Disneyland 1972 Love the old s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Amirul Muminin (a.s) Babban Abin Koyi Ga 'Yan'adam

Ali Khamenei5

Amirul Muminin (a.s) Wannan Mutum Ma'abocin Haske da Tsarkakakken Matsayi
Wasu daga cikin siffofin da Amirul Muminin (a.s) ya kebanta da su su ne siffofi na kusanci da Ubangiji da wannan mai girma yake da su, wadanda hatta fahimtarsu ma ya yi mana wahala. Irin wannan matsayi na ilimi, wannan matsayi na haske da tsarki da yake da su; irin wadannan hakika da gaskiya da suke cikin samuwarsa da kuma zuciyarsa mai haske sannan kuma suke fitowa daga bakinsa mai albarka; irin wannan kusanci da Allah da wannan ambaton Allah da suka mamaye ayyuka da maganganunsa, dukkan wadannan abubuwa ne da suka yi kama da fidirarsa mai haske da fahimtar hakikaninsu ke da wuya a wurinmu; Sai dai mun yi imani da su kuma muna alfahari da su, saboda kuwa mun ji su ne daga bakin mai gaskiya abin gaskatawa. Sai dai kuma akwai wasu siffofin Amirul Muminin (a.s) wadanda suke bayyanar da shi a matsayin wani abin koyi ga dukkanin mutane tsawon tarihi. Wadannan siffofi ne abin koyi.
Abin koyi wani lamari ne kuma wani ma'auni ne da mutum zai kwatanta aikin da yake son yi gwargwadon yadda wannan abu yake. Wannan abin koyi bai takaita da wasu kebantattun mutane kawai ba; bai kuma kebanta da musulmi ma kawai ba. Dalilin da ya sa kuke ganin fuskar Amirul Muminin (a.s) ta kasance mai jan hankali tsawon tarihi, ba don komai ba ne sai don saboda irin wadannan siffofi ne. A saboda haka ne hatta mutumin da bai yi imani da Musulunci ba ko kuma wanda bai yarda da imamancin wannan mai girma ba, to amma a cikin jikinsa yana jin girma da daukakansa, sannan kuma ko yana so ko ba ya so yana yabonsa. Saboda haka, wadannan siffofi abin koyi ne ga kowa, mu ma da a yau muke da jamhuriyar Musulunci kuma muke da'awar gudanar da wata hukuma mai koyi da halayen Imam Ali (a.s), to wannan abin koyi ne da ya fi zama abin karbuwa fiye da komai wanda kuma ba za a taba kau da kai daga gare shi ba. Ba abu ne kawai da za a fadi da harshen baki ba cewa 'Amirul Muminin Ali' da bayyanar da so da kauna kawai ba; amma a aikace a dinga saba wa ayyukansa da abubuwan da ya fada mana ba. Ni da irina wadanda ma'aikatan (jami'an) gwamnati ne muna da nauyin gaske a wuyanmu; saboda mu wajibi ne mu yi aiki, sannan kuma mu bi hanyar da ya bi. Mai yiyuwa ne wasu su ce: ina ku ina Amirul Muminin? Ina ku ke, ina kuma irin karfi da iko da imani da hakuri da karfin ruhinsa? Na'am wadannan kalaman gaskiya ne. Babu wani guda daga cikinmu da za a iya hada shi da shi (Amirul Muminin). Ba ma za a iya cewa shi yafi ko kuma shi yana sama ne mu muna kasa ba, ko da wasa, lalle wannan kwatance ma kuskure ne. Shi yana can koluluwar sama ne, mu muna can kasa ne muna yi wa kanmu dawafi. Bambancin yana da girman gaske, to amma ana iya zabar hanyar da za'a bi, wato wajibi ne mu kama hanyar da ya kama da kuma manufar da ya sa a gaba, mu kusato da kanmu..

Daidaito Cikin Zatin Amirul Muminin (a.s)
Ta kowace fuska kuka kalli zatin Amirul Muminin (a.s), za ku ga abubuwan mamaki da su ke boye a cikinsu. Wannan kuwa ba karin gishiri ba ne. Hakan yana nuni da irin gajiyawa ta mutumin da a cikin shekaru aru-aru ya yi nazarin rayuwar Amirul Muminin (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sannan ya kuma riski cewa ta hanyar amfani da wannan tunanin da kuma hankalin da ake da shi ba za'a iya riskar hakikanin Ali (a.s) - wannan madaukakin mutum - ta hanyoyin fahimta da aka sansu ba, ta kowane bangare akwai abin ban mamaki. Ko shakka babu Amirul Muminin (a.s) wani karamin kwafi ne na Manzon Allah (s.a.w.a) sannan kuma almajirin wannan mai girma; to amma a wurinmu shi ma'abocin girma ne - tare da cewa shi yana daukar kansa karami kuma kaskantacce a gaban Manzon Allah kuma almajiri ne a wurin wannan ma'abocin girma - idan har muna so mu kalle shi da mahanga ta mutane, to a wajenmu wani mutum ne wanda ya ketare mutane.....
Wani abin da nake son fadi dangane da rayuwar Amirul Muminin (a.s) da kuma wadannan siffofin da ya kebanta da su wadanda na baiwa sunan 'daidaito cikin zatin Amirul Muminin (a.s)'. Akwai daidaito mai ban mamaki cikin zatin wannan mutum mai girma. Wato siffofi wadanda a zahiri masu karo da juna ne da ba za su hadu a karkashin inuwa guda ba cikin rayuwar Amirul Muminin (a.s), wadanda an tsara su tare da junansu cikin yanayi mai kyau, wanda shi kansa lamari ne mai ban sha'awa da kyau, amma mutum ba zai taba ganin wadannan siffofi sun hadu a wajen wani mutum na daban ba. Akwai irin wadannan siffofi masu karo da juna tare da Amirul Muminin (a.s) da yawan gaske. Ba guda daya ko biyu ba ne, suna da yawan gaske. To yanzu bari in gabatar da irin wadannan siffofi masu karo da juna wadanda suka hadu a cikin zatin Amirul Muminin (a.s):
A matsayin misali, rahama da saukin zuciya a gefen dagewa da tsayawa kyam, abubuwa ne da ba sa haduwa da junansu; amma Amirul Muminin (a.s) yana da matsayi na koli na tausayi da rahama da taushin zuciya wanda a hakikanin gaskiya lamari ne da da wuya a same shi a wajen wani mutum na daban...haka Amirul Muminin (a.s) ya kasance a bangaren rahama da tausayawarsa.
