MAHANGAR JAGORAN JUYIN JUYA HALIN MUSULUNCI NA IRAN DANGANE DA ADDINI

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Addini a matakin farko wani lamari ne da ya san ciki da wajen duniya. Yana da masaniya kan duniya, masaniya dangane da dan'adam, dangane da tafarki, hanya da manufa. Dukkan wadannan masaniya sune asasin addini ya ginu kansu. Addini yana ganin dan'adam a matsayin ginshiki kuma matattaran duniya. Dan'adam a matsayinsa na ginshiki zai iya kokari na tunani sannan kuma ya bude yankunan da suke rufe.
Duniya fage ne na asasi wajen aiki da nauyi da sako na addini. Addini ya zo ne don shiryar da kokarin dan'adam a wannan fage mai girma da bangarori daban-daban (na rayuwa) da ba su jiha mai yau. Duniya da addini a irin wannan ma'ana ta duniya lamari ne da ba za a iya raba su da juna ba. Saboda addini ba zai iya samar da wani waje da zai gudanar da sakonsa ba in ba duniya ba. Ita ma duniya ba za ta iya samun ababe da suke karfafa ruhi da kyawawan dabi'u da soyayya ba tare da taimako na addini ba. Duniya - wacce ita ce fagen rayuwar dan'adam - ba tare da addini ba za ta koma ga rayuwa irin ta dabbobi da rashin doka da oda. Alhali kuwa wajibi ne mutum ya samu shu'urin jin yana da tsaro da kwanciyar hankali a duniya da kuma riko da tafarkin daukaka da kamala ta ruhi.
Raba addini da duniya da wannan ma'ana tana nufin raba rayuwa, siyasa da tattalin arziki da koyarwa ta Ubangiji; hakan kuwa yana nufin kawar da adalci da ababen da suke da alaka da koyarwa ta Ubangiji (cikin rayuwa). Sannan kuma duniya da ma'anar dama ga rayuwar mutum, da ma'anar ni'imomi daban-daban a fagen (rayuwa ta) duniya, da ma'anar ababe masu kyau da dadi da kuma ababen bakin ciki da sosa rai, hakan wata hanya ce ta kamalar bil'adama. A mahangar addini dukkan wadannan abubuwa dama ce ga dan'adam wajen sama wa kansa hanyar isa ga daukaka da kamala da samar da kwarewar da Allah Madaukakin Sarki Ya tanadar masa. To idan haka ne kuwa to duniya da irin wannan ma'ana ba za a iya raba ta da addini ba....koda yake duniya tana da wata ma'ana da fahimta ta daban. A wasu ruwayoyi na addini an bayyana duniya da ma'anar son kai da zama fursunan son zuciya...a bisa ruwayoyinmu irin wannan duniya abar korewa ce sannan kuma ba za a iya hada ta da addini ba.
A mahangarmu al'umma su ne asasin komai. A koyarwa ta Musulunci da mahangarsa, koyarwa ta Ubangiji da tunanin dan'adam ba su yi hannun riga da junansu ba, suna da alaka da junansu. Da farko dai matukar babu ma'abuta addini a wata kasa to kuwa ba za a iya tabbatar da gwamnati ta addini ba a kasar da kuma al'umma ma'abuciya addini. Wato al'umma ba za su bukaci irin wannan gwamnati ba, ballanta a samar da ita.
Manufar mulki irin na addinin Allah ita ce kula da halin da wadanda aka zalunta suke ciki (don biya musu bukatunsu) da kuma aiki da farilla da hukumce-hukumcen Ubangiji saboda kuwa sa'adar dan'adam tana cikin aiki da hukumce-hukumcen addini ne. Don kuwa adalci da 'yancin bil'adama suna cikin aiki da hukumce-hukumcen addini ne. A ina ake iya samun 'yanci? Saboda biyan bukatun dukkanin bil'adama na daga cikin abubuwan da addini ya ginu a kansu.
Babu wani bambanci tsakanin mutumin yau da mutumin shekaru dubu da suka gabata a bangaren bukatunsu na asasi. Bukatu na asasi na bil'adama su ne: yana bukatar tsaro, yana bukatar 'yanci, yana bukatar masaniya, yana bukatar kyakkyawar rayuwa ba tare da wahalhalu ba, yana adawa da nuna bambanci da zalunci. Bukatun da suke tasowa abubuwa ne da za a iya lamuninsu karkashin inuwar wadanann abubuwa. Amma bukatu na asali ana iya biyansu ne ta hanyar addinin Allah banda wanin hakan.
Manzon Allah (s.a.w.a) shi ne ya zo da addini, shi ne ya zo da wannan mahangar. Duk da cewa ya kasance yana kiran mutane zuwa ga abubuwan da suke karfafa ruhi sai dai duk da haka kuma ya kasance mai mika wa mutane ababen da suka shafi duniya. A wasu lokuta shi da kansa yake ba wa mutane ilimi na rayuwa da kuma wanda ya shafi gudanar da lamurran rayuwa. A wasu wuraren kuma da suke bukatar fita waje da nemo kwararrun da suke da irin wadannan ilmummuka ya kan bukace su da su tafi wajen ma'abuta irin wadannan ilmummuka su koyo su sannan su gane wa idanuwansu abubuwan da suke gudana.
Karnonin tsakiya (lokacin jahiliyyar turai) karnoni ne da ke cike da duhu da jahilci ga mutanen Turai, a bangare guda kuma lokaci ne mai haske da ci gaba ga mu musulmi. Turawa suna kokarin boye wannan hakika, marubutan turawan ba sa kawo irin wadannan bayanai, to amma (abin bakin ciki) mu ma mun yarda da hakan.
Karni na sha tara wanda karni ne na koli wajen binciken ilimi na duniya a kasashen yammaci, karni ne da aka san shi da sunan karnin raba addini da fagen rayuwa ta dan'adam. Wannan tunani ya yi tasiri hatta a cikin kasarmu ta yadda asasin jami'oinmu suka kasance bisa asasin da ba shi da alaka da addini. An nesanta malamai daga jami'oi kamar yadda su kansu jami'oin suka nesanta kansu daga malamai da makarantun addini.
Mutanen da ma suke goyon bayan addini suna ganin 'bai kamata addini ya tsoma baki cikin al'amurran siyasa ba', sai dai abin da ba su sani ba shi ne cewa wannan sabuwar mahanga farfaganda da makircin ma'abuta girman kai da 'yan mulkin mallaka ne akan hukumar Musulunci da kokarin sake rayar da addinin Musulunci. Koda yake akidar raba addini da siyasa ba lamari ne na yau ba tun shekaru aru aru take nan. Wadanda suka samar da ita kuwa su ne 'yan mulkin kama-karya wato ma'abuta karfin da suke son rike madafan iko da mulki da gudanar da mulki yadda suke so ba tare da wani ya isa ya tsoma musu baki ko kuma ya hana su ba. A fili yake ba za su so hukumce-hukumcen Musulunci da masu kira zuwa ga hukumcin Musuluncin su tsoma musu baki cikin harkokin gudanarwarsu ba. Don haka ake ganin sarakuna da azzaluman shugabanni masu mulkin kama karya su ne mutanen farko da suka gabatar da wannan batacciyar akida ta 'raba addini da siyasa'.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved