Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCIN DA YA SHAFI SHAN MAGANI DAN HANA DAUKAN CIKI
Ali Khamenei4

T845: (1). Ya halatta mace mai lafiya ta yi amfani da magani don hana daukan ciki zuwa wani lokaci?
(2). Mene ne kuma hukumcin yin amfani da maganin nan mai hana daukan ciki mai suna (I.U.D)? Wanda har yanzu kuwa an kasa gane ta yaya ne yake hana daukan ciki, illa kawai an san cewa yana hana shigar maniyi mahaifa.
(3). Kana shin matsalolin yau da gobe na tattalin arziki suna halatta a sha maganin da zai hana daukan ciki na har abada?
(4). Ko kuwa hakan yana halatta ne saboda cuta wacce ake tsorace wa ran mai cikin?
(5). Haka kuma dai shin yana halatta ga matan da haihuwarsu za ta taimaka wajen samar da yaran da suke da cututtuka na gado wanda zai shafi jikinsu ko ruhinsu su ki daukan ciki na har abada?

A: (1). Ba abin da zai hana mace ta sha magani don hana daukan ciki na dan wani lokaci muddun dai da izinin mijinta.
(2). Bai halatta ayi amfani da magani ba wanda aikinsa shi ne zubar da ruwan maniyi bayan ya riga ya shiga mahaifa, ko kuma zai janyo a kalli al'aura ko taba ta, irin wanda suka haramta.
(3). Rashin abubuwan masarufi na yau da gobe ko yawan 'ya'ya ko abin da ya yi kama da haka bai kamata mutum ya kula da ita ba yanda ta dalilinta zai hana wa kansa ciki na har abada.
(4). Ba laifi mutum ya hana ciki don gudun abin da aka ambata, kai yin ciki bai ma halatta ba in har zai janyo hadari cikin rayuwar ita uwar jinjiri, sai dai idan ya faru ne ba da zabi ba.
(5). Ba abin da zai hana hakan in har akwai manufa ta masu hankali a ciki kana kuma hakan ba zai jawo cuta sosai ba sannan ya kasance da izinin miji.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din