(Ku dubi) lokacin da ya tafi gidan macen nan da mijinta ya rasu wacce take da kananan yara a gabanta, da yadda ya kunna wuta ya gasa musu burodi da shirya musu abinci, sannan kuma ya ci gaba da sanya abincin cikin bakunansu, duk dai da nufin ya dadada musu da sanya su farin ciki. Haka kuma ya ci gaba da wasa da su, yana sunkuyawa domin su hau kan kafadarsa yana yawo da su cikin wannan 'yar bukka tasu, don dai ya faranta wa wadannan marayu ransu. To wannan shi ne rahama da tausayin Amirul Muminin (a.s). Daya daga cikin manyan (sahabban) lokacin yana cewa: na sha ganin yadda Amirul Muminin (a.s) ya ke lakato zuma da hannunsa mai albarka yana sanya wa cikin bakunan marayu da marasa shi ta yadda 'har na yi kwadayin ina ma da a ce ni maraya ne' (Bihar al-Anwar, juzu'i na 41, shafi na 29), wato ya dinga samun wannan rahama da tausaya ta Amirul Muminin (a.s). Wannan shi ne rahama da tausayawa ta Amirul Muminin (a.s).
A bangare guda kuma shi kansa wannan Amirul Muminin (a.s) din a yayin yakin Nahrawan; lokacin da wadansu karkatattun mutane masu tsattsauran ra'ayi suka so raunana asasin hukumarsa ta hanyar fakewa da dalilai marasa tushe, da suka hadu ya yi musu nasiha amma dai ba ta yi wani amfani ba, ya kafa musu hujja hakan ma dai bai yi amfani ba, ya tura musu wakili (mai shiga tsakani) shi ma dai bai yi amfani ba; ya taimaka musu da dukiya tare da yi musu alkawari amma duk hakan bai yi amfani ba. Lokacin da suka yi gaba da gaba a nan ma ya yi musu nasiha amma ba ta yi amfani ba, don haka abin da ya saura shi ne daukan mataki a kansu. Wannan shi ne Ali. Saboda ya fahimci cewa masu adawa da shi din ba mutanen kirki ba ne, tamkar kunama suke, to a nan fa dagewa kan matsaya da rashin sassauci sai ya zamanto shi ne abin yi.
A hakikanin gaskiya ba a bayyana hawarijawa kamar yadda su ke. Abin bakin ciki na kan ga cikin maganganu da wake da jawabi da fina-finai da sauran abubuwa ana bayyana harijawa a matsayin mutane masu girmama ababe masu tsarki. Hakan kuskure ne. A ina suke girmama ababe masu tsarkin? A lokacin Amirul Muminin akwai mutane masu yawan gaske da suke aiki don amfanin kansu kawai. Idan har kuna son sanin hawarijawa, to bari in nuna muku su hatta a wannan zamani namu. Kungiyar munafukai, na san ba ku manta da su ba....
Lalle ya kamata ku san hawarijawa da kyau: mutane ne wanda a zahiri suke nuna su masu riko da addini ne, masu riko ne da ayoyin Alkur'ani, mahaddata Alkur'ani da haddace Nahjul Balagah...suna nuna a zahiri sun yi imani da wasu akidoji na addini; to amma suna adawa da saba wa asasin addini, sannan kuma su masu tsaurin ra'ayi ne kan hakan. Suna nuna su bayin Allah ne, alhali su mabiya shaidan ne. Kun dai ga yadda a wasu lokuta munafukai suke irin wannan da'awar; amma daga baya (don cimma manufarsu) ta fada da juyin juya halin Musulunci da (marigayi) Imam da tsarin jamhuriyar Musulunci sai suka hada baki da kuma zama yaran Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da Saddam da ma duk wani mutum (wanda za su sami biyan bukatansu ta wajensa). To harajiwa ma haka suka kasance. To a wancan lokacin haka Amirul Muminin (a.s) ya tsaya kyam wajen yakarsu. Wannan shi ne dai wannan Alin "Masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu"(Suratul Fath:29).
Ku duba ku gani; yadda wadannan siffofi guda biyu wadanda suke tare da Amirul Muminin (a.s) suka zamanto abubuwa masu kyau da ban sha'awa. Mutumin da saboda irin wannan tausayi da taushin zuciya ba zai iya daurewa ganin wani yaro maraya cikin yanayi na damuwa da kunci ba. Yana mai cewa matukar ban sanya wannan yaro dariya (farin ciki) ba to kuwa ba zan tafi daga wannan waje ba. A bangare guda kuma ya tsaya kyam wajen fuskantar wadannan karkatattun mutane - wadanda suke tamkar kunama da take iya cizon kowane irin mutum wanda bai ci ba bai sha ba - yana tsayin daka wajen fuskantarsu.
...wani misalin kuma shi ne tsantseni da kuma irin nau'in hukumarsa. Hakan lamari ne mai ban mamaki. Me ake nufi da tsantseni? Shi ne mutum ya nesanci duk wani abu da ya ke tattare da shubuha wanda kuma ake ganin alamun sabawa wa addini a cikinsa. A daya bangaren kuma ya ya hukuma za ta kasance? Shin za a iya samun wani mutum da zai iya yin wannan taka tsantsan cikin hukuma? To mu dai muna cikin ayyuka, muna ganin yadda hakan yake da muhimmancin gaske a duk lokacin da wani ya samu nasarar samun hakan. A cikin gwamnati, ya kan fuskanci mas'aloli da yi musu kallo na bai daya. A lokacin da yake aiwatar da doka, akwai mu'amaloli da yawa da ake yi; amma mai yiyuwa ne wajen aiwatar da wannan dokar a zalunci wani mutum. Mai yiyuwa ne wani ma'aikaci ya aikata ba daidai ba a wani sashe na wannan kasa da kuma wani bangare na duniya. Ta yaya mutum zai iya kiyaye taka tsantsan na Ubangiji yayin fuskantar wadannan abubuwa? Saboda haka ne a bisa zahiri gwamnati da taka-tsantsan ba sa tafiya tare. To amma Amirul Muminin ya hada taka tsantsan mafi kaiwa koli da mafi tsayuwar hukuma, hakan kuwa lamari ne mai ban mamakin gaske.
Ya kasance ne mutum ne da ba ya jin nauyin kowa (wajen tabbatar da adalci da hukumcin Ubangiji). Matukar a ra'ayinsa wani shugaba ko jami'i yana da rauni kuma bai dace da aikin da aka ba shi ba, to kuwa ya kan tube shi. A matsayin misali, yana daukan Muhammad bin Abubakar a matsayin dansa ne, kamar yadda yake kaunar dansa haka yake kaunarsa, shi ma (Muhammad) yana ganin Amirul Muminin (a.s) ne tamkar mahaifinsa. Shi ne karamin dan halifa Abubakar sannan kuma mabiyin Amirul Muminin (a.s) na hakika, kuma a hannun wannan ma'abocin girma ya girma. Amirul Muminin (a.s) ya tura Muhammad bn Abubakar zuwa Masar, daga baya kuma sai ya rubuta masa wasika yana cewa lalle ni ina jin cewa - kamar yadda muke fadi - ya kai abin kaunata ba za ka wadatar da Masar ba, don haka na cire ka na dora Malik al-Ashtar. Muhammad bn Abubakar bai ji dadin hakan ba, ransa ya baci. Mutum ne fa, duk kuwa da cewa matsayinsa babban matsayi ne, amma daga karshe dai an taba shi. To amma ko kadan Amirul Muminin bai damu da hakan ba. (Ku duba ku gani) Muhammad bn Abubakar, mutum mai irin wannan matsayi, yayi yakin Jamal sannan kuma lokacin mubaya'a ya amfani Amirul Muminin, da ne wajen Abubakar sannan kuma kani yake ga Uwar Muminai - A'isha -. Saboda haka irin wannan mutumin yana da wani matsayi na musamman a wajen Amirul Muminin, to amma wannan ma'aboci girman bai taba rufe ido kan hakan ba, bai ba wa wannan damuwa da bakin ciki na Muhammad bn Abubakar wani muhimmanci ba. Wannan shi ne taka tsantsan. Taka tsantsan din a gwamnati yakan amfani su kansu mutane da kuma su kansu jami'an gwamnati. Mafi girma daukaka da kolin taka tsantsan ya kasance cikin gwamnatin Amirul Muminin.....
Wani misalin kuma shi ne karfi da kuma irin zaluncin da aka yi wa wannan bawan Allah. A zamanin wannan babban bawan Allah, wane ne ya fi Amirul Muminin (a.s) - wannan jarumi mai ban mamaki - karfi da jaruntaka? Har zuwa karshen rayuwar Amirul Muminin (a.s) babu wani mutum da ya taba bugun kirjin cewa yana da jaruntakar da zai iya tsayawa a gaban jaruntakarsa. Wannan mutum, shi ne mutumin da aka fi zalunta a zamaninsa - kamar yadda aka fadi kuma haka lamarin ma yake - mai yiyuwa ne ma shi ne mutumin da aka fi zalunta tsawon tarihin Musulunci. Karfi da zaluntar mutum wasu siffofi ne guda biyu da ba su haduwa tare. A mafi yawan lokuta ba a zaluntar ma'abota karfi, to amma an zalunci Amirul Muminin (a.s).
Wani misali na daban shi ne zuhudu (gudun duniya) da ayyukan gina kasa. Amirul Muminin (a.s), a bangaren zuhudu da rashin ba da kima ga duniya abin misali ne. mai yiyuwa ne jigo mafi girma ko kuma daya daga cikin mafiya girma da aka yi magana kansu cikin littafin Nahjul Balaga, shi ne zuhudu. Shi kansa Amirul Muminin (a.s) din shi ne wanda tsawon shekaru ashirin da biyar tsakanin wafatin Manzon Allah (s.a.w.a) zuwa lokacin halifancinsa, ya yi amfani da dukiyarsa wajen ayyukan gina kasa, ya kan gina lambuna, ya kan tona rijiyoyi, ya kan samar da magudanan ruwa da samar da gonaki. Babban abin mamakin shi ne cewa dukkan wadannan ayyuka ya kan yi su saboda Allah.
Bai baci ba idan muka fahimci cewa Amirul Muminin (a.s) yana daga cikin mutanen da suka fi samun kudaden shiga a zamaninsa. An nakalto shi yana cewa: "Idan aka raba sadakar da nake fitarwa ga Bani Hashim, da ta ishe su", (Bihar al-Anwar, juzu'i na 41, shafi na 43).....
Adalcin Aliyu bn Abi Talib shi ma wata siffa ce. A lokacin da muke cewa akwai adalci tattare da Aliyu bn Abi Talib, amincin Allah ya tabbata a gare shi, fahimta ta farko da kowane mutum zai yi ita ce cewa ya shimfida adalci na zamantakewa tsakanin mutane. Wannan shi ne adalci; amma adalcin da ya fi hakan shi ne daidaitawa. 'Da adalci ne aka tabbatar da sammai da kassai' (Awali al-Li'ali, juzu'i na 4, shafi na 103)
Wato daidaito cikin halitta. Wannan shi ne gaskiya. Shi ne adalci da kuma gaskiya. A karshe dai adalci da gaskiya abu guda ne, suna da ma'ana daya. A rayuwar Amirul Muminin (a.s), siffar da ake iya gani ita ce siffar adalci da daidaito. Dukkanin abubuwa masu kyau suna nan a wajensu a yanayi mafi kyau.
Wata siffar kuma da Amirul Muminin (a.s) ya kebanta da ita, ita ce neman gafarar da wannan mai girma ya ke yi....Addu'oi da tuba da neman gafarar da Amirul Muminin (a.s) ya ke yi suna da matukar muhimmanci. Mutumin da yake yaki da gwagwarmaya, ya ke shiga fagen yaki, sannan kuma ya ke shiga fagen siyasa. Ya jagoranci kasa mafi girma a duniya a wancan zamanin na tsawon shekaru biyar. (Idan muka dubi yankin da ke karkashin hukumar Amirul Muminin (a.s) za mu ga cewa ya kai na kimanin kasashe goma ko makamantan haka), irin wannan iko mai fadin gaske da kuma irin wadannan ayyuka da himma, muna iya cewa lalle Amirul Muminin (a.s) wani gagarumin dan siyasa ne wanda a hakikanin gaskiya ya ke mulkin duniya, musamman idan muka yi la'akari da irin siyasarsa, fagen yakinsa, yadda ya gudanar da lamurran da suka shafi zamantakewa ta al'umma da yadda ya gudanar da hukumci tsakanin al'umma da kiyaye hakkokin mutane da yayi. Wadannan ayyuka ne masu girman gaske, wanda yake bukatar aiki da himmar gaske da ke daukan dukkan lokacin mutum. A cikin wurare irin wadannan mutanen da suke da bangare daya suna cewa wannan aikin yana a matsayin ibadarmu ne. Muna aiki ne a kan tafarkin Allah, muna yin aiki ne saboda Allah. Shi kuwa Amirul-Muminin baya yin magana kwatankwacin wannan. Yana yin wadannan ayyukan kuma yana yin ibadu..

