoyi.
T942. Mene ne hukumcin muminai su je wurin mutane masu yin magani ta hanyar yin amfani da rauhanai ko kuma aljanu tare da yakinin cewa aikin alheri kadai suke aikatawa.
A: Yin haka a kan kansa bai da laifi in har da gaske akwai waraka a cikin hakan amma ta hanyoyin da shari'a ta halatta.
T943. Shin ya halatta a rika buga kasa a matsayin sana'a?