Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCIN SHIGAR DA CIKI TA HANYAR NA'URA
Ali Khamenei4

T852: Shin ya halatta a shigar da ciki ta hanyar na'ura in har maniyyin na ma'aurata ne aure kuma na shari'a? In ya halatta to shin wani likita ajanabiy zai iya yin wannan aikin kana yaron da aka Haifa 'dan ma'auran ne? Idan bai halatta ba shin in yin hakan shi zai kare auren nasu zai halatta ayi?

A: Ba abin da zai hana yin wannan aiki akan kansa illa dai kawai a nesanci abubuwan da suke haram don haka bai halatta ba wani namiji daban ajanabiy ya dau nauyin wannan aikin in har yin aikin zai janyo tabawa ko ganin abin da bai halatta ba kana kuma dai dansu ne muddun dai maniyyin nasu ne.
T853: Da za'a sami maniyyin mutum tun yana raye sai aka zura shi ta hanyar na'ura cikin mahaifar matarsa bayan ya rasu? Tambayar farko a nan ita ce shin yin hakan ya halatta? Tambaya ta biyu shin dan zai zamo dan mijin a shari'a? Tambaya ta uku shin wanda aka haifa zai gaji mai maniyyin?

A: Yin hakan ba laifi ba ne kana dan kuma na mai maniyyin ne da wacce ta haife shi, sai dai kuma ba zai gaji wanda ya haife shi ba.
T854: Shin ya halatta matar mutumin da ba ya haihuwa a sanya mata maniyyin wani mutum daban a cikin mahaifarta?

A: Babu hani cikin yin haka in har an nesanci abubuwan da suke haram misalin kallo ko tabawa ko makamantansu, sai dai kuma in an sami da ba na mijinta ba ne dan wanda aka zuba mata maniyyinsa ne, amma yaron dan matar ne, A nan ya kuma kamata a yi ihtiyat domin kubutar da kai cikin harakar gado da kuma nasaba.
T855: Shin ya halatta mace ta zuba ruwan maniyyin mijinta wanda ya rasu cikin mahaifarta?
1- Bayan rasuwarsa kafin gama iddarta.
2- Bayan rasuwarsa da gama iddarta.
3- Bayan ta auri wani namijin na daban.
Shin cikin wadannan halaye ya halatta ta zuba ruwa mijinta wanda ya rasu cikin mahaifarta? Ko kuma bayan mijinta na biyu shi ma ya rasu ya halatta ta zuba ruwan na farkon?
A: Ba abin da zai hana dukkannin wadannan abubuwan illa kawai in mijinta na biyu yana da rai lallai ne ta nemi izininsa.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


pacman, rainbows, and roller s