SALO DA TARIHIN HUKUMAR AMIRUL MUMININ (A.S)
Abubuwan Lura Cikin Hukumar Amirul Muminin (a.s)
Na farko shi ne cikakken riko da addinin Allah da dagewa wajen tsayar da addinin Allah. Wannan shi ne abin lura na farko. Duk wata hukumar da asasin ayyukanta ba su kasance wajen tsayar da addinin Allah ba, ba hukuma ce ta Ali ba. A tsakiyan (lokacin) yaki - wadanda suka kasance a fagen dagan kallafaffen yakin shekaru takwas za su fahimci abin da nake fadi - a irin wannan yanayi da kowane soja himmarsa ita ce neman hanyar da zai kai hari sannan kuma ta wace hanya zai kare kansa. Wani mutum ya zo wajen Amirul Muminin (a.s) ya tambaye shi kan tauhidi, ya ce masa: cikin (surar) "Kul huwallahu ahad", me ake nufi da kalmar ‘ahad'? to wannan dai ba mas'ala ce ta asasi ba. Bai yi tambaya kan asalin samuwar Allah ba; ya yi tambaya ne kan wani reshe kawai. Wadanda suke kewaye da Amirul Muminin (a.s) sai suka zo gaba suka ce yanzu lokacin yin wannan tambaya ne? Amirul Muminin (a.s) ya ce: ‘a,a, ku bari in ba shi amsar tambayarsa. Mu saboda hakan ne muke yaki'. Wato yakin Amirul Muminin, siyasar Amirul Muminin, shata dagar Amirul Muminin, jinin dake cikin zuciyar Amirul Muminin (a.s) da dukkanin matakan da yake dauka a hukumarsa dukkansu don a tabbatar da addinin Allah ne. Wannan wani abin lura ne. Matukar tabbatar da addinin Allah bai zamanto manufa ba a tsarin Musulunci da kuma jamhuriyar Musulunci wacce take bayyana kanta a matsayin mai koyi da Imam Ali, ba ta damu ba ko mutane su yi aiki da addinin Allah ko kuma a'a, su kasance suna da akida ko ba su da ita, a tabbatar da hakki na Ubangiji ko kuma a'a, mu ce babu ruwanmu da hakan - matukar lamarin ya zama haka - to wannan ba hukuma ce ta Ali ba. Tabbatar da addinin Allah shi ne lamari na farko kuma shi ne jigon dukkanin siffofin rayuwar Amirul Muminin (a.s) da hukumar Amirul Muminin (a.s). Adalcinsa ma ya samo asali ne daga wannan. Tsarin demokradiyya da kula da mutane cikin rayuwar Amirul Muminin (a.s) ma yana da alaka da hakan.
Siffa ta biyu da kuma abin lura na biyu a hukumar Amirul Muminin (a.s) shi ne adalci; adalci na gaba daya. Wato babu wata maslaha ta kashin kai kuma babu wata siyasa da take da alaka da shi kansa da yake gabatar da ita kan adalci. "Shin kuna umurta na ne da in nemi nasara ta hanyar zalunci, wallahi ko da wasa" (Tuhaful Ukul, 185). Ni ba a shirye nake in yi nasara ta hanyar zalunci ba. Ku duba ku ga yadda wannan lamarin yake a fili, wani irin madaukakin kyalle ne wannan. Idan aka ce muku mai yiyuwa ne a wannan fage na siyasa, a wannan fage na gasa ta ilimi, a wannan fage na zabe, a wannan fage na yaki, za ku yi nasara to amma da sharadin sai kun aikata wannan zaluncin. To a nan wan ne za ku zaba? To Amirul Muminin (a.s) dai cewa ya yi ni kan ba na son wannan nasarar. Babu matsala in sha kashi, amma lalle ba zan yi zalunci ba. Dukkanin abubuwan da kuka ji dangane da adalcin Amirul Muminin (a.s), dukkansu suna nuni ne da bukatarsa wajen tabbatar da adalci na gaba daya. Tabbatar adalci ga kowa kuma cikin dukkanin lamurra; wato adalci na tattalin arziki, adalci na siyasa, adalci na zamantakewa da kuma adalci na kyawawan dabi'u. Wannan daya ne daga cikin abin lura na hukumar Amirul Muminin (a.s). Ba ya yarda da zalunci; ba ya mika kai ga zalunci, ko da kuwa zai rasa wani abu nasa ne. Daya daga cikin zalunci mafi girma shi ne nuna wariya. Shin nuna wariya ne cikin aiwatar da hukumci ko kuma wariya wajen aiwatar da dokoki da tsare-tsaren da aka tsara. A wajen Amirul Muminin (a.s) wadannan ba abubuwa ne da zai amince da su ba....
Wata siffa daga cikin siffofin hukumar Amirul Muminin (a.s) kuma abin lura shi ne tsoron Allah. Ku duba ku gani, ko wane guda daga cikin wadannan abubuwa wata tuta ce wata alama ce. Me ake nufi da tsoron Allah? Shi ne irin tsananin taka tsantsan din da mutum yake yi cikin ayyukansa wajen ganin bai kauce wa tafarkin gaskiya ba; wannan ita ce ma'anar tsoron Allah. Wato mutum ya yi tsananin kula da kansa. Ya yi taka tsantsan wajen mu'amala da kudi, taka tsantsan wajen wasa da mutumcin mutane, taka tsantsan wajen zabi, taka tsantsan wajen watsi da abubuwa, taka tsantsan wajen magana kada a fadi abin da ba gaskiya ba. Wato tsananin kula da taka tsantsan. Idan kuka duba Nahjul Balagah za ku ga cike yake da wadannan batutuwa...ku dubi Nahjul Balaga tun daga farkonsa zuwa karshensa, dukkanin Nahjul Balaga cike yake da kira zuwa ga tsoron Allah; kira zuwa ga takawa da nesantar abubuwan da Allah ya hana. Matukar mutum bai zamanto mai tsoron Allah da nesantar abubuwan da ya hana ba, ba zai iya tsayar da addini ba.....Gurbatar zuciyar mutum da zunubbai ba ya barinsa ya fahimci gaskiya, ina kuma ga batun ya tafi neman gaskiyar. Tsoron Allah daya ne daga cikin siffofin hukumar Amirul Muminin (a.s), wacce ta ginu bisa nufi da bukatar mutane. Magudi - wato mutum ya mulki mutane ta hanyar tursasawa da amfani da karfi - ba ya cikin tunanin Amirul Muminin (a.s). Duk da yana jin (halifanci) hakkinsa ne, amma ya koma gefe har sai lokacin da mutane suka zo da kansu, suka nace, watakila ma suka yi kuka, suka yi ta roko suna cewa Malam ka zo ka mulke mu. A wannan lokacin ne ya zo, ya rike madafan mulkin al'umma. Shi da kansa yana cewa idan da a ce mutane ba su zo ba, idan da a ce ba su nace ba, idan da a ce wannan bukata ta mutane ba da gaske ba ce, to da ba ruwana da wannan aiki. Mulki ba wani abin burgewa ba ne a wajen Amirul Muminin (a.s). Neman mulki ya kan zama abin burgewa ne ga mutanen da suke son biyan bukatun zukatansu da soyace-soyacen zuciyarsu, ba haka lamarin yake a wajen Amirul Muminin (a.s) ba. Damuwarsa ita ce sauke nauyin shari'a, da neman tabbatar da gaskiya. Mutane ne suka mika masa mulki, shi kuma ya amince sannan kuma ya ci gaba da kare shi da dukkan karfinsa.

