BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!
Albarkokin Watan Ramalana Mai Albarka
Darussan Watan Ramalana Mai Albarka
Hakika watan Ramalana wata dama ce ga musulmi da wajibi ne su yi amfani da ita wajen karfafa rayuwarsu ta duniya da lahira. Daya daga cikin darussan da ake samu a watan Ramalana ta hanyar addu'oi, azumi da karatun Alkur'ani mai girma, wanda wajibi ne a yi kokarin amfanuwa da shi, shi ne tunawa da fakirai da marasa shi sakamakon zama cikin yunwa da kishirwa. A cikin addu'ar ranakun watan Ramalana mai albarka muna karanta cewa: "Ya Allah Ka arzurta duk wani fakiri, Ya Allah Ka ciyar da duk wani mai yunwa, Ya Allah Ka tufatar da duk wani maras sutura" wannan addu'a ba wai kawai addu'a ce ta ranakun watan Ramalana ba, a'a kira ce ga kowa wajen shirin fada da talauci da kokari wajen share kurar talauci da rashi daga fuskar fakirai da marasa shi (kokari wajen biyan bukatun mabukata). Wannan nauyi na gaba daya dake kan kowa da kowa. A cikin Alkur'ani mai girma ma muna karanta cewa"Shin ka ga wanda ke karyata ranar sakamako. To wannan shi ne mai ingije maraya. Kuma ba ya kwadaitarwa kan ciyar da matalauci"(Suratul Ma'un 1-3). Daya daga cikin alamun karyata addini shi ne nuna halin ko in kula wajen fada da talaucin da marashi shi suke fama da shi. A watan Ramalana muna iya fahimtar yadda marasa shi suke ji sakamakon rashin abinci da abin sha da sauran abubuwan da suke bukata. Wajibi ne hakan ya sanya mu jin shu'urin sauke nauyin da Musulunci ya dora mana dangane da mas'alar talauci da taimakon marasa shi da yin duk abin da za mu iya wajen sauke wannan nauyi...
Wajibi ne kowa ya ji cewa akwai wani nauyi a kansa na cewa bai kamata ya bar wani iyali daga cikin iyalan musulmi da sauran al'ummomin da suke rayuwa tare cikin talauci da rashi ba, ya ji cewa akwai wani nauyi a kansa na ya taimaka musu. A yau wannan wata bukata ce ta duniya baki daya ga dukkanin al'ummomi dake da alaka da yanayi na tausayi da kyawawan dabi'u. A wajen musulmi kan baya ga kasantuwarsa wani nauyi ne na dan'Adamtaka da tausayawa, har ila yau wani nauyi kuma na shari'a.
Wajibi ne ku taimakawa makwabtanku da sauran marasa shi. Daya daga cikin batutuwan da ke da muhimmanci cikin batun taimakon fakirai da mika musu hannun taimako shi ne batun almubazzaranci da son kawa tsakanin al'umma. Babban bala'i ne a samu ruhin yaduwar almubazzaranci, wuce haddi wajen amfani da abubuwan rayuwa, yawan ci da sanya tufafi kala-kala, yawan nuna kai da kokarin yin ado ba gaira ba dalili tsakanin al'umma. Allah kadai ya san irin dukiyar da ake wasa da ita da hana aiwatar da ayyukan da ake samun yardar Ubangiji a cikinsu sakamakon almubazzarancin da ake yi.
Darussa Na Aikace Da Ake Samu Cikin Watan Ramalana
Wani abin da nake son tunasar da al'ummarmu cikin wannan huduba shi ne cewa mafi girman darasin watan Ramalana mai albarka shi ne gina kai da tsarkake shi. Matakin farko kuma mafi muhimmanci na gina kai shi ne mutum ya sanya dabi'u da halayensa bisa mizani don ganin nakasin da yake da shi da kokarin magance shi. Hakan wani nauyi ne da ke kanmu gaba daya.
Ina kiran al'umma da cewa: Ku tausayawa junanku sai Allah Ya tausaya muku. Kada masu karfi su yi kokarin wuce haddi da cutar da sauran mutane da take musu hakkokinsu. Kada wani ya yi amfani da karfin dukiya ko mukami na daidaiku da na jama'a da yake da shi wajen wuce haddi kan sauran mutane da take musu hakkokinsu. Ya kamata mu ji cewa mu bayin Allah ne; mu ji cewa muna da nauyin zama tare, kyautatawa da taimakon wadanda muke tare da su, to a irin wannan yanayi ne rahamar Ubangiji za ta sauka a kanmu. Koda yake hakan nauyi ne dake kan kowa; to amma ya fi hawa kan wadanda suke da karfi, dukiya, mukami da fadi a ji cikin al'umma.Dangane da watan Ramalana, a yau na zabo mana ‘yan wasu jumloli ne daga cikin hadisi na arba'in da hudu na cikin littafin ‘Sahifat Sajjadiyya' da suka shafi wannan wata na Ramalana don karanto mana su. To sai dai kafin hakan ina kiran al'ummarmu musamman matasa da su lizimci wannan littafi na Sahifat Sajjadiyya, don kuwa akwai dukkanin abubuwan da ake bukata cikin wannan littafi wanda a zahirinsa na addu'a ne amma a badininsa littafi ne da ya kumshi dukkan komai. Imam Sajjad (a.s) cikin wannan addu'a kamar sauran addu'oin da suke cikin littafin Sahifat Sajjadiyyan yana magana ne tamkar yana kafa hujja da kuma koyar da tarbiyya alhali yana mai kaskantar da kansa ga Allah Madaukakin Sarki. Mafi yawa daga cikin addu'oin Sahifat Sajjadiyya - a iyakacin sanina - suna da irin wannan yanayi. Komai a tsare yake, tamkar wani mutum ne yake zaune a gaban masu saurare yana musu magana cikin hikima.
A nan ma haka lamarin yake. A addu'ar farko da nake son magana a kanta Imam Sajjad (a.s) yana cewa: "Muna gode wa Wanda Ya sanya mu daga cikin ma'abutanta (godiyar)" (addu'a ta 44 ta cikin Sahifat Sajjadiyya), wato ba mu gafala daga ni'imomin da Allah Ya yi mana ba, don haka muke gode masa. Allah Madaukakin Sarki Ya bude mana hanyoyi don mu gode masa. Kamar yadda kuma ya tsara mana hanya da tafarki sannan kuma ya ba mu damar bin tafarkin.
Daga nan sai wannan jumla da take cewa: "Sannan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya sanya watanSa watan Ramalana daga cikin wadannan hanyoyi". Wato muna gode wa Allah da ya sanya watan Ramalana ya zamanto daya daga cikin hanyoyin isa gare shi da kuma isa ga kamala da taskar girmanSa. A nan Imam (a.s) yana ishara ne da ‘watanSa' (watan Ramalana) a matsayin daya daga cikin wadannan hanyoyi. Akwai cikakkiyar ma'ana cikin hakan. Idan muka duba da kyau za mu ga cewa dukkanin watanni na Allah ne, to amma a fili yake cewa a lokacin da Mamallakin dukkan komai Ya ware wani abu ya nasabta shi gare Shi to hakan yana nuni da muhimmancin gaske da wannan abu yake da shi ne. Daya daga cikin abubuwan da Allah Ya kebance shi shi ne wannan wata na Ubangiji. Hakan kawai ya isa ya zamanto falala da daukaka ga watan Ramalana, wannan wata na azumi kuma wata na Musulunci. Watan da azumi a cikinsa yana daga cikin lamurra masu muhimmancin gaske wajen tsarkake zuciya, saboda a cikinsa ne ake fada da yunwa da sauran abubuwan da zuciya take so.
