Ring ring
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Mahangar Jagora Dangane Da Al’adu


Ali Khamenei5

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Gabatarwa:

Al'ada tana nufin dabi'u da halaye da suke juya rayuwata da rayuwarka. Al'ada tana nufin abubuwan da muka amince da su da kuma akidu da kuma abubuwan da rayuwarmu ta daidaiku da ta jama'ance take fuskanta.
Saboda haka mu muna ganin al'adu a matsayin tushen rayuwar mutum ne. Al'ada tana nufin ababen da suka zamanto wani sashi na rayuwar wata al'umma, wato irin tunaninta, irin imaninta, koyarwarta, dukkan wadannan su ne suke zama tushen al'adun wata kasa. Wadannan abubuwa su ne suke mayar da wata al'umma imma dai ta zamanto jaruma mai kishi da ‘yanci ko kuma wofantacciyar kuma baiwa.
Al'adu su ne asasi kuma tubalin mutumcin kowace al'umma. Al'adun wata al'umma ce suke sanya ta zamanto ma'abuciyar ci gaba, madaukakiya, kwararriya, ma'abuciyar ilimi da fasaha da kere-kere kuma ma'abuciyar mutumci na kasa da kasa. Matukar al'adun wata kasa suka fuskanci matsala sannan kuma ta rasa asasin al'adunta, to hatta irin ci gaban da wasu kasashen za su taimaka mata ba za su iya samar mata irin matsayin da ya dace da ita ba cikin al'umma da kuma iya kare manufofinta ba.
Al'adun al'umma na gaba daya suna da bangarori biyu: bangaren farko shi ne abubuwa da batutuwan da suke a fili kowa yake iya ganinsu wadanda kuma suke da tasiri cikin makomar kowace al'umma; sai dai sukan yi tasiri ne bayan wani lokaci. Wato suna da tasiri cikin rayuwa da makomar wata al'umma. A matsayin misali yanayin tufafi da yadda ake sanya su sannan kuma da wani abu suke koyi. Wadannan suna daga cikin fitattun misalan al'adun al'umma da suke a fili. Ko kuma yadda gine-gine suke a cikin al'ummar, wani irin gida ne suke rayuwa, hakan wani bangare ne na al'adun wata al'umma.
Bangare na biyu na al'adun al'umma na gaba daya, tamkar bangaren farkon ne, yana da tasiri cikin makomar wata al'umma, to sai dai tasirinsa na gaggawa ne kuma ana jinsa a jika sosai. Wato su kansu wadannan lamurran da suke da alaka da wannan bangare na al'adu na gaba daya ba abubuwa ne da ake jinsu sosai ba, to amma tasirinsu cikin al'umma da ayyana makomarta yana da karfin gaske. Mafi girman misalin hakan shi ne batun kyawawan halaye, wato halaye na daidaiku da na zamantakewar al'umma.
Wani misalin al'adu na gaba daya na al'umma kuma shi ne a samu daidaikun mutanen wata al'umma su zamanto mutane ne masu fatan alheri sannan ba masu neman abubuwan amfanin kansu su kadai ba ne; face dai mutane ne wadanda a shirye suke su shigo cikin fage saboda amfanin al'ummarsu da kasarsu. Wato sukan fifita manufa da amfani na gaba dayan al'umma kan amfani da manufa ta daidaiku.
Saboda haka, tasiri da rawar da al'ada take takawa rawa ce irin ta rai cikin jikin al'umma. Juya al'ummomi ta hanyar tilasta musu al'adun kasashen waje ba bakon abu ba ne, dadadden lamari ne; to sai dai cikin ‘yan karnonin baya-bayan nan sakamakon irin ci gaban ilimin da kasashen yammaci suka samu da kuma yadda suke tsara lamurransu yadda suka dace sun sami nasarar tsara hakan da ciyar da shi gaba. Sun san yadda ya kamata su aikata hakan sannan wani bangare ya kamata su fi ba shi muhimmanci.
