Watan Ramalana Mai Alfarma

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Hakika shigowar watan Ramalana mai albarka babbar ranar idi ce ga musulmi, don haka abu ne mai kyau idan muminai za su taya ‘yan'uwansu murna da kuma musu nasihar su yi kokarin amfanuwa da alherorin da suke cikin wannan wata gwargwadon iyawarsu. Saboda wata ne na bakuncin Ubangiji. A wannan watan muminai da wadanda suka cancanci amsa wannan kira na bakunci ne kawai za su sami damar zama a tabarmar liyafar bakuncin Ubangiji Ma'abucin karimci. Hakan kuwa ba ya ga tabarmar karimcin Ubangijin na gaba daya wacce dukkanin bil'adama ko kuma ma dukkanin halittun Ubangiji za su amfana daga gare ta. Wannan wata kebantacciyar tabarma ce ta bakuncin Ubangijin ga kebantattun mutane.
Muhimmin batu a babin watan Ramalana shi ne cewa mutum - wanda yake cikin tarkon abubuwa daban-daban da suke sanya shi gafala daga Ubangiji da kuma tura shi zuwa abubuwan da suke jan mutum zuwa ga lalacewa - yana samun wata dama ce da zai iya kwadaitar da ruhinsa - wanda yake son samun daukaka da ci gaba - zuwa ga tafarkin daukaka da kuma kusanci da Allah Madaukakin Sarki da kyawawan dabi'u. Watan Ramalana yanayi ne na sabunta rai da gina mutum, sannan kuma yanayi ne na kusantar Ubangiji.
Albarkokin watan Ramalana sukan fara ne daga kan daidaiku da dukkanin musulmin da suke son halartar wannan bakunci na Ubangiji a wannan wata mai alfarma, su kan fara ne daga zukata. Abubuwan da suke fara tasirantuwa da albarkokin da ke cikin wannan wata mai alfarma su ne zukata da rayukan muminai da masu azumi da masu shiga wannan babban fage mai tsarki na watan Ramalana. A bangare guda azumin da ake yi a wannan wata, a wani bangaren kuma karatun Alkur'ani mai girma da ake yi a wannan wata sannan a wani bangaren kuma lizimtar addu'oi da ake yi a wannan wata, dukkan wadannan abubuwa sukan sanya mutum cikin fagen tsarkake kai da zuciya. Don haka dukkaninmu muna bukatar wannan tsarkakewa.
Watan Ramalana na kowace shekara wani bangare ne na Aljanna da Allah Madaukakin Sarki Yake shigar da mu cikinsa daga wutar jahannaman wannan duniya da kuma ba mu damar shiga aljanna ta hanyar zama kan shimfidar liyafar Ubangiji a wannan wata. Wasu su kan shiga wannan Aljanna ne na tsawon kwanaki talatin (na watan). Wasu kuma saboda wadannan ranaku talatin su kan shiga Aljanna na tsawon dukkan shekara, wasu kuma na dukkan rayuwarsa, wasu kuma sukan wuce su ne cikin gafala wanda hakan babban abin bakin ciki ne. Mutumin da ya samu karfin fada da soyace-soyacen zuciyarsa saboda albarkacin watan Ramalana, to alal hakika ya samu babbar rabo wanda wajibi ne ya kiyaye shi. Haka nan mutumin da ya saba da aikata munanan dabi'u da bin soyace-soyacen zuciyarsa - gwargwadon iyawarsa - to yana iya yin galaba kan hakan cikin watan Ramalana, don haka wajibi ne ya kiyaye hakan. Dukkanin bala'oin da dan'adam ya fada cikinsu sun samo asali ne daga bin son zuciya. Dukkanin zaluncin da ke gudana, dukkanin cutar da ake yi da rashin adalci, dukkanin yakukuwan zalunci, dukkanin lalatattun hukumomi, dukkanin mika kai da amincewa da zalunci tsakanin al'ummomi, dukkansu sun samo asali ne daga biye wa son zuciya da mika kai ga soyace-soyacen zuciya. Idan har mutum ya samu karfin da zai iya yin galaba a kan soyace-soyacen zuciyarsa, to kuwa mutum ya samu shiriya. To watan Ramala ya kawo muku wannan yanayi.
Saboda haka, asalin lamarin shi ne nesantar aikata sabo wanda wajibi ne mu yi iyakacin kokarinmu cikin wannan watan ta hanyar kokari da tattaunawa da zuciyarmu, mu ga cikin ikon Allah mun nesanci zunubi. Matukar muka nesantar da zunubai daga gare mu, to a wannan lokaci ne hanyar tashi sama da shawagi cikin farfajiyar samar (Ubangiji) za ta budu mana, mu yi wannan tafiya ta karfafa ruhi da shawagin da aka tsara wa mutum. Amma hakan ba abu ne mai yiyuwa ba matukar muna da nauyin zunubai a kanmu. Saboda haka, watan Ramalana wata gagarumar dama ce na nesantar zunubi.