"Wata ne na mika kai ga Allah Madaukakin Sarki". A matsayin misali za a ga cewa a lokacin da wani saurayi ya dauki azumi, ga yunwa ga kishirwa sannan kuma ga sauran ababen sha'awa da suke jan hankulansa, to amma duk da haka ya kan yi tsaye wajen fada da dukkan wadannan ababen sha'awa. Mene ne dalilin hakan? Don biyayya ga Allah Madaukakin Sarki ne. Hakan shi ne mika wuya ga umurnin Allah. Babu wasu ranaku na shekara da dan'adam yake mika kai cikin sauki ga Allah Madaukakin Sarki kamar yadda yake yi a watan Ramalana. Don haka watan Ramalana wata ne na mika wuya ga Allah Madaukakin Sarki.
Darussa Na Aikace Da Ake Samu Cikin Watan Ramalana
Imam, ya ci gaba da cewa: "sannan wata ne na tsarki" wato wata ne na tsarkake zuciya. A cikin wannan wata akwai abubuwan da suke tsarkake mana ruhinmu. Mene ne wadannan abubuwa? Daya daga cikinsu shi ne azumi, wani abin kuma shi ne karatun Alkur'ani mai girma, dayan kuma shi ne addu'a da kankan da kai (ga Allah Madaukakin Sarki). Irin wadannan addu'oi dukkansu ni'imomi ne da Allah Ya ba je su a kan shimfidar liyafar bakunci gare mu don mu amfana da su. A takaice abin da maganar Imam (a.s) take nufi shi ne cewa Allah Madaukakin Sarki yana tarbar bakinsa ne a cikin wannan bakunta nasa da azumi...
Daga nan kuma sai ya ci gaba da cewa: "sannan kuma watan tsarkake kai" wato wannan wata ne da za mu tsarkake kanmu (da ayyukanmu su zamanto dukkan abin da za mu yi ya zamanto saboda Allah ne)....
Wannan wata ne na wanke kai, idan muka duba da kyau za mu ga cewa tsarkake kai a cikin watan yana da saukin gaske. Saboda da wannan azumi da fada da son zuciya, za mu iya tsarkake kanmu. Mafi yawa daga cikin batan da muke gani ko dai saboda sabon da muke aikatawa ne ko kuma saboda irin abubuwan da suke fitowa daga gare mu ne.
Watan Ramalana na kowace shekara wani bangare ne na Aljanna da Allah Madaukakin Sarki Yake shigar da mu cikinta daga wutar jahannaman wannan duniya da kuma ba mu damar shiga aljanna ta hanyar zama kan shimfidar liyafar Ubangiji a wannan wata. Wasu su kan shiga wannan Aljanna ne na tsawon kwanaki talatin (na watan). Wasu kuma saboda wadannan ranaku talatin sukan shiga Aljanna na tsawon dukkan shekara, wasu kuma na dukkan rayuwarsa, wasu kuma sukan wuce su ne cikin gafala wanda hakan babban abin bakin ciki ne. To shi kan mutumin da yaki amfanuwa da irin wannan gagarumar ni'ima da kamala da ake samu a wannan shimfida ta Ubangiji a watan Ramalanan ba a maganarsa, to amma duk wanda da ya ganshi (cikin irin wannan yanayi) yana da hakkin ya tausaya masa. Haka watan Ramalana yake. Wata ne na bakuncin Ubangiji. Wata ne dake da Lailatul Kadri a cikinsa....
Daya daga cikin mafi girma da muhimmancin manufar azumin watan Ramalana - ko kuma ana iya cewa dukkan manufar - ita ce tsoron Allah "Ko kwa ji tsoron Allah". Hakan kuwa a hannunmu yake. Wajibi ne dukkanmu mu gyara kanmu idan ma za mu iya har da wasu. Hakan ba lamari ne da ya kebanci malamai ba, duk da cewa malamai da sauran masu wa'azi suna da shiri sosai sama da saura. Saboda Allah Madaukakin Sarki Ya ba su karfin bayani, kwarewa da wannan matsayi na al'umma don haka wajibi ne mu yi amfani da wannan dama. Daya daga cikin abubuwan da ake samunsu cikin sauki a wannan wata na Ramalana, wanda kuma Allah Madaukakin Sarki a fili Ya yi bayani kansa shi ne cewa "Lailatul Kadri yafi watanni dubu. Mala'iku da Ruhu (Mala'ika Jibrilu) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni. Aminci ne shi daren, har fitar alfijir (Suratul Kadr: 3-5) wani dare ne da ake samun amincin Ubangiji a cikinsa har zuwa asubahi (سلام قولاً من رب رحیم) hakan ya kebanci muminai ne kawai. Ya kebanci mutanen Aljanna ne. Ya kebanta ne ga bayin Allah da suka tsarkake zukatansu. An ba mu hakan ne don mu amfana da shi. Wannan shi ne abin da nake son fadi dangane da abin da ya shafi watan Ramalana. Hakan ya zamanto wani mabudi ne na dukkan al'amurra; daga nan ne ake farawa. Kamar yadda asalin juyin juya hali daga wajen ya faro, wato daga masallaci da addini.
Watan Ramalana wata babbar dama ce ta tsarkake kai. Mu tamkar danyen sinadari ne da idan muka yi aiki a kan kanmu da samun nasarar mai da wannan sinadari zuwa ga yanayi mai kyau to lalle mun aikata abin da ya dace mu aikata a rayuwa. Hakan shi ne asalin manufar rayuwa. Kaicon mutanen da suka gagara yin wani abu wa kansu a bangaren ilimi da aiki, sannan kuma suka bar duniya kamar yadda suka zo duk kuwa ma da irin tsatsa da lalacewa da fasadin da suke tasowa wa dan'adam tsawon rayuwa. Wajibi ne a koda yaushe mumini ya kasance mai kula da kansa da aiki don karfafa shi. Bai kamata wani yayi zaton don an ce koda yaushe ya kasance cikin hakan yayi tunanin hakan ya yi yawa ko kuma ma abu ne da ba zai yiyu ba, koda wasa. Abu ne mai yiyuwa kuma bai yi yawa ba. Matukar mutum ya kula da kansa, ya nesanci ayyukan da aka hana ko kuma wadanda suka saba wa shari'a sannan kuma ya kama hanyar Allah da dukkan karfinsa to babu makawa zai yi nasara. Hakan shi ne gina kai na koda yaushen da ake magana kansa wanda tsare-tsare, ko shakka babu koyarwar Musulunci sun yi daidai da wannan gina kai na koda yaushe da ake magana kansa. A matsayin misali ita kanta sallar da ake yinta sau biyar (rana), zikirin da ake ta yi, nanata fadin kalmar "Kai muke bautawa kuma daga wajenka muke neman taimako", haka nan ruku'i da sujadar da ake yi wa Allah Madaukakin Sarki ana masa tasbihi da godiya, don me ake dukkan wadannan abubuwa? Dalilin shi ne don mutum ya zamanto cikin yanayin gina kansa a koda yaushe. Koda yake akwai matsaloli da yawa kuma kowannenmu yana da tasa matsalar da take damunsa. Wato matsala ta rayuwa, matsaya ta daidaiku, matsala ta iyali da ‘ya'yaye da sauransu wadanda suke hana mu ayyuka don kanmu kamar yadda ya dace. Don haka ne wannan wata guda na Ramalana da Allah Ya ba mu sai mu yi kokarin amfanuwa da shi. Kada mu yi wasa wannan wata ya kubuce mana.
Abin da nake nufi shi ne cewa matukar ba za mu iya dawwama cikin kokarin gina kanmu da kula da shi ba, to alal akalla mu yi kokarin amfanuwa da watan Ramalana mana. Muna da karfin aikata hakan. Daya daga cikin mafi girman irin wannan karfi da muke da shi shi ne dai wannan azumi da muke yi a watan Ramalana. Hakan daya ne daga cikin mafi girman nasara ta Ubangiji gare mu. Wace irin nasara kenan? Nasara a nan tana nufin Allah Madaukakin Sarki Ya samar wa dan'adam abin da ya dace. Don haka ta hanyar wajabta azumi Allah Madaukakin Sarki Ya share mana hanyar da ta dace wajen samun nasarar gina kanmu a wannan wata. Azumi ni'ima ce ta Ubangiji mai girman gaske. Cikinmu dai ba komai a cikinsa don haka wata dama da hanye ce da muka samu ta fada da zuciya ya zuwa wani haddi cikin rana. Ba za ku iya cin abin da kuke so ko kuma shan abin da kuke so ba sannan kuma kun hana kanku amfani da abubuwan da zuciyarku take so na tsawon wani lokaci. Haka wani kokari ne na fada da zuciya don samun damar gina kai wanda shi ne kan gaban dukkan ayyuka.
