A: Kaciya ga maza wajibi ce, kana ma sharadi ne na karbar dawafi cikin aikin hajji da umara. Da mutum zai zauna bai yi ba har bayan balaga, to ya zama wajibi ya yi.
T870: Mutumin da bai yi kaciya ba sai dai kuma kan kaciyar tasa ya fito gaba daya shin shi ma dole ne ya yi kaciya?
A: In har ba wani abu da ya kare kan kaciyar tasa na loba wacce yake zamowa wajibi a yanke to ba lallai ba ne ya yi kaciya.
T871: Shin wajibi ne a yi wa yara mata kaciya?