Shi kansa azumi, da muke ganinsa a matsayin wani nauyi da takalifi na Ubangiji, a hakikanin gaskiya wani daukaka da kuma ni'ima ce ta Ubangiji (gare mu), kuma wata gagarumar dama ce mai kimar gaske ga duk wanda ya samu damar daukan azumi, ko da yake akwai wahalhalu cikin hakan. Babu wani aiki mai girma da amfani da babu wahala cikinsa. Babu inda mutum zai je matukar ba zai iya jure wahala ba. Idan abin a kwatanta wahalar da mutum zai sha ne sakamakon azumi da kuma irin lada da ni'imar da zai samu sakamakon daukan azumi to bambanci na da yawan gaske, don kuwa tamkar ma bai aikata wani abu ba ne. Azumi yana da marhaloli guda uku (kamar yadda malamai suka bayyana), kowane guda daga cikin wadannan marhaloli uku na da amfani ga ma'abutansa. Marhala ta farko ita ce marhalar azumi na gaba daya, wato nesantar ci da sha da sauran abubuwan da aka haramta. Idan ma har muka takaita ga wannan marhala ta kame baki to ita ma kanta tana da amfani mai yawan gaske. Saboda hakan ma ya kan zamanto jarrabawa gare mu sannan kuma abin koyarwa. Wato darasi ne gare mu sannan kuma koyarwa ta rayuwa. Motsa jiki ne mai matukar muhimmanci sama da irin motsa jikin da aka sani. Akwai wata ruwaya da aka samo ta daga wajen Imam Sadik, amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda yake cewa: "Don masu dukiya su yi daidai da fakirai", wato Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta azumi ne don mai dukiya da talaka su zamanto daya a wadannan sa'oi da ranaku (na watan Ramalana). (A sauran ranaku) mutumin da ba shi da abin hannu ba zai iya cin abin da yake son ci ko shan abin da yake son sha ba a duk lokacin da ya so, amma shi kuwa mai dukiya a tsawon rana duk abin da yake son ci ko sha zai iya samu. Don haka mai dukiya ba ya iya riskar halin da mara shi yake ciki na rashin iya samar wa kansa abubuwan da yake bukata a duk lokacin da ya so. To amma a ranakun azumi kowa ya zama daya, an hana su ci ko shan abin da suke so tsawon wannan lokaci.
Mutumin da yake cikin wahalar yunwa da kishirwa, ya riga da ya san irin wahalhalun da watakila za a iya fuskanta a wannan tafarki (azumi), don haka yana da karfin juriya. Watan Ramalana ya kan sanya wa mutum karfin hakuri da juriya a gaban wahalhalu da matsalolin da suka taso. Yana ba wa mutum kyautar hakuri wajen sauke nauyi na Ubangiji dake kansa. Wato dukkanin wadannan fa'idoji suna nan a wannan marhala. Har ila yau baya ga yunwa da kishirwa da kuma nesantar abubuwan da a yanayin da ba na azumi ba halal ne mutum ya aikata su, har ila yau kuma azumi na wannan marhala ya kan sanya wa mutum haske da tausasawa. Hakan babban ni'ima ce.
Marhala ta biyu ta azumi ita ce nesantar zunubi da sabon Allah; wato kiyaye kunnuwa, idanuwa, harsuna da zukata - kai hatta ma bisa wasu ruwayoyin - har da fatar mutum da gashinsa daga zunubi.
Kamar yadda mutum ya nesanci abinci da abin sha da sauran ababen da zuciya take so, haka nan zai nesanci sabo ma. Wannan wata marhala ce da ta ketare wancan (ta farkon). Wannan wata dama ce ta watan Ramalana, wata dama ce da mutum zai yi kokarin amfanuwa da ita da tarbiyantar da kansa wajen nesantar aikata sabo. Saboda haka marhala ta biyu ta azumi ita ce mutum ya nesanci aikata zunubai, wato ya yi kokarin nesantar da kansa, musamman ku matasa, don haka ku yi kokarin amfanuwa da wannan dama. Ku dai matasa ne, matashi kuwa yana da karfi da iko sannan kuma ga tsarkakakkiyar zuciya da take cike da haske. Ku yi kokarin amfanuwa da wannan dama tsawon watan Ramalanan. Ku yi kokarin jarraba nesantar zunubai - wanda ita ce marhala ta biyu ta azumi - da tarbiyantar da kanku da hakan.
Marhala ta uku ta azumi ita ce nesantar duk wani abin da zai kawar da zuciyar mutum daga tuna Allah Madaukakin Sarki. Wannan ita ce marhala ta koli ta azumi. A lokacin da azumi ya sake rayar da tuna Allah cikin zuciya, sannan kuma ya samar wa zuciya masaniyar Ubangiji, to kuwa zuciya za ta haskaka. Saboda haka duk wani abin da zai gafalar da mutum daga ambaton Allah da tuna Shi, to abu ne mai cutarwa ga azumi a wannan marhala. Lalle mutanen da suka sami damar kai kansu zuwa ga wannan marhala sun rabauta.
