Rayuwar Imam Ali Al-Hadi (a.s) Da Gwagwarmayarsa

Imam Hadi (a.s) shi ne yayi nasara a gwagwarmayar da yayi da halifofin zamaninsa (wato na daular Abbasiyawa). Hakika yayi nasara a zahiri da badini a gwagwarmayar da yayi, wannan shi ne abin da ya dace mu tunasar a dukkanin maganganunmu da jawabanmu.
Halifofin daular Abasiyawa shida ne suka yi mulki a zamanin imamancinsa inda dukkaninsu suka halaka. Na karshensu shi ne Mu'utaz wanda kuma shi ne ya kashe Imam al-Hadi (a.s) kamar yadda shi kansa Imam din ya bayyana, sannan shi ma Mu'utaz din ya halaka bayan dan wani lokaci. Mafi yawan wadannan halifofi na daular Abbasiyawa sun yi mutuwa ce ta kaskanci. Dayansu dansa ne ya kasha shi, daya kuma dan dan uwansa ya halaka shi, haka dai Bani Abbas suka tarwatse, sabanin ‘yan Shi'a. Saboda hakika Shi'anci ya samu bunkasa da ci gaba gami da daukaka a zamanin Imam Ali Al-Hadi da Imam Hasan Al-Askari amincin Allah ya tabbata a gare su.
Imam Ali Al-Hadi (a.s) ya rayu ne na tsawon shekaru arba'in da biyu a duniya, inda ya shafe shekaru ashirin a garin Samarra. Yana da wata gona (a garin Samarran) wacce ta hanyarta ne yake rayuwa. Asalin garin Samarra yayi kama da sansanin soji. Halifa Mu'utasim ne ya gina garin domin ya zauna a ciki da wasu masu masa hidima Turkawa, wadanda ya tattaro su daga yankunan Turkistan, Samarkand, Maghulistan da Gabashin Asiya. Don haka wajibi ne a kebance su da hana su haduwa da turkawanmu da suke nan.... Da kuma Turkawan Azirbijan da sauransu. Wadannan Turkawa dai ba su jima da musulunta ba saboda haka ba su san matsayin Imaman Ahlulbaiti (a.s) ba da kuma kimar sauran muminai, haka nan da kuma koyarwar addinin Musulunci. Don haka suke cutar da mutane tare da gwabza yaki da larabawa da musulmi da suke Bagadaza.
A zamanin Imam Hadi (a.s) ‘yan Shi'a da dama sun taru a garin Samarra, inda Imam ya samu daman gudanar da al'amuransu tare da isar da sakon shiriya ta hanyarsu zuwa ga sassa daban daban na duniyar musulmi ta hanyoyi daban-daban da suka hada da wasiku da sauransu. Lalle wadannan ‘yan Shi'a sun sami damar bunkasa wannan tafarki na Shi'anci a garuruwan Kum, Khurasan, Rayya, Madina, Yemen da sauran yankuna masu nisa na duniya, saboda haka yawan masu shiga cikin wannan mazhaba yayi ta karuwa kullum rana. Imam Hadi (a.s) ya gudanar da dukkan wadannan ayyuka ne karkashin walkiyar takwabin wadannan halifofi guda shida da suke adawa da shi.
Dubi cikin tarihin rasuwar Imam Hadi (a.s) zai nuna mana cewa adadi mai girma ne na ‘yan Shi'a suka taru a garin Samarra ba tare da ‘yan leken asirin mahukuntan daular Abasiyawa sun gano hakan ba, saboda idan da a ce sun fahimci hakan da sun dauki matakin ganin bayansu dukka. Amma bayan da ‘yan Shi'an suka yi karfi suka bunkasa a garin Samarra sai ya zame babu ta yadda mahukuntan daular Abasiyawan za su gama da su cikin sauki.
Gwagwarmayar da wadannan Jagororin shiriyan masu daukaka (a.s) suka yi ta rana guda ta kan yi babban tasiri na kimanin shekaru masu yawa. Sannan kuma tasirin rayuwarsu mai albarka a cikin al'umma ta rana guda tana daidai da tasirin ayyukan da jama'a za su yi na tsawon shekaru masu yawa. Ta haka ne wadannan masu girma suka kare addini. Amma da a ce addinin (Musulunci) shi ne addinin da Mutawakkil da Mu'utaz da Mu'utasim da Ma'amun suke jagorantarsa kuma malaman fada irinsu Yahaya Dan Aksam da makamantansa fasikai, wadanda suka kauce hanya, mabarnata suka tarjama shi ne, to da babu bukatar wannan addini, kai ya ma dace ne a kawar da shi daga tushensa, ya kawo karshe tuntuni.
