BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Abubuwan Tsoro Guda Uku
Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
" ﺇﻧّﻤﺎ ﺃﺧﺎﻑ ﻋﻠﻰ ﺃﻣﺘﻲ ﺛﻼﺛﺎً، ﺷﺤّﺎً
ﻣﻄﺎﻋﺎً ﻭﻫﻮﻯً ﻣﺘﺒﻌﺎً ﻭﺇﻣﺎﻣﺎً ﺿﺎﻻً "
"Hakika ina ji wa al'ummata
tsoron abubuwa uku: rowa
da ake mata biyayya, son rai
da ake binta da shugaba
batacce.
(Tuhaful-Ukul shafi na 58).
Rowa dai dabi'a ce da ta
kunshi kwadayi da rike
hannu. Wato kwadayin
neman tara kyale-kyalen
duniya da rashin taimako.
To sai dai wannan dabi'a ba
ta zama hatsari ga mutumin
da ke da ita matukar bai
biye mata ba. Hatsarin shi
ne lokacin da dabi'ar rowa
ta zame abar biyayya ga
mutum kuma ya mike ba ji
ba gani wajen tara kyale-
kyalen duniya ido rufe.
Son rai da ake binta sau da
kafa ita ce biyayya ga duk
wasu sha'awowin da
zuciyar mutum ta riya masa.
Wanda alakar dake tsakanin
dabi'ar rowa da ake mata
biyayya da halin son rai da
ake bi, alaka ce da halayen
biyu suke kama da juna a
wani bangare, sannan
kuma a wata fuskar suka yi
hannun riga.
Shi kuwa shugaba batacce
shi ne jagoran da ya kauce
hanya madaidaiciya, wanda
yake jagorantar al'umma
zuwa ga (wani abu)
sabanin gaskiya, kuma yake
janta zuwa ga bata da
halaka. Wannan batar ta
shugaba ta samo asali ne
daga dabi'ar rowa da son
rai. Don haka idan aka dubi
tarihi za a ga cewa kauce
hanya da halifofin daular
Umayyawa da na
Abasiyawa suka yi a
wancan zamanin ya samo
asali ne daga matakin da
suka dauka na bin son
ransu da sha'awowin
zukatansu. Saboda haka ne
dukkanin kokarin
Annabawa da Waliyan Allah
suka kasance wajen yaki da
wadannan abubuwa masu
hatsari guda biyu, wato son
rai da bin sha'awar zuciya.