Abubuwa Uku Da Suka Fuskanci Hukumar Amirul Muminin (a.s)
Ana iya takaita abubuwan da suka faru lokacin Amirul Muminin (a.s) wadanda kuma suke tattare da zaluncin da aka yi masa kamar haka: a lokacin gwamnatinsa - hukumar da ba ta kai shekaru biyar ba - wannan mai girma ya fuskanci abubuwa guda uku: wato (fitinar) Kasitin da Nakithin da Marikin. Cikin wannan ruwaya wacce ‘yan Shi'a da Sunna duk sun ruwaito ta an ruwaito Amirul Muminin (a.s) yana cewa: "An umurce ni da in yaki al-Nakisin da al-Kasitin da al-Marikin" (Da'aim al-Islam, juzu'i na 1, shafi na 388) shi da kansa ne ya ba su wadannan sunaye.
Kasitin yana nufin azzalumai. Amirul Muminin shi da kansa ya sanya musu wannan suna na azzalumai. Su wane ne wadannan mutane? Su ne wadanda a zahiri suka amince da Musulunci saboda wata maslaha tasu wadanda tun asali ma ba su yarda da hukumar Imam Ali ba. Duk abin da Amirul Muminin (a.s) ya yi musu bai yi amfani ba.
....saboda haka, wata kungiya ce wacce tun farko ma ba ta yarda da hukumar Imam Ali (a.s) ba, suna so ne hukuma ta kasance ta wani yanayi na daban, wato ta kasance a hannunsu. Daga baya dai sun tabbatar da hakan sannan kuma duniyar musulmi ta ga irin nau'in hukumarsu. Wato shi kansa wannan Mu'awiyan wanda a lokacin da yake gasa da adawa da Amirul Muminin yake nuna so da kauna ga wasu daga cikin sahabbai, to amma daga baya a lokacin mulkinsa sai ga shi yana nuna musu mummuna hali da kakkausar mu'amala har lokacin da Yazid ya dare karagar mulki da abin da ya faru a Karbala. Daga baya kuma aka zo lokacin Marwan da Abdul Malik da Hajjaj bn Yusuf al-Thakafi da Yusuf bn Umar al-Thakafi wadanda suka samo asali daga wancan hukuma. Wato hukumar da tarihi ya kan girgiza yayin ambato irin zaluncin da ta aikata - irin hukumar Hajjaj - wadannan su ne hukumomin da Mu'awiyya ya gina tushensu sannan kuma bisa wadannan abubuwa ne suka yaki Amirul Muminin (a.s). Tun farko dai abin da suke so a fili yake, wato hukuma ta duniya kawai tsantsan, wacce ba abin da ta sa a gaba in ban da bautan soyace-soyacen zuciya, wato irin wadannan abubuwan da kowa da kowa ya gansu lokacin mulkin Banu Umayya. Koda yake ba wai ina son yin bahasi na akida ba ne a nan. Abin da nake fadi abubuwa ne da suka zo cikin tarihi. Ba wai tarihin Shi'a ba, a'a abubuwa ne da suka zo cikin tarihin Ibn Athir da tarihin Ibn Kutaiba da makamantansu wadanda ina da su kuma an ajiye su. Wadannan abubuwa ne da suke cikin abubuwan da babu mai kokwantonsu, ba wai lamari ne na sabanin tunani na Shi'a da Sunna ba.
Kungiya ta biyu da Amirul Muminin (a.s) ya yi yaki da ita, ita ce kungiyar Nakisin, wato wadanda suka karya (alkawari) mubaya'ar da suka yi. Da farko dai sun yi mubaya'a wa Amirul Muminin (a.s), to amma daga baya sun karya wannan mubaya'a ta su. Su din nan musulmi ne sabanin kungiya ta farko, masu son kansu ne. Sun yarda da hukumar Ali amma fa idan har za su sami kaso mai tsoka cikin hukumarsa; a dinga shawara da su, a ba su mukamai, a ba su mulki, kada a sanya ido kan dukiyar da suka samo, ka da a nemi jin cewa daga ina suka samo su...Mutane irin su Sa'ad bn Abi Wakkas tun farko ma bai yi mubaya'a ba, wasu daga cikinsu tun ma da farko ba su yi mubaya'a ba; to amma irin su Talha da Zubair wadannan manyan sahabban da sauransu sun yi mubaya'a ga Amirul Muminin (a.s), sun mika kai da kuma yarda da shi. To amma bayan gushewar watanni uku zuwa hudu, sai suka ga cewa lalle ba za a iya tafiya da wannan hukuma ba, saboda wannan hukuma ce da ba ta san aboki ba, mai tafiyar da hukumar ba ya ganin yana da hakki, haka nan iyalansa, haka nan wadanda suka riga shiga Musulunci ba su da wani hakki (sama da saura) - duk kuwa da cewa ya rigayi kowa shiga Musulunci - ba ya sassauci wajen gudanar da hukumcin Ubangiji. Lokacin da suka ga haka, sai suka yanke cewa lalle ba za a iya tafiya da irin wannan mutumin ba. Don haka sai suka janye, suka je suka shirya yakin Jamal wanda a hakikanin gaskiya fitina ce. Sun janyo uwar muminai A'isha cikinsu. An kashe mutane da daman gaske a wannan yakin. Daga karshe dai Amirul Muminin (a.s) ne ya yi nasara da dawo da lamurra yadda suka dace. Wannan ita ce kungiya ta biyu wacce ta shagaltar da Amirul Muminin (a.s) na wani lokaci.