Dukkanin rayayyun al'ummomin duniya sun yi amanna da cewa duk wata al'ummar da ta yi sake ta bari al'adun kasashen waje suka yi mata kawanya to kuwa wannan al'umma ta gama. Al'ummar da ta yi nasara ita ce al'ummar da al'adunta suka yi nasara. Galaba ta al'adu ita ce take haifar da galaba ta tattalin arziki da siyasa da tsaro da aikin soji da sauran abubuwa.
Samun iko kan al'adun (wata kasa) ya fi hatsari kan samun iko na tattalin arziki da na siyasa. Me ya sa haka? Saboda a duk lokacin da wata al'umma ta samu iko na al'adu kan wata al'ummar, to kuwa za ta rasa mutumci na ‘yan kasanci da take shi. Matukar aka raba wata al'umma da tarihinta, da mafarinta, da al'adunta da zatinta da ci gaban ilimi da ababen alfahari na addini da siyasa da al'adunta - aka kwace mata bakin magana da take da shi da irin ilimi da tarihin al'adun da take da shi - to wannan al'umma za ta zamanto al'umma ce wacce sai yadda aka yi da ita. Wannan al'umma ba za ta iya samun damar tsayawa da kafafunta ba, sai dai idan an samu wasu tsayayyun mutane daga cikinta sun tashi tsaye da kokari ba dare da rana.
Yakin lalata al'adu shi ne a samu wasu mutane - ta bangaren siyasa ne ko tattalin arziki - saboda wata manufa ta siyasa da mamaya, su kaddamar da yaki kan tushen al'adun wata al'umma (da nufin lalata su). Wadannan mutane sukan shigo da wasu sabbin abubuwa (sabbin al'adu) cikin wannan al'umma ko kuma wannan kasa, ko dai ta hanyar tilasci ko kuma da nufin musanya su da al'adu da akidun kasa. Hakan shi ne yakin lalata al'adu. Manufar musanyen al'adu ita ce amincewa da al'adun kasa da cike gibin da suke da shi. To amma a yakin lalata al'adu manufa ita ce kawar da tushen al'adun kasa da tumbuke su. Kamar yadda a musanyen al'adu al'umma ko kasa tana daukan kyawawan al'adu wata al'ummarce wadanda suka dace da nata wadanda kuma take bukata, misali hakan kuwa shi ne ilimi (wanda wata al'umma takan samo shi daga wata don ta cika nata al'adun).
Haka nan musayen al'adu ana yinsa ne bisa zabinmu amma yakin lalata al'adu zabi ne na makiya (wato yana hannun makiya ne). Haka nan muna musayen al'adu ne don mu sami kamala, wato mu cika al'adunmu. To amma yakin lalata al'adu kan ana yinsa ne don kawar da al'adunmu. Musayen al'adu yana daga cikin lamurra masu kyau; amma yakin lalata al'adu yana daga cikin munanan abubuwa. Haka nan kuma musayen al'adu ana yinsa ne cikin karfi da kwarewar wata al'umma; alhali yakin lalata al'adu yana da alaka da raunin wata al'umma ne.
Al'adun kasashen yammaci hangin jimina ne akwai na ci akwai na zubarwa (wato akwai masu kyau akwai marasa kyau). Babu wanda ya isa ya ce dukkanin al'adun kasashen yammaci marasa kyau ne; a'a. Al'adun yammaci tamkar na kasashen gabashi ne, akwai masu kyau akwai marasa kyau. Saboda haka wata al'umma ma'abuciyar hankali sai ta zabi masu kyaun ta kara wa al'adunta, sannan kuma ta yi watsi da wadanda ba su da kyaun.
Al'adun Musulunci, al'adu ne masu girma da kima ga wata al'umma ta dan'adam, tana da mafi girma da daukakan ababe masu kyau, wadanda a hakikanin gaskiya za su iya daukaka wata al'umma daukaka ta hakika da sanya mata farin ciki da ci gaba. Al'ummar musulmi gungu ne na al'ummu da kabilu da mabiya mazhabobi daban-daban. Mafi dadewar al'adu suna nan ne a yankin da musulmi suke rayuwa a cikinsa. Don haka irin wannan bambance-bambance da kuma kasantuwa a wani waje wanda ya fi muhimmanci a duk fadin duniyan nan shi kansa yana iya zama wani abin karfafawa ga wannan al'umma mai girma da kuma zama wata hanya samun gagarumar ci gaba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din