T856: Akwai mutanen da a zahirinsu maza ne, sai dai kuma suna dauke da wasu abubuwa na mata ta bangaren yanayin hankalinsu kana suna da cikakkiyar karkata zuwa ga jinsin mata, ta yanda in har ba'a yi saurin canza halittarsu ba za su fada cikin barna. Shin ya halatta ayi musu jiyya ta hanyar mayar da su mata bisa yi musu (tiyata)?
A: Ba laifi ba ne ayi irin wannan tiyata idan don gano hakikanin yanayinsu ne da sharadin in har ba za'a afka cikin haram ba kana ba zai jawo barna ba.
T857: Mene ne hukumcin yin tiyata ga mata-maza don a mai da shi mace ko namiji?
A: Ba laifi akan kansa muddin dai za a kiyaye abubuwa na haram da suke tattare da haka.