Kungiya ta uku, ita ce kungiyar Marikin. Marik wato wanda suke ficewa. Yayin sanya musu wannan suna an nakalto cewa ficewar wadannan mutane daga addini ta yi kama da yadda kibiya ke ficewa daga jikin baka. Yayin da kuka ciro kibiya da sanya ta cikin baka da harbata, ya ya kuke ganin yadda wannan kibiya take fita da gudu. To wadannan mutane haka suka fice daga cikin addini. Ko da yake sun kasance masu riko da zahirin addini sukan kawo sunan addini ma. Su ne wadanda ake kira da khawarijawa. Su ne mutanen da suka gina ayyukansu bisa asasin gurguwar fahimta ta addini - hakan lamari ne mai hatsarin gaske. A saboda haka, kungiya ta uku da Amirul Muminin (a.s) ya yi fama da ita, wanda kuma ya yi galaba a kanta ita ce kungiyar marikawa. Amirul Muminin ya yi gagarumar nasara a kansu a yakin Nahrawan; sun kasance cikin jama'a, ko da yake karshensu ya zo ne lokacin da ya yi shahada....
Wasu suna kwatanta hawarijawa da masu girmama ababe masu tsarki (na addini); ko da wasa. Batun ba na girmama ababe masu tsarki ba ne. Nuna kai da zama ana salla da addu'a. Wannan ba shi ne ma'anar haraijawa ba. Hawarijawa su ne masu son yin bore, suna haifar da fitina, suna shigowa fage, suna bahasin yaki da Ali sannan kuma suna yaki da Ali; alhali asasin aikin nasu kuskure ne, yakin kuskure ne; abin da suke bayyanawa kuskure ne, sannan manufarsu ta bata ce. Wadannan su ne kungiyoyi uku da Amirul Muminin (a.s) ya fuskanta.

Rashin Tabbataccen Layi, Shi Ne Babban Bambancin Hukumar Amirul Muminin (a.s) da ta Manzon Allah (s.a.w.a)
Bambanci na asasi tsakanin Amirul Muminin (a.s) lokacin mulkinsa da Manzon Allah (s.a.w.a) a lokacin mulkinsa da rayuwarsa mai cike da albarka shi ne cewa a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a) matsaya a fili take: ko dai tafarkin imani ko kuma na kafirci. Munafukai suna nan wadanda a ko da yaushe ayoyin Alkur'ani suna jan kunnen muminai da su yi hankali da su; ya kasance yana ishara da nuni da su, yana karfafa muminai wajen fuskantarsu; yana raunana ruhinsu. Wato a gwamnatin Musulunci lokacin Ma'aiki (s.a.w.a) komai a fili yake. Kamar yadda kuma wadanda suke fuskantarsu ma a fili suke: a bangare guda ga wadansu nan wadanda suke goyon bayan kafirci da dagutu da jahiliyya; daya bangaren kuma ga masu goyon bayan imani da Musulunci da tauhidi da addini. Ko da yake a wancan lokacin ma akwai mutane kala-kala - a wancan zamanin ma akwai dukkan nau'oi na mutane - to amma an shata daga. Amma a zamanin Amirul Muminin (a.s), matsalar da ake fuskanta ita ce cewa abubuwa ba a fili suke ba; saboda su kansu wadannan ‘yan kungiya ta biyu - wato nakisin - mutane ne da suke da matsayi a idanuwan al'umma. Kowane mutum ya tsaya wajen fuskantar mutane irin su Zubair ko Talha lalle zai samu shakku. Saboda shi wannan Zubairun mutum ne mai matsayi a zamanin Ma'aiki (s.a.w.a) dan baffan Manzon Allah (s.a.w.a) kuma na kurkusa da shi. Sannan kuma hatta bayan Ma'aiki (s.a.w.a) ya kasance daga cikin mutane da suka mike a Sakifa wajen kare Amirul Muminin (a.s). Na'am, ana hukumta mutum ne da karshensa. Muna rokon Allah da Ya kyautata karshenmu. A wasu lokuta neman duniya yana haifar da irin wannan yanayi, ya kan haifar da irin wannan gagarumin sauyi cikin rayuwar mutum ta yadda mutum yana iya fuskantar matsala da shakku cikin zuciyarsa, ina ga kuma sauran mutane amawa. A saboda haka, a wancan lokacin lamura suna da wahalar gaske. Mutanen da suka kasance tare da Amirul Muminin (a.s) sannan kuma suka ci gaba da tsayawa kyam tare da shi lalle sun yi amfani da basirarsu sosai. A lokuta da dama na sha karanto wannan magana ta Amirul Muminin (a.s) dake cewa: "Babu mai iya rike wannan ilimi sai ma'abuta gani da hakuri" (Bihar al-Anwar, juzu'i na 34, shafi na 249) A matakin farko basira wajibi ne. A fili yake cewa irin wadannan rikice-rikicen suna bayyana matsalolin da Amirul Muminin (a.s) ya fuskanta. Ko kuma irin wadannan ma'abota riya masu da'awar riko da Musulunci amma suna yaki da Amirul Muminin (a.s) suna fadin maganganun kuskure. A farko-farkon Musulunci, akwai tunani da akidu na bata da yawa; amma ayoyin Alkur'ani suna saukowa suna yin watsi da wadannan tunani, shin a zamanin (Annabi) yana Makka ne ko kuma lokacin da ya koma Madina. Ku dubi Suratul Bakara wacce sura ce ta Madina ku gani, a lokacin da mutum ya dube ta zai ga cewa tana magana ne kan kalubale da rikice-rikice daban-daban da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi da munafukai da yahudawa; a wasu lokuta ma ya kan yi cikakken bayani, hatta hanyoyin da yahudawan Madinan suke bi wajen cutar da Ma'aiki da shagaltar da hankalinsa, an ambace su cikin Alkur'ani; a matsayin misali ayar nan ta (لاتقولوا راعنا) "Kada ku ce: Ra'ina" (Suratul Bakara 2:104) da makamantansu. Haka nan a Suratul A'araf ma - wacce sura ce ta Makka - ta ambaci fasali makamancin wannan, tana fada da camfe-camfe. Dangane da batun haramta ko halalta naman da aka haramta amma suna kiransu da sunan abubuwan da aka haramta na karya "Ka ce: Abin sani kawai, Ubangijina Ya hana abubuwan alfasha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu" (Suratul A'araf 7:33).
Wadannan su ne abubuwan da suke haramun, ba wai wadancan irin su ‘Sa'iba da ‘Bahira' (sunayen dabbobi ne da ake barinsu a wancan lokacin don tsafi) da sauransu da kuka haramta wa kanku ba. Alkur'ani a fili ya yi fada da irin wannan tunani; amma a lokacin Amirul Muminin (a.s), su kansu masu adawa da shi din suna amfani da ayoyin Alkur'ani din ne, suna fakewa da Ayoyin Alkur'anin. Saboda haka ayyukan Amirul Muminin (a.s) a wannan bangare suka zamanto da wahala. Amirul Muminin (a.s) ya gudanar da takaitaccen zamanin mulkinsa ne cikin irin wadannan wahalhalu.
A gaban dukkan wadannan akwai kuma sansanin shi kansa Ali; wani sansani mai karfin gaske. Akwai mutane irin su Ammar da Malik al-Ashtar da Abdullah bin Abbas da Muhammad bin Abi Bakr da Maitham al-Tammar da Hujr bin Adi; mutane ne ma'abota imani da basira da sanin ya kamata wadanda suka ba da gagarumar gudummawa wajen shiryar da tunanin mutane. Daya daga cikin bangarori masu kyau na zamanin Amirul Muminin (a.s) - koda yake mai kyau ne a bangaren kokari da ke cike da kwarewa na wadannan manyan mutane; amma kuma abu mai sosa rai a bangaren irin wahalhalun da suka sha - shi ne yanayin fitarsu zuwa (garuruwan) Kufa da Basra. Lokacin da Talha da Zubairu da makamantansu suka zo suka ja daga, suka kama garin Basra suka kama hanyar Kufa. Imam Ali (a.s) ya aika da Imam Hasan da wasu sahabbansa. Irin tattaunawar da suka yi da mutane, maganganun da suka gaya musu a masallaci, irin kafa hujjojin da suka yi yana daga ciki bangarori masu cike da kumaji da kyau cikin tarihin farkon Musulunci. A saboda haka ne za ku ga cewa hare-hare da farfagandar makiyan Amirul Muminin (a.s) sun fi shafan wadannan mutane ne. Sun kulla mafi girman makircin ga Malik al-Ashtar, haka nan ga Ammar Yasir, haka nan ga Muhammad bn Abi Bakar. An kulla makirci ga wadannan mutane wadanda tun farko suka kasance tare da Amirul Muminin (a.s) sannan kuma suka tabbatar da irin karfafaffen imani da tsayin daka da basirar da suke da su. A bangaren makiya kuwa babu irin makirci da tuhumar da ba a yi musu ba da kuma neman rayukansu, a saboda haka ne mafi yawansu suka yi shahada. Ammar ya yi shahada ne a wajen yaki; amma Muhammad bn Abi Bakr ya yi shahada ne sakamakon hilar mutanen Sham. Haka shi ma Malik al-Ashtar ya yi shahada ne ta hanyar makircin mutanen Sham. Wasu daga cikinsu kuma sun saura, amma daga baya sun yi shahada ta mafi munin yanayi. Wannan shi ne yanayi rayuwa da hukumar Amirul Muminin (a.s). Idan har muna so mu dunkula maganarmu, to muna iya cewa lokacin wannan hukuma, lokaci ne na wata hukuma tsayayya amma a lokaci daya kuma wacce aka zalunta sannan kuma ta yi nasara. Wato a zamaninta ta samu nasarar durkusar da makiya kasa, sannan kuma bayan shahadarsa ya samu nasarar zama tamkar wata fitila mai haske a saman tarihi. Koda yake jinin da ke zuciyar Amirul Muminin (a.s) tsawon wannan lokaci ya kasance daga cikin wadanda ya fi fuskantar matsaloli da fitinu tsawon tarihi.


WASIYOYI DA UMARNIN AMIRUL MUMININ (A.S)

Daga Cikin Wasiyoyin Amirul Muminin (A.S)
Batun farko da kuma na karshe cikin maganganun Amirul Muminin (a.s) shi ne tsoron Allah (takawa). Yana cewa: "Ya ku ‘ya'yana! Ku kula da kanku; a tafarkin Allah da kuma mizani na Ubangiji", tsoron Allah shi ne wannan. Lamarin ba wai shi ne tsoron Allah (wato da ma'anar da aka san shi ba wato firgita) saboda wasu suna fassara takawa da ‘tsoron Allah (da wannan ma'anar). Na'am tsoron Allah da wannan ma'ana yana da nasa kimar. To amma takawa tana nufin mutum ya kula duk wani aikin da zai yi ya zamanto ya doru ne bisa abin da Allah ya tsara masa. Takawa ba abu ne da cikin sauki mutum zai yi watsi da shi ba. Idan har muka yi watsi da ita to da akwai hanya mai santsi a gabanmu, lalle santsi zai kwashe mu, za mu kuma fadi kasa har lokacin da hannunmu zai samu damar rike wani abu mai karfi ko wani dutse har mu iya tasowa sama.
"Lalle ne wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga Shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah) sai ga su, sun zama masu basira (Suratul A'araf 7:201) A lokacin da mutum mai takawa ya fara jin tashin hankalin Shaidan, cikin gaggawa ya kan dawo cikin hankalinsa da tara tunaninsa waje guda. Shaidan dai ba ya rabuwa da mu, don haka wasiya ta farko ita ce takawa.

Abubuwan da suke lazumtar Takawa: Nesantar Neman Duniya Ido Rufe
Neman takawa wani batu ne na daban. "kada ku rusuna ga duniya ko da kuwa tana bin ku". Wannan shi ne lamari na biyu. Hakan yana daga cikin wajiban takawa. Koda yake dukkanin ayyukan kwarai suna daga cikin wajiban takawa. Daga cikin har da batun nesantar neman duniya ido rufe. Ba wai yana cewa a yi watsi da duniya ba ne, abin da yake cewa shi ne kada ku rusuna ga duniya, kada ku nemi duniya (ido rufe). Mece ce duniya? Tana nufin gina kasa? Tana nufin raya dukiyar Ubangiji? Wannan shi ne ma'anar duniyar da aka ce kada mu neme ta? A'a, duniya tana nufin abin da kuke nema don kawunanku don jin dadin kanku. Wannan shi ne abin da ake kira duniya. Idan kuwa ba haka ba, gina kasa idan dai har da manufa mai kyau aka yi ta daidai take da (ayyuka don) lahira. Wannan ita ce duniya mai kyau. Duniyar da aka suka wacce kuma bai kamata mu tafi nemanta ba, ita ce duniyar da take cinye mana dukkanin karfinmu da kokarinmu da himmarmu zuwa gare ta sannan kuma ta karkatar da mu daga tafarki. Son zuciyarmu, bauta wa soyace-soyacen zuciyarmu, neman dukiya don kanmu da kuma neman jin dadin duniya, wannan ita ce duniya abar kyama.
