Duck hunt
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCIN FEDE MAMACI DA NUFIN YIN BINCIKE KO CIRE WATA GABA TASA
Ali Khamenei4

T858: Saboda gano wasu cututtuka na zuciya, ko kananan jijiyoyin da suke hade da ita, ko kuma don gudanar da wani bincike shin ya halatta a fede jikin mamaci wanda yake musulmi domin gudanar da wadannan abubuwan? Kana in an gama shin ya halatta a binne zuciyar ko jijiyar a wani wuri daban ba tare da jikin da aka ciro ta ba? Kamar yanda kuma binne zuciya ko kuwa jijiya ita kadai bayan bincike zai wahala to ya halatta a hada ta da wata gawar a binne ta?

A: Ba laifi a fede jikin mamaci in har za'a ceto wani ran ne ta hanyarsa ko kuma da nufin yin bincike don abin da al'umma take da bukatarsa, ko kuma don nufin gano wata cuta da take barazana ga rayuwar mutane, sai dai in za'a sami wanda ba musulmi ba to a wannan lokacin wajibi ne rashin yi da musulmi, amma kuma gabbai wanda aka ciro su daga jikin musulmi lallai ne a binne su tare da jikin muddin in hakan zai yiwu, in ko ba zai yiwu ba sai a binne ta ita kadai ko tare da wata gawar daban.
T859: Shin ya halatta a tono kaburburan musulmi da wanda ba na musulmi ba don a debo kasusuwansu a yi amfani da su kan bincike cikin makarantun horar da likitoci?

A: Bai halatta a tono kaburburan musulmi ba, sai dai in ya kasance akwai tsananin bukatar haka ta fuskar magani kana kuma kasusuwan wanda ba musulmi ba ba zai samu ba.
T860: Shin ya halatta a dasa gashi akan mutumin da gashinsa ya kone ga wanda idan bai yi hakan ba zai rika jin kunya da takura a tsakanin mutane?

A: Karin gashi ba haram ba ne da sharadi gashin ya kasance na dabbar da ake ci ne ko kuma gashin mutum ne.
T861: Ina so in yi kyautar gabobina domin ayi amfani da su bayan na mutu don haka na ba wa hukumar da abin ya shafa labarin haka sai suka nemi na rubuta hakan cikin wasiyya kana na ba wa magada labari shin ina da hakkin yin haka?

A: Ba laifi a yi amfani da gabban mamaci domin a saka a jikin wani da nufin ceto ransa, ko warkar da ciwonsa ba kuma abin da zai hana a yi wasiyya kan haka, sai dai kuma bai halatta a ciri gabar da cire ta zai zama alama ce ta cin mutunci ga mamacin ba, bisa yanda al'ada take gani (wato a idon jama'a).
T862: Mene ne hukumcin gyaran jiki ta hanyar tiyata don kara futo da kyan mutum?

A: Yin haka babu laifi akan kansa.
T863: Shin ya halatta a sai da gabobi ga masu bukata.

A: Babu laifi cikin yin haka in har babu cutarwa, wanda ya wajaba a kiyaye musamman ma idan kare wani rai daban ya rataya ne akan hakan to babu laifi.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din