Hadin Kai Tsakanin Shi'a da Sunna

A yau daya daga cikin manyan manufofin manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai da kuma Amurka a duniyar musulmi ita ce haifar da sabani da rarrabuwa. Mafi girman hanyar cimma wannan manufa kuwa ita ce haifar da rikici da sabani tsakanin Shi'a da Sunna. A yau kowa yana gani da jin irin kalaman da suke fitowa daga bakunan ‘yan mulkin mallakan duniya dangane da kasar Iraki. Wani irin rura wutar (fitina) da shuka irin rarrabuwa ne ba sa yi. Shekara da shekaru kenan hannayen ‘yan mulkin mallakan da masu neman mulki ruwa a jallo na duniya suke aikata irin wannan aiki. Don haka wajibi ne a yi taka tsantsan a dukkanin lokuta kuma a dukkanin bangarori. Don kuwa yaki tsakanin Shi'a da Sunna shi ne abin da Amurka za ta fi yin farin ciki da shi.
Wajibi ne kasahen musulmi su farka, bai kamata su dauki abokin gaba da makircinsa da sauki ba (wato bai kamata su yi rikon sakainar kashi wa hakan ba). Wajibi ne su mike tsaye su yi taka tsantsan, sannan kuma su ci gaba da kiyaye wannan taka tsantsan din. Yau rana ce ta hadin gwuiwa da fahimtar juna da aiki kafada da kafada tsakanin al'ummomi da kasashen musulmi. Don haka a daidai wannan lokaci kuma a daidai wannan waje nake son in yi kira da kuma jan kunnen al'ummarmu, al'ummar Iraki da al'ummar Pakistan da sauran al'ummomin kasashen musulmi da cewa su yi watsi da duk wani sabani da rarrabuwa ta mazhaba, Shi'a da Sunna. Ni a yau ina ganin wasu hannaye da suke ta kulla makirci da sunan Shi'a da Sunna don haifar da rikici da yaki tsakanin musulmi. Ko shakka babu akwai hannayen yahudawan sahyoniya mashaya jini da na sauran ma'abuta girman kan duniya cikin irin kashe-kashe da bama-baman da ake tayarwa a masallatai da husainiyoyi da wajajen sallar jam'i da juma'a, don kuwa wannan ba aikin musulmi ba ne. Labarin da muke da shi suna nuni da cewa dukkanin irin hare-haren da kashe-kashen da ake yi a Iraki, a nan Iran, a Afghanistan da Pakistan da ma sauran kasashe akwai muggan hannayen yahudawan sahyoniya da sauran makiya musulmi ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar amfani da wasu mutane.
Ko da yake wadannan kalamai da muke fadi ba wai muna cewa ne dan Shi'a ya zama dan Sunna ba ko kuma dan Sunna ya zama dan Shi'a ba. Haka nan kuma manufarmu ba ita ce a shigar da wata mazhaba cikin wata ta daban ba, koda wasa. Abin da muke cewa shi ne kowani guda daga cikin ‘yan Shi'a da ‘yan Sunna kowa yayi iyakacin kokarinsa wajen karfafa akidarsa ta hanyar ilimi, aiki na ilimi lamari ne mai kyaun gaske kuma babu wata matsala cikin hakan. Wasu sukan kore batun mazhaba wai don kawai a samu hadin kai tsakanin musulmi. Ai kore mazhaba ko da wasa ba zai magance matsalar ba, a'a tabbatar da mazhaba ne ma zai magance matsalar. Babu matsala dukkanin wadannan mazhabobi da muke da su kowane guda daga cikinsu yana iya yin aikinsa gwargwadon koyarwarsa, to sai dai wajibi ne ya kyautata alakarsa da sauran ‘yan'uwansa. Su rubuta littafa na ilimi amma a wajajen ilimi ba a wajajen da ba su da alaka da ilimi ba. Don haka matukar wani mutum zai iya tabbatar da abin da akidarsa ta dogara a kansa, mu ba za mu hana shi ba. To amma matukar mutum yana son ya haifar da rikici da sabani ta hanyar maganganu da ayyukansa da sauran hanyoyi, to mu dai muna ganin hakan a matsayin hidima ce ga makiya. Don haka wajibi ne ‘yan Sunna su yi taka tsantsan haka nan su ma ‘yan Shi'a.
Duk wanda yake bin wata mazhaba ko wata akida yana da hakkin ya kare ta da kuma girmama ta. To sai dai wannan girmamawa bai kamata ta zamanto kuma wata hanya ta cin mutumcin akidu da ababen girmamawar wasu mutane ba wadanda suke da sabani kansu ba. Dukkanmu mun yi imani da Musulunci guda, da Dakin Ka'aba guda, Annabi guda, salla guda, aikin hajji guda da jihadi guda da kuma shari'a guda. Abubuwan da muka hadu kansu sun fi abubuwan da muka rabu a kansu yawa. Abin da makiya suke so shi ne a samu sabani tsakanin Shi'a da Sunna ba wai kawai a nan Iran, a'a a duk duniyar musulmi.