Hakika jihadi da kokarin da Jagororin shiriya na iyalan gidan manzon Allah (s.a.w.a) suka yi ba ya kare Shi'anci ba ne kawai, ya kare addinin Musulunci ne da Alkur'ani da koyarwar addini dukkansa. Wannan itace alamar bayin Allah da Waliyansa tsarkaka masu tsarki. Lalle da a ce addinin Musulunci ba shi da masu da shi irin wadannan mutane (Imaman Ahlulbaiti) da yanzu addinin ya zame labari bayan bayyanarsa yau tsawon shekaru dubu da dari biyu zuwa da dari uku kuma da bai zame yana da sauran karfin farfado da koyarwar Musulunci a cikin zukata ba. Haka nan kuma da ya gushe da kadan kadan. Har ila yau da bayan Manzon Allah addinin Musulunci ya kasance ba shi da mutane da za su tabbatar da wadannan ilimummuka masu girma a taskar tarihin dan adam da na Musulunci, da dole ne addinin Musuluncin ya zame shafaffe babu abin da yayi saura daga gareshi. Idan ma har za a samu wani abu daga gare shi, to da bai kasance daga cikin hakikanin koyarwarsa ba, da zai zame matsayi daya da addinin Kiristanci da Yahudanci da suka zame kusan babu abin da yayi saura daga hakikanin koyarwarsu.
Kasantuwar Alkur'ani da hadisan Manzon Allah (s.a.w.a) da dukkan wadannan hukumce hukumce da ilimummuka na Musulunci cikin aminci bayan shudewar shekaru dubu (da doriya), hakika hakan wani lamari ne da ba haka kawai aka same shi ba, lalle hakan ya samo asali ne sakamakon kokari himma tukuru. Lalle hakan ya samu ne sakamakon gagarumar himma da wahalhalu da bugu da zagi da dauri (a gidajen yari) da kisa da wadannan madaukakan bayi (Imaman Ahlulbaitin Manzon Allah) suka fuskanta.
Akwai wani hadisi da yayi magana dangane da lokacin yarintar Imam Ali Al-Hadi (a.s) ban sani ba shin kun ji ko ba ku ji ba? A lokacin da Mu'tasim ya daga Imam Jawad (mahaifin Imam Hadi) daga Madina zuwa Bagadaza a shekara ta 218 (hijiriyya) - shekaru biyu kafin shahadarsa - Imam Ali Al-Hadi ya saura a Madina tare da sauran danginsa a lokacin kuwa yana da shekaru shida ne a duniya. Bayan isar Imam Jawad (a.s) Bagadaza sai Mu'utasim ya tambayi labarin iyalan Imam. Lokacin da ya samu labarin cewa babban dansa dan shekara shida yana Madin, sai yace wannan wani babban hatsari ne gare mu, wajibi ne mu yi tunanin mafita. Sai (Mu'utasim) ya umurci daya daga cikin makusantansa da ya tafi Madina ya samu wani mutum daga cikin makiya Ahlul-baiti (a.s) ya damka masa kula da Imam Hadi domin ya koyar da shi tare da tarbiyantar da shi yadda zai koma makiyin Ahlulbaiti kuma mai kyaunar halifofin Abbasiyawa.
Bayan mutumin nan ya bar Bagadaza ya isa Madina ya samu daya daga cikin malaman Madina mai suna Al-Junaidi da ya kasance mai tsananin kiyayya da gaba da Ahlulbaiti (a.s) ya ba shi wannan aiki. A wancan lokacin Madina tana dauke da irin wadannan malaman. Sai ya ce masa aikinka shi ne ka kasance malami mai tarbiyantarwa ga wannan yaro kuma ka da ka bar shi ya gana da wani mutum na daban domin muna son ya kama hanyarmu ne. A lokacin Imam al-Hadi yana da shekaru shida ne kamar yadda na ce, sannan kuma wannan umurni ne na mahukunta don haka babu wani da yake da ikon hanawa. Bayan wani lokaci daya daga cikin mutanen da suke da alaka ta kusanci da mahukuntan daular Abbasiyawa ya gamu da Al-Junaidi inda ya tambaye shi labarin yaron da aka damka masa shi kan ya koyar da shi. Sai Al-Junaidi yace ka ce yaro? Shin wannan yaro ne? Na kan bijiro masa wata mas'ala daya ta adabi sai ya bude mini kofofi da dama kan wannan mas'alar sai na koma ni ke koyon adabin daga gare shi! Wai shin a ina wadannan mutane (Ahlulbaiti) suka yi karatu ne?
Wani lokaci na kan ce masa: Karanta wata sura daga Alkur'ani idan za ka shiga daki -yana so ne ya musguna masa ta wannan hanyar - sai ya tambaye ni wata sura kake son in karanta maka? Sai in ce masa ya karanto wat doguwar sura misalin Suratu Ali-Imrana. Nan take sai ya karanta surar ya kuma yi mini sharhin abin da ta kunsa! Hakika wadannan malamai ne, sun haddace Alkur'ani kuma sun san tawilinsa da tafsirinsa ... ai wannan ba yaro ba ne.
Alaka ta ci gaba da gudana tsakanin wannan yaro - wanda yake yaro ne a zahiri amma waliyi ne daga cikin waliyan Allah, Allah yana cewa: "Kuma muka ba shi hukunci tun yana karami"- da malaminsa (Al-Junaidi) na tsawon lokaci har ta kai ga daga karshe dai ya zama dan Shi'a mai ikhlasi ga ahlul-baiti (a.s).