Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali


Marigayi Sayyid Sadr Ya Kasance Mutum Ne Dan Baiwa Na Hakika
Sayyid Muhammad Bakir

Da farko muna maraba da ku da sauran mata musamman ma ‘ya'yanku maza da mata abin girmamawa. Kuma muna alfahari da marigayi shahid Ayatullahi Sayyid Muhammad Bakir Sadr a matsayin mutum mai zurfin ilimi, mujahidi, mai kaifin basira. Hakika ya kasance abin alfaharinmu dukkanmu, kuma muna alfahari da ku saboda kun jure wahala mai girma da tsanani mai kona zuciya na tsawon shekaru fiye da ashirin kuma kuka yi hakuri kan haka. Lalle ku zuriya ce daga babban gida wanda hakuri da karamci da mutunci suka kasance daga dabi'un wannan zuriya ta ku.
Bayan shahadar marigayi Ayatullahi Sadr kun rayu a cikin mummunar hali a birnin Najaf, sannan mazajen wadannan mata suma suka yi shahada hakika an jarrabi kowane guda daga cikinku ta hanyoyi da dama, amma kuka yi hakuri kan haka. A gaskiya hakurinku yana da kima mai girma a wajenmu. Ku sani na kasance ina muku addu'a daga nesa, kuma na san irin tsanani da matsalolin da kuke fuskanta.
Allah ya albarkaci shahid marigayi Sayyid Muhammad Sadr haka nan makusantanku da ‘ya'ya'yen shahid Sadr Allah Ya yarda da shi. Wadannan sune mata da suka yi hakuri a lokacin mulkin danniya mai daga hankali inda mazajensu suka yi shahada a lokacin suna cikin kuruciyarsu wanda ya zame ‘ya'yansu ne kawai suka saura. Hakika suna da matsayi mai girma a wajen Allah kuma hakurin da kuka yi yana da kima mai girma a wajen Allah madaukaki, Ina rokon Allah ya faranta muku zuciya da ladarsa da kyakkyawar sakamakonsa a duniya da lahira.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khamenei ya ci gaba da cewa:
... na tafi kasar Iraki a shekara ta 1336 hijira shamsiyya (1959 miladiyya) inda na hadu da Sayyid Muhammad Bakir Sadr a can, a lokacin yana matakin samartakansa yana da shekaru kimanin ashirin da biyar a duniya kuma tun a wancan lokacin ya kasance mashahuri a fagen ilimi da daukaka. Ni na kasance ina da shekaru kasa da nashi, a lokacin ina da shekaru kimanin goma sha takwas a duniya.
Hakika godiya ta tabbata ga Allah domin sauran zuriyarku ma sun kasance ma'abuta albarka madaukakiya, misalin marigayi Sayyid Ridha da Sayyid Musa.
Mun samu labarin shahadar Ayatullahi Sadr ne a farkon farkon samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran inda hakan ya kasance hasara mai girma gare mu domin shahid Sadr ya kasance kashin bayan tsarin Musulunci da al'ummar musulmi na hakika. Kuma kafin samun nasarar juyin juya halin Musulunci mun kasance muna da masaniya dangane da littattafansa da ayyukan da yake gudanarwa masu tsananin muhimmanci da kima, sannan bayan nasarar juyin juya halin Musulunci ya fitar da bayanai masu muhimmanci na goyon baya. Hakika akwai buri mai girma da aka sanya a kan Sayyid Sadr. La'anar Allah ta tabbata a kan Saddam, kuma godiya ta tabbata ga Allah da ya kawo karshensa.
Marigayi Sayyid Sadr ya kasance dan baiwa na hakika. Muna da mutane madaukaka masu yawa da suka shahara a fagen ilimin Musulunci, fikihu, usulu da sauran fannin ilimi, sai dai ‘yan baiwa a cikinsu kadan ne. Shi kuwa Sayyid Sadr ya kasance daga cikin kadan da suka samu matsayin baiwa na hakika inda tunaninsa ya kasance yana tsinkayar abubuwa nesa da na sauran mutane kuma godiya ta tabbata ga Allah domin ya samu nasarar yaye dalibai na kwarai.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Snack's 1967