Watan Ramalana wata babbar dama ce da Allah Madaukakin Sarki Ya ba mu don mu sami damar gina kanmu. Baya ga cewa sa'oin wannan wata suna da albarkoki da yawa da Allah Madaukakin Sarki Ya tsara su haka nan. Ladar raka'a guda ta salla da kuka yi a wannan wata, zikiri da fadin Subhanallah da kuka yi, ‘yar sadakar da za ku bayar da sada zumuncin da za ku yi a wannan wata ta nunnuka ladar irin wannan aiki da kuka aikata a wani watan na daban ba Ramalana ba. Hakan wata babbar dama ce. Hanya ce da ta dace mutum ya bita wajen gidan kansa a wannan wata mai alfarma.
Hakikanin Ikhlasi
Daya daga cikin siffofin da suke da muhimmanci da ya kamata mu kula da su a kokarin gina kanmu wanda mai yiyuwa ma ana iya gabatar da shi kan sauran abubuwa shi ne ikhlasi (cikin ayyuka). Ikhlasi shi ne aikata wani abu don Allah Madaukakin Sarki kawai. A wasu lokuta a kan sami wani mutum da ba ruwansa da ibada sam-sam a wasu lokutan kuma ya kan yi sai dai ba kawai don Allah Shi kadai ba. Ikhlasi da tsarkake ayyuka yana nufi yin Allah don neman yardar Madaukakin Sarki Allah kawai.
Na rubuto mana wata ruwaya da take magana kan ikhlasi da zan karanto muku ita. An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: "Kowani abu yana da hakikaninsa".
"Hakikanin ikhlasi bai riske bawa ba" sai dai mutum ba zai iya kaiwa ga ikhlasi na hakika ba ta yadda "ba ya so a gode masa kan wani abin da ya aikata don Allah". Hakan lamari ne mai wahalar gaske kuma matsayi ne mai girman gaske, wato mutum ba ya so a jinjina masa kan wani aiki da yayi don Allah.
Na ga irin wannan siffa a lokuta da daman gaske tattare da marigayi Imam (Khumaini), Allah Ya kara masa yarda. A lokuta daban-daban na ga hakan cikin ayyukansa. Bai damu da cewa wai abin da zai aikata zai dadada wa wani rai ko kuma a'a, shi dai yana kokarin sauke nauyin da ke kansa ne (da kuma neman yardar Ubangiji Madaukakin Sarki). A lokacin da nauyi yake da yawa, lokacin da ayyuka suka zamanto masu girma, lokacin da hatsari yake cikin wani aiki, to anan ana bukatar tsarkakekkiyar zuciya da ikhlasi mai yawan gaske.
Darussa A Aikace Da Ake Samu A Watan Ramalana
Yanzun nan na tuna cewa yana da kyau in yi muku ishara da nafilolin nan na raka'oi talatin da hudu na sallolin dare da rana da suka zo cikin wata ruwaya, shi ya sa na ga ya dace in sanar da ku, lalle suna da muhimmancin gaske. Watan Ramalana wata babbar dama ce. Mu dai ba ma'abuta sallolin nafila ba ne, amma idan watan Ramalana ya shigo mai zai hana mu zama hakan? Wani aiki ne ya fi salla alhali mutum yana cikin halin rike baki (azumi)? Raka'oi hudu na sallar azahar kafin hakan kuma akwai wasu raka'oi takwas na nafila, wato salloli hudu masu raka'oi bibbiyu. Haka nan sallar la'asar tana da raka'oi hudu sannan kafinta kuma a yi wasu raka'oi takwas na nafilar sallar la'asar. Ku lizimci yin wadannan nafiloli. Haka nan nafilolin sallar magariba wadanda suka fi wadancan muhimmanci. Sai kuma nafilolin dare wadanda raka'oi sha daya ne. Sai kuma nafilar sallar asubahi wacce raka'a biyu ce. Akwai wadansu mutane da tashi kafin sallar asuba don yin sallar dare a sauran ranakun shekara ya kan yi musu wuya. To amma a wannan wata (na Ramalana) sukan tashi. Hakan wata nasara ce daga Ubangiji. Me ya sa ba za mu amfana da wannan nasara ba? Ina rokon Allah Ya ba mu damar amfanuwa da damar dake cikin watan Ramalana.
Akwai Albarkoki Masu Ban Mamaki Cikin Watan Ramalana
Watan Ramalana wata ne dake cike da albarkoki sannan kuma yana da fagage masu yawa. Irin masaniyyar da musulmi suke samu dangane da Alkur'ani mai girma da addu'a da zikiri da salla da sauran mas'aloli na addini a duk inda suke a aikace ne ko kuma a akidance ba za su taba samunsa a wani wata na daban ba.
Don haka akwai albarkoki masu ban mamaki a cikin wannan wata. Yayin da nake duba jerin abubuwan da suka yi daidai da wannan wata na fahimci cewa wannan wata wata ne dake cike da addu'oi daban-daban a bangarorin daban-daban...lizimtar Alkur'ani, samun masaniyar Alkur'ani, haddace Alkur'ani, yawaita karatun Alkur'ani wanda shi kansa wani fage ne na daban. Sauran lamurran ma haka suke.
Komawa Ga Rayuwar Amirul Muminin, Daya Ne Daga Cikin Albarkokin Watan Ramalana
Daya daga cikin albarkokin wannan wata na Ramalana shi ne komawa ga rayuwar Amirul Muminin kuma Shugaban masu tsoron Allah Aliyu bn Abi Talib, amincin Allah su tabbata a gare shi. Babu wani lokacin da za mu samu wannan damar ta dubi cikin rayuwar Amirul Muminin da fahimtar bangarorinta daban-daban. Babu wani cikin sauran mutane ko masu wa'azi ko jami'an gwamnatin kasashen musulmi - wadanda a yau su suka fi kowa bukatar wannan masaniya - da yake da damar samun wannan dama ta (fahimtar rayuwar Amirul Muminin) a wani wata na daban da ba Ramalana ba. Kowani mutum, kowani jami'in gwamnati - komai girman matsayinsa ko kuma kankancinsa - yana bukatar masaniya dangane da rayuwar Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da dukkanin bangarorinta.
Mas'ala ta asasi cikin watan Ramalana ita ce mutum - wanda abubuwan da suke sanya a gafala daga Ubangiji da kuma wadanda suke lalata rayuwa suka yi masa kawanya - ya yi kokarin samun damar daukaka ruhinsa zuwa ga madaukakin matsayi da samun kusanci ga Allah Madaukakin Sarki da misaltuwa da ayyukan kwarai. Watan Ramalana shi ne watan da ke ba da irin wannan damar.
Koda yake a wasu watannin ma da ba na Ramalana ba akan samu wasu dama. A matsayin misali wadannan salloli biyar na ranaku su kansu wata dama ce da mutum zai iya amfani da ita wajen daukaka ruhinsa; mu sami damar gyara kanmu da nesantar da duk wata cuta da gafala daga gare mu. Lalle salla wata babbar dama ce. Matukar ba ku taba gwada hakan ba - duk da cewa bisa al'ada kun gwada kuma cikin ikon Allah hakan shi ne aikinku na kullum - to ku gwada ku gani. Za ku gane cewa a lokacin da kuke salla, matukar kun tsai da hankalinku waje guda da daidaita shi, ko shakka babu za ku fahimci cewa akwai bambanci tsakanin lokacin da kuka idar da sallar da yadda kuke kafin sallar, amma fa da sharadin cewa kun san me kuke yi lokacin da kuke sallar. Yana da kyau ku san me kuke fadi yayin da kuke yin zikirin sallar, hakan kuwa lamari ne mai sauki.
