T846: Shin ya halatta a zubar da ciki saboda matsalolin yau da gobe na tattalin arziki?
A: Sam bai halatta a zubar da ciki ba don matsalolin yau da gobe na abin da za'a ci.
T847: Farkon daukan ciki sai likita ya gaya wa mai ciki bayan bincike da ya yi cewa akwai hatsari a tare da ita muddin ta bar cikin, kana ma za'a haifi yaron da illa, don haka likitan sai ya sa a zub da cikin, shin yin hakan ya halatta? Shin kuma dai yana halatta a zubar da ciki kafin busa masa rai?
A: Don gudun haihuwar yaro mai illa bai halatta zub da ciki a shari'a ko da kuwa ba'a busa masa rai ba, amma tsoron lafiyar uwa da ci gaban rayuwarta sanadiyyar ciki in har likita ya yi nuni da hakan wanda yake amintacce kuma kwararre to ba laifi a zubar in har ba'a busa masa rai ba.
T848: Shin ya halatta a zub da maniyyin da ya shiga cikin mahaifa kafin ya zama jini, wanda hakan ya kan kai kamar kwana ar'ba'in, kana wane maniyyi ne ya haramta a zubar da shi? Lokacin da ya shiga mahaifa ne? Ko lokacin da ya zama gudan jini ne? Ko lokacin da ya zama tsoka ko lokacin da ya zama kashi kafin busa rai?
A: Bai halatta a zubar da maniyyi ba bayan ya shiga mahaifa ko a zubar da ciki. Cikin dukkan wadannan halaye bai halatta.
T849: Mene ne hukumcin zubar da ciki akan kansa? Kana kuma mene ne hukumcin zubar da shi lokacin da ya zama hadari cikin rayuwar uwa? Idan ya halatta shin akwai bambanci da wanda aka busa wa rai da wanda ba'a busa wa ba.
A: Zub da ciki haram ne a shara'ance, bai kuma halatta sai in har ya kasance hadari cikin rayuwar uwa to, ba laifi a irin wannan hali a zubar da shi kafin shigar rai, amma bayan shigar rai bai halatta ba ko da kuwa hadari ne ga rayuwar ita uwa sai dai idan kuma rashin zub da shi din zai kawo rasuwarsu ga baki daya, kuma ba zai yiwu yaron ya rayu ba ko ta kaka sai dai uwar za ta iya rayuwa saboda dalilin zubar da shi.
T850: Mace ce ta zubar da cikinta na zina wanda ya kai wata bakwai da umarnin babanta shin za ta biya diyya? In har za'a biya diyya waye zai biya daga cikinsu? Kana ga waye za a ba da diyyar? Sannan nawa ne abin da za'a biya a daidai wannan lokacin bisa fatawarka?
A: Haram ne a zubar da ciki ko da kuwa na zina ne, umarnin uba bai kau da laifin zubar da shi don haka idan ta aikata ko ta taimaka aka aikata dole ne ta biya diyya, amma akwai maganganu kan yawan adadin abin da za'a bayar illa ihtiyat a nan shi ne yin sulhu, kana diyyar tana kasancewa cikin hukumcin dukiyar gadon mutumin da bai da magada.
T851: Nawa ne diyyar cikin wata biyu da rabi wanda aka zubar da gangan? Kuma waye ya kamata a ba wa diyyar?
A: Idan ciki ya zamo gudan jini aka zub da shi diyyarsa dinari arba'in ne idan kuma har ya zama tsoka dinari sittin ne idan kuma ya yi kashi wanda ba nama dinari tamanin. Kana wannan diyya ana ba da ita ne ga wanda zai gaji jinjirin bisa marhalolin gado sai dai wanda ya zubar da cikin bai gadan komai a cikinta.