Watan Ramalana wata ne na addu'a da tanadin tsoron Allah. Wata ne da wajibi ne mu karfafa karfin da muke da shi na ruhi da ababen da suke kusata mutum da Ubangiji sakamakon albarkacin ibadu da ambaton Allah Madaukakin Sarki dake cikinsa, don mu sami damar tafiya kan tafarkin da muke kai cikin sauki da kuma sauri.
Watan Ramalana wata ne na tanadi da samun karfi. Watan Ramalana wata ne da ya kamata dukkanin al'umma su yi shirin kai kansu zuwa ga ma'ajiyar gaibi da ruhi ta Ubangiji don diban guzuri gwargwadon iyawarsu. Su shirya kansu don samun ci gaba. Saboda wannan wata ne na Ramalana. Za ku iya tseratar da kanku daga lalacewa da fasadi da makamantar hakan ta hanyar salloli da sauran takalifin da aka dora wa mutum sannan kuma da azumi da addu'oin da ke cikin watan sannan kuma ku kara da karatun Alkur'ani mai girma - kamar yadda aka ce watan Ramalana, daminar Alkur'ani -, yanayi ne abin a amfana da shi.
A watan Ramalana - a dukkanin ranaku da darare - ku yi kokarin haskaka zukatanku da ambaton Allah gwargwadon iyawarku, don ku shirya wa shiga hallarar daren lailatul kadri mai tsarki wanda "Lailatul kadri ya fi darare dubu. Mala'iku suna saukowa tare da Ruh (Mala'ika Jibril) a cikinsa da umurnin Ubangijinsu daga dukkan al'amurra" (Suratul Kadr: 3 da 4). Dare ne da Mala'iku suke ta shawagi tsakanin kasa da sama suna haskaka zukata da rayuwa da haske da falala da tausayin Ubangiji. Dare ne na aminci "Aminci ne shi har zuwa ketowan alfijir" (Suratul Kadr: 5). Dare ne na amincin zukata da rayuka, dare ne na warkar da cututtuka na halaye, cututtuka na ruhi, cututtuka na zamantakewa da a yau suke damun al'ummomin duniya ciki kuwa har da na musulmi. Amincin ne daga dukkan wadannan abubuwa da ake samu a wannan dare, to amma fa da sharadin mun shirya wa shiga wannan dare.
A kowace shekara, Allah Madaukakin Sarki Ya kan ware wata dama ta musamman (ga bayinsa), wannan dama kuwa shi ne watan Ramalana mai alfarma. A tsawon watan Ramalana, zukata sukan tausasa sannan ruhi kuma ya kan haskaka da dauke idanuwa, sannan kuma ya kan shirya mutum wajen tafiya cikin gonar rahamar Ubangiji ta musamman., Kowani mutum gwargwadon irin shiri da himmar da yake da shi ne zai amfana da wannan bakunci mai girma na Ubangiji. Lokacin da wannan wata ya zo karshe, ranar farko ta sabuwar shekara ita ce ranar idin karamar salla. Wato ranar da mutum zai iya samun damar tafiya a kan madaidaicin tafarkin Ubangiji ta hanyar amfani da irin guzurin da ya samu a watan Ramalana, sannan kuma ya kauce wa hanyoyin da suka kauce. Saboda haka ranar idin karamar salla rana ce ta karban goron sallar rahamar Ubangiji bayan watan Ramalana.
Akwai wani batun kuma dangane da ranar idin karamar salla shi ne kuwa kokari da yin shiri tsawon shekara don fuskantar watan Ramalana mai zuwa. Matukar mutum yana son ya samu damar shiga liyafar bakunci na Ubangiji a kowane watan Ramalana, sannan kuma matukar yana so ya debi rabonsa cikin daren Lailatul Kadri da wadannan darare masu albarka, to wajibi ne ya kula sosai. Wajibi ne ya shirya kansa tsawon watanni sha dayan nan da suke zuwa kafin watan Ramalana. Mutum ya kuduri aniyar cewa ayyukansa za su kasance masu kyau ta yadda a shekara mai zuwa watan Ramalanan zai iya karbansa sannan kuma bakuncin Ubangiji zai zamanto mai kyau a gare shi. Wannan shi ne mafi girman albarka da ni'imar da mutum zai iya samu sannan kuma ya zama masa wata hanya ta nasara a dukkanin lamurran da suka shafi duniya da lahirarsa, kuma suka shafe shi kansa da na kurkusa da shi da kuma dukkanin al'umman musulmi baki daya.
Matukar muka shiga watan Ramalana cikin shirin da ake bukata, to kuwa za mu sami nasarar amfanuwa sosai da liyafar bakuncin Ubangiji, sannan kuma za mu sami nasarar kara haurawa martaba ta sama. A irin wannan yanayi ne kuwa za ku iya ganin abubuwan da za su sanya mana farin ciki cikin rayuwarmu da zukatanmu da kuma cikin rayuwarmu ta al'ummace.