Salla Mi'irajin Mumini Ne
Bai kamata mu ce mu farisawa ne don haka ba za mu iya fahimtar abin da ake fadi da larabci ba. Saboda fahimtar dukkanin kalmomin da ake fadi a cikin salla - tun daga farkonta har zuwa karshenta - lamari ne mai saukin gaske ba zai dauki sama da awa guda ba. Akwai littafan da aka rubuta wadanda a cikinsu an tarjama wadannan kalmomi. Idan har kuka ba da muhimmanci ga ma'anoninsu, ku ka fahimci abin da suke magana kai sannan kuka yi tuntuni cikinsu shi ya fi. Idan ma hakan bata samu ba, to alal akalla yayin da kuka yi sujada ku san cewa kuna magana ne da Allah Madaukakin Sarki, haka nan lokacin ruku'i ku san cewa kuna girmama Ubangiji ne, haka nan lokacin da kuke karatu da zikiri ku san da wa kuke magana. Hakan yana da muhimmancin gaske.
Matukar aka samu irin wannan kulawa sannan aka tabbatar da tunani da ambaton Allah yayin salla to kuwa wannan salla za ta zamanto muku ‘mi'irajul mumin' sannan kuma za ku sami daukaka. Wannan daukaka shi ne bayan salla ku ji cewa lalle kun sami wani sauyi sannan zuciyarku ta haskaka. Dukkanin nau'oi na ibada dama ce gare mu, to sai dai watan Ramalana wata dama ce ta musamman cikin shekara.
Tsawon wadannan kwanaki talatin ko ashirin da tara baya ga salloli biyar na rana da kuma sauran nafiloli da a koda yaushe mutum yana iya yinsu akwai addu'oin da ake yinsu wadanda suke kara wa zuciyar mutum haske. Wadannan addu'oi dai an ba mu su. Sannan kuma an koyar da mu yadda za mu yi magana da Allah Madaukakin Sarki da yin munajati da shi. An koya mana irin kalmomin da za mu yi amfani da su yayin ganawa da Ubangiji Madaukakin Sarki. Wasu daga cikin wadannan addu'oi an samo su ne daga wajen Imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su, wadanda idan da ba don su ba mutum ba zai iya ayyana yadda za a iya gabatar da bukatu ga Allah Madaukakin Sarki ba.
Baya ga wadannan, shi kansa azumin watan Ramalanan wata hanya ce ga mai azumi ta tsarkake zuciya da haskaka ta sannan kuma da shiri don samun wannan ni'ima ta Ubangiji. Matukar kuka lizimci salla da sauran ayyukan da aka tsara sannan kuma da azumi da addu'oin da ake yi sannan kuka kara da karanta Alkur'ani mai girma to za ku sami nasarar tsarkake kanku da tsamar da ita daga tsatsa da fasadi da sauran bala'oin da suka cika duniya. Don haka watan Ramalana wata ne mai tsananin amfani.
Kusanci Zuwa Ga Allah A Watan Ramalana
Abin da ke da muhimmanci shi ne mu yi kokarin samun damar kusantar Ubangiji a watan Ramalana, hakan kuwa abu ne mai yiyuwa. A baya na gaya muku cewa a wasu lokuta bayan karewar watan Ramalana na kan tafi wajen marigayi Imam (Khumaini), Allah Ya yi masa rahama, a lokacin na kan fahimci cewa fuskarsa ta kara haske, sannan kuma maganarsa da mu'amalarsa ta bambanta da yadda suke kafin watan Ramalanan. Haka watan Ramalana yake ga mutum ma'abucin imani da matsayin mai girma. Irin sauyin da watan ya ke haifar wa irin wannan mutum da haske da zuciyarsa take samu ana a fili suke a duk lokacin da mutum ya gan shi, sannan kuma daga maganganunsa mutum zai iya fahimtar irin haske da daukakar da ya samu. Haka bayin Allah suke. Don haka wajibi ne mu yi kokarin amfanuwa da wannan dama.
Wani batu kuma da nake son in yi mana ishara da shi a rayuwarmu wanda kuma nake fatan zai zamanto wata hanya gare ni da ku Ya ku 'yan'uwa maza da mata wajen kyautata kawukanmu shi ne nesantar sabon Allah a cikin rayuwarmu, hakanyana da muhimmancin gaske. Aikata mustahabbai da nafiloli da addu'oi da sauran ayyuka dukkansu rassa ne. Asalin lamarin shi ne mutum ya yi kokarin hana kansa aikata sabo da dukkanin abubuwan da suka saba wa shari'a. Hakan kuwa yana bukatar tsoron Allah. Tsoron Allah da nesantar saba maSa suna daga cikin mafi muhimmancin - ko kuma ma abu na farko - da ya kamata mutum ya misaltu da su. Don kuwa su ne suke hana mutum aikata sabo. Sabon Allah ba ya barin mutum ya kusanci kogin gafarar Ubangiji da ke da fadin gaske ballantana ya amfana da shi. Haka nan sabon Allah yana hana mu jin dadin dake cikin addu'oi. Sannan kuma ba ya barinmu mu yi tunanin hanyoyin da za mu bi wajen gina kanmu. Don haka wajibi ne mu yi iyakacin kokarinmu wajen ganin mun nesanci sabo. Wannan shi ne sharadin farko...
Nesantar Sabo Tana Bude Kofar Amfanuwa Da Rahama Da Gafarar Ubangiji
Wajibi ne mu samar da hanyar da za mu amfana da rahama da gafarar Ubangiji, hakan kuwa ta hanyar nesantar sabo ne. Don haka ne ma a cikin Du'a Kumail kuke ganin Amirul Muminin, amincin Allah su tabbata a gare shi, yake cewa: Ya Allah Ka gafarta min zunuban da suke tsare addu'a". Sabon Allah ya kan zamanto garkuwa daga karbar addu'a. A cikin wadannan darare da asubahi cikin addu'ar Abu Hamza muna karanta cewa: "(Ya Allah! Ka sanya shamaki tsakanina da zunubaina wadanda suke hana ni yi maka biyayya", wato Ya Allah Ka sanya wata garkuwa tsakanina da zunubaina, zunuban da suke hana ni aiwatar da ayyukan da suka hau kaina da hana ni samun damar kusantarKa. Wannan shi ne asalin lamarin.
Mafi girma da muhimmancin lamurra a tsari da hukuma ta Musulunci shi ne cewa hukumar ba ta share fagen sabon Allah tsakanin al'umma, amma a gwamnatocin dagutai kuwa ita da kanta gwamantin ce take bata yanayin ne da sabo da zunubai. Idan ma mutum ba ya son aikata zunubi to a wasu lokuta lamurra sukan yi masa wahala saboda kusan dukkan komai suna kwadaitar da mutum ne zuwa ga sabon Allah. Amma a tsarin Musulunci lamarin ba haka yake ba. A gwamnatin Musulunci ba a bata yanayi da gubar sabo...a tsarin Musulunci ba wai ma ba a ganin sabo a matsayin abin da ke kawo ci gaba ba ne, a'a na ana ganinsa ne a matsayin abin da ke kafar ungulu ga ci gaba da koyarwa ta addini sannan kuma mizani na faduwar mutum.
Don haka asalin lamarin shi ne nesantar sabo da zunubai wanda dole ne mu yi kokari wajen ganin mun aikata hakan a wannan wata na Ramalana. Kuma da yardar Allah za mu samu damar nesantar da zunubai daga gare mu ta hanyar kokari da dubi cikin ayyukanmu. Matukar muka nesantar da zunubai daga rayuwarmu a wannan lokaci ne za mu sami damar tashi da yawo cikin malakutin sammai da shawagi cikin hallarar da aka tsara masa. To amma idan muna dauke da kayan zunubai hakan ba zai taba samuwa ba. Don haka watan Ramalana wata gagarumar dam ace ta nesantar zunubai.
