XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

HUKUMCE HUKUMCE KAN KARATUN LIKITANCI
Ali Khamenei4

T872: Dole ne dalibai maza ko mata wajen karatun likitanci su shafi ko su kalli wadanda ba muharramansu ba domin koyon wani abu, wanda wannan binciken yana daga cikin tsarin koyarwa na darasussuka, wanda kuma ba makawa sai an yi domin da hakan ne za'a iya maganin wata cuta mai zuwa na gaba idan har ba'a yi ba yana janyo rashin gano cuta nan gaba, wanda hakan zai janyo mara lafiya ya gaza warkewa da wuri har ma takan kai ga rasuwa a wasu lokutan. To shin irin wannan binciken ya halatta?

A: Babu laifi cikin halaccin yin binciken cuta ga wanda ba muharrami ba in har akwai larurar yin hakan da nufin gano cuta da saninta da maganinta da kuma tsamo rayuka.
T873: Shin ya halatta a kalli hotunan mutanen da ba musulmi ba wanda aka yi su kamar tsirara-tsirara wanda suke cikin littattafan koyon likitanci domin karatu?

A: Ba abin da zai hana in har ba'a yi nufin haram ko kuma jin dadi ba, kana ba a ji tsoron afkuwar barna ba.
T874: Daliban jami'a wadanda suke koyan likitanci a lokacin darasinsu akwai zamanin da suke kallon hotuna ko kuma fina-finai daban daban na gabobin jiki da nufin koyon wani abu? Shin hakan ya halatta? Kana kuma mene ne hukumcin kallon al'aura cikin wannan hali ga wanda ba jinsinsa ba ko jinsinta?

A: Babu laifi cikin kallon fina finai ko kuma hotuna kawai, muddun dai ba da nufin jin dadi ba ko kuma tsoron fitina domin abin da yake haram shi ne kallon jikin wanda ba jinsinsa ba ko nata da shafarsa, amma kallon fim ko kuma wani hoto na al'aurar wani, akwai matsala a cikinsa.
T875: Mene ne abin da ya kamata mace ta yi lokacin haihuwa, kana kuma mene ne ya halatta ungozoma ta yi dangane da bude al'aura da kallon ta?

A: Sam bai halatta ga ungozoma ta kalli al'aurar mace ba lokacin haihuwa sai in har da larura, haka ma likita dole ne ya nesanci kallon jikin mara lafiya mace ko kuma shafa muddin dai babu larura kan yin hakan, kuma dole ne mace ta rufe jikinta in har tana fadake kuma tana da ikon rufewar ko kuma ta nemi wani ya rufe mata.
T876: Shin ya halatta ungozoma ta kalli al'aura a lokacin da take koyon aikin ungozomanci?

A: Kallon al'aura domin koyon wani abu sam bai halatta ba, sai dai idan ya rataya kan maganin wata cuta ce mai hadari da ceto rai wanda maganin yana tattare da a koye shi ta hanyar kallon al'aura.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din