Bari in kara da wannan batu ma na cewa kada ku mai da Amirul Muminin Ali (a.s) ya zamanto dalilin rabuwa tsakanin Shi'a da Sunna da sauran kungiyoyin Musulunci. Don kuwa Amirul Mumini matattara ce ta hadin kai, ba ta rarrabuwa ba. ‘Yan'uwanmu maza da mata da suke ko ina a duk fadin kasar nan su san cewa Amirul Muminin (a.s) matattara ce ta hadin kai. Dukkanin duniyar musulmi suna mika wuya ga Amirul Muminin, babu Shi'a babu Sunna. Wasu ‘yan tsiraru ne kawai masu sunan Nawasib (masu kiyayya ga Ahlulbaiti) su ne kawai suke adawa da Amirul Muminin. Amma sauran musulmi kan - shin ‘yan Shi'a ne ko ‘yan Sunna - suna girmama Amirul Muminin. Ku duba ku gani mana Imaman mazhabobin Ahlussunna suna da baitukan wakoki na yabon Amirul Muminin. Ba wai kawai Amirul Muminin ba hattta sauran Imamai ko kuma a ce mafi yawansu suna girmama su. Dangane da mu ‘yan Shi'a matsayi da mukamin wadannan Imamai a fili yake.
Abin bakin cikin shi ne cewa akan samu wasu mutane a duniyar musulmi da don neman kusanci da Amurka da sauran cibiyoyin girman kan duniya a shirye suke su yi duk wani aikin sabo da aka sa su, wajen haifar da rikici tsakanin Shi'a da Sunna (babu ruwansu). A yau din nan ina ganin wasu hannaye a kasashen da suke makwabtaka da mu wadanda suke gudanar da wasu ayyuka da gangan kuma ma tsararru don dai su haifar da rikici tsakanin Shi'a da Sunna. Su rarraba al'ummomi a tsakaninsu, su sanya kungiyoyi da jam'iyyu na siyasa rikici da tada jijiyoyin wuya a tsakaninsu, don su sami damar kama kifaye daga gurbataccen ruwa da kuma kiyaye haramtattun manufofinsu a kasashen musulmi. Don haka wajibi ne mu yi taka tsantsan.
Mutanen da suke kwadaitar da ‘yan Sunna wajen yakan ‘yan Shi'a ko kuma ‘yan Shi'a wajen yakan ‘yan Sunna, ba wai suna son Shi'an ba ne ba kuma suna son Sunnan ba ne, ko da wasa. Suna adawa ne da Musulunci. Ma'anar ayar da take cewa su
"masu rahama ne a tsakaninsu" (Suratul Fath 48:29) shi ne cewa ‘yan'uwa musulmi a tsakaninsu masu rahama da tausayawa ne ga junansu. Kokari da makircin makiya a kansu ne gaba daya. A bangare guda suna kwadaitar da mai wuce gona da iri da kuma nasibi mai kiyayya da Ahlulbaiti, a wani bangaren kuma su yi kokarin sanya ‘yan Sunna su ji cewa ‘yan Shi'a manyan abokan gabansu ne - abin bakin cikin shi ne cewa wasu daga cikin wadanda aka barsu a baya cikin lamurran addini su kan yarda da hakan - a bangare guda kuma suna kwadaitar da ‘yan Shi'a wajen cin mutumcin ababe masu tsarki na ‘yan AhlusSunna. Babban makircin makiya shi ne su hada wadannan mazhabobi fada da junansu. Makiyan sukan shigo ne ta hanyar da mai yiyuwa kun gafala kanta ba ku damu da ita ba. Don haka ku yi taka tsantsan sannan ku yi kokarin fahimtar makiyi ta ko wace irin hanya ko kuma da ko wanin tufafi ya zo muku da shi.
"Lalle za ka gane su ta yanayin maganganunsu" (Suratu Muhammad 47:30) wato za ku iya gane su hatta ta maganganunsu.
Daya daga cikin abubuwan alfaharin da al'ummarmu take da shi shi ne tana nesantar abubuwan da akwai sabani na mazhaba da kabilanci cikinsu kuma akwai yiyuwar su haifar da rikici da sabani na mazhaba ko kabilanci. Hakan yana bata wa makiya rai. Saboda kuwa yaki tsakanin Sunna da Shi'a lamari ne mai muhimmancin gaske ga makiya. Rarrabuwa da sabani tsakanin al'ummar musulmi zai haifar da rauni da rage irin karfin da al'ummar musulmi take da shi, sannan kuma kamar yadda Alkur'ani mai girma ya fadi ne
"sai karfinku ya tafi" (Suratul Anfal 8:46)
Daya daga cikin abubuwan da za su iya zama mana matattara ta hadin kai shi ne samuwar Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wajibi ne dukkan musulmi da masanan cikinsu su ba da himma wajen bayyanar da matsayin wannan babban bawan Allah da sanya kaunarsa cikin zukata don dukkanin al'umma su fahimci matsayinsa.
Wajibi ne dukkanin kungiyoyi da mazhabobin musulmi - ‘yan Shi'a ne ko ‘yan Sunna ko kuma sauran mabiya sauran mazhabobi su dauki batun hadin kai tsakanin musulmi da dukkan karfinsu. Ma'anar hadin kai tsakanin musulmi a fili take. Hadin kai tsakanin musulmi wani lamari ne da ke karfafa rayuwa. Ba wasa da take ba ne kawai, a'a wajibi ne dukkanin musulmi su tabbatar da hadin kai a tsakaninsu, su kama hanya guda. Koda yake hadin kai wani lamari ne mai wahalar gaske. Don kuwa hadin kan yana tafiya ne tare da samuwar bambancin mazhabobi da hanyoyin rayuwa da hukumce-hukumce na fikihu. Abin da ake nufi da hadin kai shi ne a samu haduwar baki da zuciya tsakanin al'ummar musulmi a duk lokacin da wani gagarumin aiki mai amfani ga duniyar musulmi ya taso, kada su tada jijiyoyin wuya a tsakaninsu.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved