pacman, rainbows, and roller s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Damuwa Da Lamurran Al'ummar Musulmi

Ali khamenei3

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:
ﻣﻦ ﺃﺻﺒﺢ ﻣﻦ ﺃﻣﺘﻲ ﻭﻫﻤّﺘﻪ
ﻏﻴﺮﺍﻟﻠّﻪ ﻓﻠﻴﺲ ﻣﻦ ﺍﻟﻠّﻪ ﻭﻣﻦ ﻟﻢ
ﻳﻬﺘﻢّ ﺑﺄﻣﻮﺭ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﻠﻴﺲ ﻣﻨﻬﻢ
ﻭﻣﻦ ﺃﻗﺮّ ﺑﺎﻟﺬﻝ ﻃﺎﺋﻌﺎً ﻓﻠﻴﺲ ﻣﻨّﺎ
ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ
"Wanda ya wayi gari daga
cikin al'ummata amma
dukkan kokarinsa bai
zamanto wajen neman
yardar Allah ba, to ba ya
tare da Allah. Kuma duk
wanda bai damu da
al'amarin muminai ba, to ba
ya daga cikinsu. Kuma duk
wanda ya amince da
kaskanci bisa radin kansa,
to ba ya tare damu
Ahlulbaiti.
(Tuhaful-Ukul shafi na 47).
Duk wanda ya wayi gari
muradi da niyyarsa ba su
zama kokari wajen neman
yardar Allah ba, to ba ya
daga cikin rundunar Allah
kuma masu aiki dominSa.
Kuma duk wanda ya wayi
gari bai damu da al'amarin
musulmai ba, wato
amfaninsu da cutuwarsu ba
su da bambanci a wajensa,
to baya daga cikin
musulmai na hakika.
Damuwa da al'amurran
musulmai yana da rassa
masu yawa. Reshen da yafi
daukaka shi ne ba da
muhimmanci ga al'amurran
da suka shafi daukakar
al'ummar musulmi da
karfinta da kokarin ganin
addinin Musulunci ne ke
gudanar da rayuwarta. Har
ila yau yana daga cikin
rassan damuwa da
al'amurran musulmi
taimakawa mabukata,
raunana da marasa galihun
cikinsu.
A bangare guda kuma duk
wanda ya zama raunanne,
makaskanci bisa radin
kansa baya tare da
Ahlulbaiti kebantattun
Iyalan gidan Manzon Allah
(s.a.w.a). Yana da kyau a
fahimci cewa mika kai da
yarda da kaskanci ba wai ya
takaita a gaban manyan
‘yan siyasar duniya
ma'abuta girman kai ba ne
kawai, ya kumshi amincewa
da kaskanci a gaban
hamshakan masu dukiya da
‘yan jari hujja ma. Bai dace
mutum ya kaskantar da
kansa ya zame maras kima
saboda kwadayi da buri ba.
Yazo cikin ruwaya cewa
mumini yana iya lamuntar
komai amma ban da
kaskanci.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din