Muhimmancin Azumi Da Yin Hakan Cikin Watan Ramalana
Azumi da muke ganinsa a matsayin daya daga cikin takalifin Ubangiji, har ila yau kuma wata kyauta da ni'ima ce ta Ubangiji, sannan kuma wata gagarumar dama ga dan'Adam saboda samun damar daukan azumi da yayi, duk kuwa da cewa akwai wahalhalu cikin hakan. Babu wani aiki mai girma da daukaka da babu wahala cikinsa. Babu inda mutum zai je matukar ba zai iya jure wa wahala ba. Idan abin a kwatanta wahalar da mutum zai sha ne sakamakon azumi da kuma irin lada da ni'imar da zai samu sakamakon daukan azumi to bambanci na da yawan gaske, don kuwa tamkar ma bai aikata wani abu ba ne.
Azumi ba shi ne kawai mutum ya nesanci ci da sha ba. Wajibi ne wannan kame baki ya ginu bisa asasin niyya. Saboda idan abin a ce mutum ya zauna na tsawon awanni sha biyu zuwa sha biyar bai ci komai ko shan wani abu ba sakamakon wata matsala da yake fuskanta ko kuma rashin lokacin hakan to ai ba shi da wata lada kan hakan. To amma idan har wannan kame baki ya ginu ne bisa niyya - Ka sanya mu daga cikin wadanda suka yi niyya sannan suka aikata - , wato mutum ya kuduri aniya sannan sai ya ci gaba da aiki to hakan shi ne abin da zai sanya mutum samun lada.
Niyya daya ne daga cikin sharuddan azumi. Mece ce niyya? Abin nufi shi ne cewa wannan aiki da mutum zai yi, wannan kame baki da mutum yayi ya kasance saboda Allah ne kuma a tafarkin Allah don biyyayya ga umurnin Allah. Hakan shi ne yake ba wa duk wani aiki kima. Don haka ne ma a cikin addu'ar daren farko na watan Ramalana muke karanta cewa: "Ya Allah Ka sanya mu daga cikin wadanda suke yin niyya sannan su aikata, kada Ka sanya mu daga cikin wadanda suka tabe sai suka yi kasala (Al-Ikbal Bi A'amal al-Hasana, juzu'i na 1, shafi na 1376). Kasala ita ce rashin karfin gwuiwa cikin aikata wani aiki na duniya ne ko na lahira, to hakan tabewa ne.
Azumi yana daga cikin mafiya kyaun ayyuka. Ko da yake a zahiri kamar ba komai ba ne to amma a badini kan lalle wani abu ne mai amfanarwa. Daga lokacin da ka kudura aniya, lokacin da ka shiga cikin sahun masu azumi - wato tun daga lokacin ketowar alfijir - har zuwa karshen rana kana cikin ibada ne sakamakon wannan niyya da ka kulla. Idan ma ka yi barci, to kana cikin ibada ne, haka nan idan ma kana tafiya ne ibada kake yi.
An ruwaito Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa, yana cewa: "Numfashinku a cikinsa (watan Ramalana) ma tasbihi ne sannan barcinku ma a cikinsa ibada ne" (Amali na Sheikh Al-Saduk, shafi na 84). Ya ya barci zai zama ibada? Ya ya numfashi zai zamanto fadin 'subhanallah'? hakan saboda matukar dai kuna cikin niyya ko da kuwa kun zauna ba abin da kuke yi, to kuna cikin ibada ne.
A wata ruwayar kuma yana cewa: "Barcin mai azumi ibada ce, shirunsa kuwa tasbihi ne" (Thawab al-A'amal, shafi na 75) wato idan ma kuka yi shiru tamkar kuna fadin 'subhanallahi' ne'. Sannan kuma ya ci gaba da cewa: "Ayyukansa abin karbuwa ne haka addu'oinsa abin amsawa ne" (Thawab al-A'amal, shafi na 75), wato ayyukanku karbabbu ne haka nan addu'oinku abin amsawa ne. Shurinku ibada ne, haka nan numfashinku ibada ne, barcinku ma ibada ne. Don me? Saboda wannan kame baki da kuka yi, haka nan nesantar abubuwan da jiki da zukatanku suke so da kuka yi kun yi hakan ne cikin wadannan kwanaki talatin, wato cikin watan Ramalana, don Allah.
Dukkan wadannan ibadu da ma wasunsu suna komawa ne ga cewa mutum ya yi watsi da sha'auce-sha'aucen zuciyarsa ne.....
Akwai wata ruwaya da aka ruwaito daga wajen Imam Sadik amincin Allah ya tabbata a gare shi lokacin da yake magana da Muhammad bn Muslim yana cewa: "Ya Muhammad! Idan kana azumi ko wajibi ne jinka da ganinka da harshenka da namanka da jininka da fatarka da gashinka su ma su yi azumin" (Al-Mukna'a, shafi na 310). Wato a wannan hadisi Imam Sadik (a.s) yana gaya wa wannan mabiyinsa ne cewa (idan kana azumi) to kada ka fadi karya, kada ka cutar da muminai, kada ka batar da mutanen da ba su da masaniya sosai, kada ka kulla makirci ga 'yan'uwa musulmi da kasashen musulmi, kada ka yi fatan sharri ga wani, kada ka tuhumci wani, kada ka boye kayayyakin da mutane suke bukata, ka kasance ma'abucin amana. Mutumin da a watan Ramalana ya nesanci abinci da abin sha da sauran sha'auce-sha'aucen zuciya, to wajibi ne harshensa da idanuwansa da kunnuwansa da dukkanin gabobinsa su ma su zamanto suna azumin, ya ji cewa yana hallarar Ubangiji ne don haka ya nesanci aikata zunubi....
A wata ruwayar kuma Amirul Muminin (a.s) yana cewa: "Azumin rai shi ne kamewar dukkanin gabobin riskan abubuwa guda biyar daga aikata sabo, da kuma tsarkake zuciya daga dukkanin abubuwan da suke haifar da sharri". Mu yi mu'amala da Allah da sauran bayin Allah da tsarkakakkiyar zuciya. Akwai ruwayoyi da yawa da suka yi magana kan hakan.
Wannan wata, wata ne na azumi; wata ne na saukar Alkur'ani da lizimtar Alkur'ani; watan ibada da addu'a da munajati ne - saboda addu'a ita ce ruhin ibada - wata ne na neman gafara da tuba da komawa ga Allah Madaukakin Sarki da lizimtar tsoronSa; wata ne na jihadi - saboda a wannan wata mai albarka ne aka yi yakin Badar a shekara ta biyu ta hijira da kuma bude garin Makka da aka yi a shekara ta takwas bayan hijira da fara yakin Hunain a wannan shekarar - wata ne na fada da son zuciya da jihadi da Shaidan da makiya Allah. Wata ne na shiri don samun tsoron Allah da kiyaye shi, wata ne na sada zumunci, gaskiya da kyautata alaka da sauran 'yan'uwa na addini, neman ilimi sanin Ubangiji da tuntuni cikin Alkur'ani mai girma. A takaice dai wata ne na tanadin neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki tsawon shekara. Fatanmu ita ce cewa mun sami damar aiwatar da ayyukan da suka dace da wannan watan cikin kwanakin da suka gabata sannan cikin kwanakin da suka saura kuma za mu kara kaimi wajen tsarkake zuciyarmu da kyautata alakarmu da Ubangiji da kuma mu'amalarmu da sauran mutane da tunanin cikin ayoyin Alkur'ani mai girma da kokari da azama wajen fada da soyace-soyacen zuciya.
Yana da kyau a isar da sakon taya murnar shigowar wannan wata ga 'yan'uwa (da abokan arziki) sannan kuma a yi musu wasicci da himma wajen amfanuwa da ni'imomin da suke cikin watan. Saboda wata ne na bakuncin Ubangiji, a wannan watan muminai da mutanen da suka dace da wannan liyafa ta Ubangiji ne za su zauna a kan taburmar liyafar. Baya ga daya tabarmar liyafar karimcin Ubangijin da dukkanin bil'adama da ma sauran halittun duniya suke amfana da ita. Ita wannan taburma ta musamman ne ga zababbun bayin Allah.
Wani bangare mai muhimmanci da ke da alaka da watan Ramalana yazo cikin wannan aya mai girma ta cikin Suratul Bakara da sauran ayoyin da suka biyo bayanta da a cikin wannan huduba zan yi ishara da ita.
Da farko Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka gabace ku". Mun san cewa salla da zakka ba kawai na al'ummar Annabi (s.a.w.a) ba ne, Annabawan da suka gabaci Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ma suna da salla da zakka (cikin shari'arsu) gwargwadon yadda hukumcinsu ya tanadar. Annabi Isa (a.s) yana gaya wa mabiyansa cewa: "Ya yi min wasicci da salla da zakka matukar ina raye". Akwai wasu ayoyin ma da suke ishara da irin wannan ma'anar. Ayar farko da na karanto tana cewa ne: azumi tamkar salla da zakka suna daga cikin hukumce-hukumcen da ba su takaita da Musulunci kawai ba; face dai al'ummomi da Annabawan da suka gabata ma an farallanta musu azumi.
Azumi Wata Hanya Ce Ta Samun Takawa
A rayuwar ruhi ta dan'Adam a kowani zamani ne kuwa, kamar yadda salla ta zamanto wajiba saboda kasantuwarta wata hanya ta kulla alaka tsakanin mutum da Ubangijinsa, sannan kamar yadda zakka ta zamanto wajiba saboda kasantuwarta hanya ta tsarkake dukiyar mutum, haka azumi ma ya zamanto wajibi kuma wani asasi na cikan dan'Adam da kamalarsa ta ruhi. Idan kuwa ba haka ba to da ba a ci gaba da riko da wannan aiki (azumi) ba kuma da bai ci gaba da dawwama cikin addinan da suka gabata ba.
Koda yake yanayin da ake yin azumin ya bambanta daga wannan al'umma zuwa wancan, to sai dai nesantar cin abinci da abin sha wato rike baki da gabubba daga wasu abubuwa suna daga cikin abubuwan da hatta a addinan da suka gabata ma akwai su. Don haka azumi wani rukuni na asasi ne wajen daukakan ruhi da kamala da tarbiyyar dan'adam a kowani lokaci.
Daga nan sai Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da cewa: "Ko za ku sami takawa", wato azumi wata hanya ce ta samun takawa da tabbatar da ita a rayuwar dan'Adam. Takawa ita ce mutum ya yi taka tsantsan da dubi cikin ayyuka da halayensa ya ga shin sun yi daidai da abin da zai samar masa da yardar Allah ko kuma a'a. Wannan yanayi da hali na taka tsantsan da sanya ido da nesantar ababen da aka hana shi ne ake kira takawa (tsoron Allah).
Kishiyar takawar kuwa ita ce gafala da nuna halin ko in kula cikin halaye da dabi'u. Allah Madaukakin Sarki ba Ya yarda mutum ya dinga aikata duk abin da ya dama ko kuma nuna halin in kula cikin rayuwa ba. Wajibi ne kowani mumini ya zamanto mai taka tsantsan da sanya ido kan ayyuka da dabi'unsa.
Matukar wata al'umma ko wani mutum ya zamanto ma'abucin takawa, to kuwa ya sami alherorin duniya da lahira. Fa'idar takawa ba wai kawai ta takaita ne ga samun yardar Allah da shiga Aljanna a ranar kiyama ba ne; a'a a duniya ma mutum mai tsoron Allah ya kan ga fa'idar hakan. Duk wata al'ummar da take da takawa, al'ummar da ta zabi tafarkin Ubangiji sannan kuma ta ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki, to a duniya ma za ta amfana da ni'imar Ubangiji, za ta sami daukaka ta duniya sannan kuma Allah zai ba ta ilimi da masaniya cikin al'amurranta na duniya. Al'umma ma'abuciya tsoron Allah za ta samar da yanayi mai tsabta da tsarki ta rayuwa tsakanin al'ummominta da kuma hadin kai da aiki kafada da kafada a tsakaninsu.
Takawa ita ce mabudin dukkanin alherorin duniya da lahira. Batattun mutanen da suke fuskantar matsaloli da wahalhalu na zamantakewa kala-kala sun fada cikin wannan bala'i ne sakamakon rashin tsoron Allah da biyayya ga soyace-soyacen zuciyarsu. Al'ummomin da suka ci baya, yanayinsu a fili yake. Al'ummomin da suka ci gaba a duniya, duk kuwa da cewa sun yi nasara a wasu bangarori - sakamakon taka tsantsan da kokarin da suka yi a wasu bangarori na rayuwa - to amma duk da haka suna fuskantar matsaloli kamar yadda masana da marubutansu suka tabbatar da hakan a fili.
Takawa ita ce wasiyyar farko kuma ta karshe ta Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa. Ayoyin Alkur'ani daban-daban sun bayyana cewar wasiccin farko na Annabawan Allah ga mutanensu ita ce wasiyyar takawa. A duk inda tsoron Allah ya ke to akwai shiriyar Ubangiji a wajen; idan kuwa aka rasa takawa, to kuwa cikakkiyar shiriyar Allah ba za ta sami wannan al'umma ba. Azumi kuwa matakin farko ne na takawa.
A cikin Suratul Hadid Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Ya ku wadanda kuka yi imani, ku bi Allah da takawa kuma ku yi imani da ManzonSa, Ya ba ku rabo biyu daga rahamarSa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi", takawa ta kan sa Allah Madaukakin Sarki Ya sanya haske cikin zuciya da rayuwarku da tafarkin da kuke tafiya a kansa don ku sami damar tafiya sakamakon wannan haske sannan kuma ku sami tafarkin rayuwarku. Al'umma ba za ta iya tafiya da sanyin jiki ba. Ba tare da sanin inda za a je ba tafiya ba za ta kasance da sauki ga mutum ba. Don haka wannan haske da aka same shi sakamakon takawa da nesantar sabo shi ne zai iya shiryar da mutum zuwa ga wannan manufa. Don haka ne wasiyyar dukkan Annabawa ta kasance lizimtar takawa.
Ku yi kokarin amfanuwa da damar da ake samu a watan Ramalana. Ku yi kokarin gudanar da wadannan ranaku cikin azumi da dare kuma da zikiri da addu'oi. Watan Ramalana lokaci ne na addu'a. Duk kuwa da cewa ya kamata a koda yaushe mutum ya dauki addu'a a matsayin hanyar kulla alakarsa da Ubangiji, to amma ayar "idan bayina suka tambaye ka dangane da ni (ka ce musu) ina kusa da su ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya kira Ni" dake cikin Suratul Bakara tana da alaka da azumin watan Ramalana. Wannan aya ta " idan bayina suka tambaye ka dangane da ni (ka ce musu) ina kusa da su" ta zo ne a tsakiyar ayoyin azumi da watan Ramalana, da take kiran dukkanin bil'adama dukkanin bayin Allah wajen lizimtar addu'a.
Alakar addu'a, alaka ce ta zuciya da Allah Madaukakin Sarki. Addu'a tana nufin bukata da ambaton Allah. Haka nan bukata tana bukatar kyakkyawar fata. Matukar mutum ba ya da kyakkyawar fata da zato mai kyau ba zai bukaci wani abu a wajen Allah ba. Mutumin da ya yanke kauna ba ya neman wani abu. Don haka addu'a tana nufin kyakkyawar fata da ke da alaka da amsa bukatar da mutum yake da ita. Irin fatar cewa za a amsa wa mutum bukatarsa ita ce take sanya zuciyarsa zama cikin tunanin (cewa za a amsa masa) sannan da kuma zama cikin haske. Addu'a tana sanya al'umma ta zamanto cikin motsi da ayyukan ci gaba. Don haka wannan wata (na Ramalana) wata ne na Alkur'ani, lizimtar Alkur'ani da kuma kara mana masaniyar addinin Musulunci.
Matukar muka yi tuntuni cikin ayoyin Alkur'ani mai girma, irada da azamarmu ta kan karu. Kamar yadda wadannan ayoyi na Alkur'ani ne dai suka tarbiyyantar da dan'Adam ta yadda har ya yi watsi da duniyar kafirci da duhu. Irin wannan masaniya ce al'ummarmu ta samu har ta sami karfin tsayawa kyam wajen fuskantar duniyar jahiliyya. Ina rokon Allah da Ya kara ba wa al'ummarmu damar kusantar Alkur'ani mai girma.
Azumi A Kalaman Ma'asumai (a.s)
Marhalolin Azumi
sun bayyana cewar azumi yana da marhaloli guda uku, kowani guda daga cikinsu yana da amfani ga ma'abutansa. Marhala ta farko ita ce dai wannan marhala ta gaba daya ta azumi, wato nesantar ci da sha da sauran abubuwan da aka haramta. Idan ma har muka takaita ga wannan marhala ta kame baki to ita ma kanta tana da amfani mai yawan gaske. Saboda hakan ma ya kan zamanto jarrabawa gare mu sannan kuma abin koyarwa. Wato darasi ne gare mu sannan kuma koyarwa ta rayuwa. Motsa jiki ne mai matukar muhimmanci sama da irin motsa jikin da aka sani. Akwai wata ruwaya da aka samo ta daga wajen Imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su, da take magana kan wannan marhala. An ruwaito Imam Sadik, amincin Allah ya tabbata a gare shi, yana cewa: "Don masu dukiya su yi daidai da fakirai" (Fadha'il al-Ashhur al-Thalatha, shafi na 102) wato Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta azumi ne don mai dukiya da wanda ba shi da shi su zamanto daya a wadannan sa'oi da ranaku (na watan Ramalana). (A sauran ranaku) mutumin da ba shi da abin hannu ba zai iya cin abin da yake son ci ko shan abin da yake son sha ba a duk lokacin da ya so, amma shi kuwa mai dukiya a tsawon rana duk abin da yake son ci ko sha zai iya samu. Don haka mai dukiya ba ya iya riskar halin da mara shi yake ciki na rashin iya samar wa kansa abubuwan da yake bukata a duk lokacin da ya so. To amma a ranakun azumi kowa ya zama daya, an hana su ci ko shan abin da suke so tsawon wannan lokaci.
Akwai wata ruwayar ma da aka ruwaito ta daga wajen Imam Ridha, amincin Allah ya tabbata a gare shi, da ke ishara da wani batun na daban, inda yake cewa: "don ya san irin wahalar da ke cikin yunwa da kishirwa, sannan kuma ya fahimci rashin ranar lahira" (Ilal al-Shara'i, shafi na 270). A wannan ruwaya an yi ishara ne da rashi da kuma yunwa da kishirwar ranar kiyama. A ranar kiyama daya daga cikin bala'in da mutum zai fuskanta shi ne yunwa da kishirwa. A wannan lokacin mutum zai fuskanci tambayoyi da amsoshin Allah Madaukakin Sarki. Don haka ne ya kamata yunwa da kishirwar azumin watan Ramalana ya zamanto abin da zai tunawa mutum irin wannan yanayi mai tsananin gaske a ranar kiyama.
Har ila yau akwai wata ruwayar kuma daga wajen Imam Ridha, amincin Allah ya tabbata a gare shi, da ke ishara da wani bangare na wannan marhala ta yunwa da kishirwa, wannan ruwaya kuwa ita ce fadinsa cewa: "Yana mai hakuri da abin da ya same shi na daga yunwa da kishirwa" (Ilal al-Shara'i, shafi na). Ana ba wa mutum karfin jurewa yunwa da kishirwa. Mutanen da suke cikin jin dadi, wadanda ba su san wahalar yunwa da kishirwa ba, ba su da karfin hakuri da juriya, a mafi yawan lokuta cikin sauki za su sare, sannan kuma ba za su iya hakurin mafi yawa daga cikin jarrabawa ta rayuwa ba. Amma mutumin da ya san zafi da wahalar yunwa da kishirwa ba shakka ya san wahalar da ke tattare da su sannan kuma yana da karfin jurewa duk wata wahala da ta taso masa. Don haka watan Ramalana ya kan ba wa kowa da kowa irin karfin hakuri da juriya. Bari in kawo muku wata ruwayar ma ta daban ita ma daga wajen Imam Ridha (a.s) da take magana kan hakan da ke cewa: "sannan kuma tarbiya ce gare su wajen sauke nauyin da aka dora musu" (Ilal al-Shara'i, shafi na 270), wato hakurin yunwa da kishirwa da nesantar sauran ababen sha'awa a ranakun watan Ramalana wani nau'i ne na tarbiyyantar da kai wajen sauke nauyin shari'a da aka dora wa mutum. Abin nufi da tarbiyyar shi ne tarbiyya ta shari'a, tarbiyya ta Ubangiji da kuma zabin kan mutum...
Marhala ta biyu ita ce nesantar zunubi da sabon Allah; nesantar da kunnuwa, idanuwa, harsuna da zukata - kai hatta ma bisa wasu ruwayoyin - har da fatar mutum da gashinsa daga zunubi. Nesantar zunubi lamari ne da za a iya kwatanta shi da wani katon dutse da ke tsaye a gaban mutum (wanda kawar da shi yana da wahalar gaske), to sai dai kuma idan mutum ya yi azama tuni dai ba je shi tamkar tudun kasa. Watan Ramalana wata babbar dama ce da mutum ya samu wajen gwada hakan. Akwai wata ruwaya da aka ruwaito ta daga wajen Fatima al-Zahra, amincin Allah ya tabbata a gare ta, dake cewa: "wani amfani azumi zai yi wa mai yinsa idan dai har bai sanya shi kame harshensa da jinsa da ganinsa da sauran gabobinsa (daga aikata sabo) ba" (Al-Nadadir: 22)
Daga cikin irin wadannan sabo har da sabo na harshe, wato cin naman mutane da wulakanta su. Daga cikin irin wadannan zunubai har da zunubi na zuciya wato kiyayya da kaidi ga sauran mutane da ake yi da zuciya. Wasu daga cikin zunuban suna da ma'ana ta istilahi ta shari'a, wasu kuma zunubai ne na dabi'a da suke da marhaloli daban-daban...
Marhala ta uku ta azumi ita ce nesantar duk wani abin da zai kawar da zuciyar mutum daga tuna Allah Madaukakin Sarki. Wannan ita ce marhala ta koli ta azumi kamar yadda yazo cikin ruwaya cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Allah Madaukakin Sarki cewa: "Ya Allah me ake samu daga azumi?" sai Allah Madaukakin Sarki Ya ce masa: "Azumi yana tabbatar da hikima, hikima kuma tana tabbatar da masaniya, masaniya kuma tana tabbatar da yakini. Idan bawa ya samu yakini to ba ya damuwa kan yadda ya wayi gari cikin sauki ne ko cikin wahala" (Bihar al-Anwar: juzu'i na 77 shafi na 27). Wato azumi mabubbugar ruwar hikima ce ga zuciyar (mutum). A lokacin da hikima ta samu gindin zama a zuciya, to za ta samar da wannan masaniya da ke cike da haske. A lokacin da masaniya ta samu o kuwa yakini zai samu wajen zama, wanda hakan shi ne abin da Annabi Ibrahim (a.s) ya bukata daga wajen Allah Madaukakin Sarki sannan kuma a cikin addu'oin wannan watan ma an bukaci hakan. Idan mutum ya samu yakini kuma to dukkanin wahalhalu na rayuwa za su zamanto masa da sauki sannan kuma babu wata matsala ta rayuwa za ta zamanto masa ala kakai.
