Polly po-cket
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCE HUKUMCEN DA SUKA SHAFI GANIN LIKITA DA YIN MAGANI
Ali Khamenei4

T864: Shin ya halatta hukumar da take da nauyin daukan sojoji ta binciki al'aurar wasu don ganin ko suna da kaciya ko don neman yi musu magani? Ya halatta a tilasta su kan a yi musu binciken?

A: Bai halatta a bude al'aurar wani ba kana bai halatta a kalle ta ba, kana bai halatta a tilasta masa da ya bude al'aurarsa gaban mutanen da bai halatta su gani ba sai da larura, don yin kaciya ko kuma magani, to amma ba aikin mutane ba ne su nemi yi wa mutumin da ya balaga kaciya wannan abu ne wanda ya shafi shi mutumin haka nan ma ba wajibi ba ne a tilasta yi masa magani, sai inda mutanen suka ji tsoron in ba su nemi yi masa ba za ta kai shi ga halaka.
T865: Budurwar da take hijabi yar shekara goma sha hudu, sai aka jarrabe ta da ciwon kai, ta je wajen likita ba sau daya ba ba sau biyu ba suna nuna cewar sai ta cire hijabinta kana za ta samu sauki, kana ita ma kuma akan kanta kamar yadda ta fuskanta in har ta cire hijabin nata kan nata yana samun sauki to shin ya halatta ta cire hijabin nata? Ta ci gaba da fita kanta a waje?

A: Ba laifi ba ne ta cire hijabinta daga kanta ta zabi zama alhali babu shi a kanta sai dai kawai bai halatta ta je gaban wasu ba ko ta fito daga gida ba tare da hijabin ba sai a halin lalura.
T866: Shin ya halatta likita mace ta bude al'aurar mace don nufin yin bincike da gano cuta?

A: - Ba abin da zai hana yin haka in har larura ta ratsa.
T867: Shin ya halatta likita namiji ya taba jikin mace ko ya kalle shi domin yin magani?

A: In har da larura kan cewa dole sai ta bude jikinta ya taba ko ya kalla, wanda kuma ba mace likita wacce za ta je wajenta, ba laifi ya taba din ko ya gani.
T868: Shin ya halatta a fitar da maniyyi idan likita ya yi umarni da hakan don yin wani bincike?

A: Ba abin da zai hana yin haka a matsayin magani, in har maganin ba zai yiyu ba sai ta wannan hanya.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din