Ku duba irin muhimmancin da wannan lamari yake da shi. Mutumin da yake son samun wata hanya ta daukaka da kamala tsawon rayuwarsa, sannan kuma ya zamanto maras mika kai ga matsaloli da wahalhalu na rayuwa (to ya lizimci azumi), saboda azumi yana samar da dukkan wadannan abubuwa. Azumi yana rayar da ambato da tunanin Allah a cikin zukata sanann kuma ya haifar da masaniyar Allah cikin zukata don haka suka rike shi hannu bibbiyu...lalle mutanen da suka sami nasarar kai kansu zuwa ga wannan marhala sun ji dadinsu. Mu ma wajibi ne mu yi fatan samun hakan, mu roki Ubangiji mu yi himma da azama wajen ganin mun isa zuwa ga wannan marhalar.
Don mu amfana da wannan dama ta watan Ramalana bari in karanto mana wannan hadisi da yin karin bayani kansa. Hadisi ne ingantacce da aka ruwaito shi daga wajen Ma'aiki, tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da Alayensa, dake cewa: "Azumi garkuwa ce daga wuta". ‘Yan Ahlussunna ma sun ruwaito wannan hadisi da lafuzza da suka bambanta da wadannan, daga cikinsu akwai cewa: "Azumi garkuwar mutum mumini ne ranar kiyama kamar yadda makamin waninku yake kare shi a duniya", wato kamar yadda a duniya kuke kare kanku da makamai da sauran abubuwan kariya haka nan a ranar kiyama ma za ku kare kanku daga kunar wuta ta hanyar azumi.
Azumi Mazharin Kare Kai Ne
Wani abu ne azumi yake da shi da har Manzon Allah (s.a.w.a) ya bayyana shi da cewa "Garkuwa ce daga wuta"? Saboda azumi yana ba da kariya ne ga rai da hana shi bin son zuciya. Sannan kuma shi ne abin da ke sanya zuciya ta yi hakuri da jurewa aikata sabo da kuma yin galaba kan soyace-soyacen zuciya. Don haka ne ruwayar da ta zo karkashin wannan aya ta "ku nemi taimako da hakuri da salla" aka bayyana hakuri da azumi. Don haka azumi mazhari ne na yin kunnen uwan shegu ga soyace-soyacen zuciya...
Lailatul Kadri: Dare Ne Na Aminci Da Saukar Albarkokin Ubangiji
Watan Ramalana lokaci ne na neman gafara da addu'a da komawa ga Allah Madaukakin Sarki. A yanzu dai darare biyun da ake zaton na Lailatul Kadri ne sun riga da sun wuce -wato dararen sha tara da ashirin da daya - to amma akwai daren ashirin da uku a gabanmu, don haka ku yi kokarin amfanuwa da shi. Tun farko daren ashirin da ukun, wato tun daga lokacin da rana ta fadi, amincin Ubangiji ya ke sauka "har zuwa ketowan alfijir" (Suratul Kadr: 5)
Cikin wadannan sa'oi ne aminci da rahamar Ubangiji yake saukowa kan halittunSa. Lalle wannan dare ne mai ban mamaki, wanda yake daidai da watanni dubu "ya fi watanni dubu" (Suratul Kadr: 3)
Wasu irin albarkoki da rahamar Ubangiji ne mutum zai iya samar wa rayuwarsa cikin watanni dubu, to amma wannan dare (guda) ya fi wadannan watanni dubun. Hakan yana da muhimmancin gaske. Don haka wajibi ne ku san muhimmancin wannan dare kuma ku yi kokarin amfanuwa da shi. Ku lizimci addu'oi, tunani cikin ayoyin Allah da halittunSa da kuma makomar al'umma da abubuwan da Allah yake son mutum ya aikata da yin watsi da wannan duniya kararriya....
A watan Ramalana - kamar dukkan ranaku da darare - ku yi kokarin haskaka zukatanku da ambaton Allah gwargwadon iyawarku, don ku shirya wa shiga hallarar daren lailatul kadri mai tsarki "Lailatul kadri ya fi darare dubu. Mala'iku suna saukowa tare da Ruh (Mala'ika Jibril) a cikinsa da umurnin Ubangijinsu daga dukkan al'amurra" (Suratul Kadr: 3 da 4). Dare ne da Mala'iku suke ta shawagi tsakanin kasa da sama suna haskaka zukata da rayuwa da haske da falala da tausayin Ubangiji. Dare ne na aminci "Aminci ne shi har zuwa ketowan alfijir" (Suratul Kadr: 5). Dare ne na amincin zukata da rayuka, dare ne na warkar da cututtuka na halaye, cututtuka na ruhi, cututtuka na zamantakewa da a yau suke damun al'ummomin duniya ciki kuwa har da na musulmi. Amincin ne daga dukkan wadannan abubuwa da ake samu a wannan dare, to amma fa da sharadin mun shirya wa shiga wannan dare.
Addu'oi da ambaton Ubangijinku a cikin tsarkakan zukatanku Ya ku wadannan matasa suna haifar da mu'ujiza. Don haka tun yanzu ku shirya kanku. Hakan bai takaita kawai ga wadannan ranaku ba, a'a ku yi kokarin kyautata alakarku da Ubangiji tsawon rayuwarku.
Watan Ramalana wata ne na tanadi da samun karfi. Watan Ramalana wata ne da ya kamata dukkanin al'umma su yi shirin kai kansu zuwa ga ma'ajiyar gaibi da ruhi ta Ubangiji don diban guzuri gwargwadon iyawarsu. Su shirya kansu don samun ci gaba. Saboda wannan wata ne na Ramalana.
Daren lailatul kadri a wannan wata ake samunsa, Alkur'ani mai girma a fili ya bayyana cewar: "Lailatul kadri ya fi watanni dubu" (Suratul Kadr: 3), samun wani dare guda da yafi darare dubu lamari ne fa mai muhimmancin gaske. Me yasa wani dare guda yake da irin wannan falala da daukaka? Saboda albarkokin Ubangiji a wannan dare suna da yawan gaske, haka nan mala'iku suna yawan saukowa da kai komo a wannan dare, sannan kuma wannan dare aminci ne shi "aminci ne shi har zuwa ketowan alfijir" (Suratul Kadr: 5), amincin Allah yana tare da wannan dare tun daga farkonsa har zuwa karshensa. Ana saukar da rahama da falalar Ubangiji akan bayinSa a wannan dare.
Daren lailatul kadri dare ne na wilaya. Dare ne na saukar Alkur'ani sannan kuma dare ne na saukowar mala'iku zuwa wajen Imam al-Zaman. Don haka dare ne na Alkur'ani kuma dare ne na Ahlulbaiti (a.s). Hakan shi ne ya sanya Suratul Kadr ta zamanto surar wilaya.
Daren lailatul kadri yana da muhimmanci da amfani mai yawan gaske. Dukkanin watan Ramalana, darare da ranakunsa suna da matsayi mai girman gaske, duk da cewa daren lailatul kadri yana da daukaka sama da sauran darare da ranakun watan Ramalanan, su kuma darare da ranakun watan Ramalana sun fi sauran darare da ranakun sauran watannin shekara. Don haka wajibi ne a girmama hakan. Dukkanin mutane suna kan tabarmar liyafar Ubangiji a cikin wadannan ranaku da darare, don haka ku yi kokarin amfanuwa da hakan.
A cikin wannan wata, duk wani aikin alheri da kuka aikata, duk wata maganar gaskiya da kuka fadi, duk wata kalmar da kuka sanar da mai bukatarta, duk wata kalmar da kuka fade ta don Allah kuma a tafarkin Allah, duk wata raka'ar salla da kuka yi, duk wata ayar Alkur'ani da kuka karanta, duk wata sa'a da kuka yi alhali bakinku na rufe da azumi, duk wata nesantar zunubi da kuka yi yana da muhimmanci da girman gaske. Kada ku yi karya, kada ku ci naman wani. Ku nesanci hakan gaba daya.
Duk wani aikin alheri da kuka aikata, kyautatawa, ciyar da marasa abin hannu da taimakonsu, sada zumunci da isar da gaisuwa, taimakon marasa galihu, aikata wani aiki na ci gaban al'ummar musulmi, aiki wajen ci gaban al'umma, dukkan wadannan ayyuka ibada ce.