Na'am wannan duniyar tana da bangare na haramun kamar yadda take da bangare na halaliya. Ba haka lamarin ya ke ba cewa neman kowane abu domin amfanin kai haramun ne. A'a, akwai na halal. To amma shi kansa halal din ma sun ce kada a tafi nemansa. Idan har duniya ta kasance da wannan ma'ana, to halal dinta ma ba shi da kyau. Dukkanin kokarin da za ku iya wajen mayar da zahirin duniya zuwa tafarkin Allah, ku neme shi sannan kuma ku yi amfani da hakan. Wannan shi ne ma'anar lahira. Harkokin kasuwanci matukar ana yinsu saboda kyautata rayuwar mutane ne ba wai don arzurta kai (da cutar da wasu ba) tamkar aikin lahira ne. Sauran ayyukan duniya ma tamkar hakan ne. Saboda haka, batu na biyu shi ne kada mu sanya neman duniya a gabanmu ido rufe.
Abin da Amirul Muminin (a.s) ya fadi cikin wannan wasiyya shi kansa ya kasance tamkar madubi ne da ke nuni da dukkan wadannan abubuwa. Idan muka dubi rayuwarsa za mu ga cewa tana a matsayin takaitaccen bayani na wadannan jumloli da suka zo cikin wasiyyar. "kada ku yi bakin ciki a kan wani abu na duniya da aka hana ku", wato idan ba ku sami wani abu na wannan duniya abar suka ba ko kuma aka hana ku, to kada ku yi bakin ciki. Kada ku yi bakin ciki don ba ku da irin wannan dukiya, ko kuma ba ku da irin wannan jin dadin ko kuma kun rasa wani mukami ko walwala ba. Wannan ita ce jumla ta uku.
Jumla ta gaba (ita ce): "Ku fadi gaskiya" (kamar yadda ya zo cikin wani bugun) ko kuma "Da fadin gaskiya), babu bambanci cikin hakan. Abin da dai ake nufi shi ne ‘ku fadi gaskiya', wato ku fadi gaskiya kada ku boye wani abu. Idan har wani abu a ganinku gaskiya ne, to ku fade shi a wajen da ya zama wajibi ku fade shi. Kada ku boye gaskiya. A lokacin da masu magana suka boye gaskiya sannan kuma suka bayyanar da karya, ko kuma suka gabatar da karya a wajen gaskiya, idan har ma'abota gaskiya suka fadi gaskiyar to gaskiya ba za ta zama abin zalunta ba, gaskiya ba za ta zama bakon abu ba, sannan kuma ma'abota karya ba za su sami karfin gwuiwan kawar da gaskiya ba.
Jumla ta gaba (ita ce): "da kuma yin aiki don lada", wato ku yi aiki saboda neman lada -lada daga wajen Ubangiji, kada ka yi aiki haka kawai Ya kai mutum! Wannan aiki naka, wadannan shekaru naka da wannan numfashi da kake yi su ne jarinka na asali. Ka da ka bari haka kawai su kubuce daga hannunka. Idan har kana son gudanar da rayuwarka, idan kana son gudanar da wani aiki, idan kana son sarrafa numfashinka da karfinka to ka sarrafa su saboda lada. Menene lada? Shin wasu ‘yan tuman (sunan kudin Iran) shi ne ladan samuwar mutum? Shin shi ne ladan rayuwata da na sarrafa ta? Barka da zuwan wani shi ne ladan wani mutum? Ko da wasa. " Rayukanku ba su da kima idan ba aljanna ba, kada ku sai da ita ga wani abu ba ita ba" (Nahjul Balaga, hikima ta 456) wannan jumlar daga Imam yana fadin cewa: "Akwai ‘yantaccen mutum da zai bar wannan sauran abinci (duniya) ga masu sonta? Lalle, ladan da kake da shi shi ne Aljanna. Saboda haka kada ka sayar da kanka sai dai saboda Aljanna"

Ku Kasance Masu Husuma da Azzalumi, Masu Taimakon Wanda Aka Zalunta
Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ku kasance masu tsanani ga azzalumai, kana masu taimakon wanda aka zalunta", wato ku kasance mai husuma da azzalumi. Mai husuma ya saba da makiyi. A wani lokaci mutum ya kan zama makiyin azzalumi; wato ba ya kaunar azzalumi kuma yana kiyayya da shi. To hakan bai wadatar ba. ‘Ka kasance mai husuma da shi, wato ka kasance mai tsanani gare shi. Ka rike wuyansa kada ka sake shi. Bil'adama bayan Amirul Muminin (a.s) zuwa yanzu, sakamakon rashin rike wuyan azzalumai sun fada cikin bala'i da damuwa. Idan da a ce hannayen mutane masu imani sun rike wuyayen azzalumai, da zalunci bai yadu irin yaduwar da yayi ba, face ma dai ya ya fadi kasa. Wannan shi ne abin da Amirul Muminin (a.s) yake so: "Ku kasance masu tsanani ga azzalumai". A duk fadin duniya, a duk inda zalunci yake da kuma azzalumi, to kai da kake nan ka dauki kanka a matsayin mai husuma da shi. Ba wai muna cewa ne ka tashi daga wannan bangaren na duniya ka nufi wancan bangaren na duniya ba ka kama wuyayen azzalumai ba. Abin da muke cewa shi ne lalle ka nuna husumarka. A duk inda ka samu dama ka zamanto mai husuma da shi ka kuma kama wuyansa." A wani lokaci mutum ba zai sami damar kusatan azzalumi har ya sami damar nuna husumarsa ba; a saboda haka daga nesa ne ya ke nuna husumar tasa. Ku duba ku ga abubuwan da suke faruwa a duniyan nan a yau da kuma irin matsalolin da bil'adama suke fuskanta sakamakon rashin aiki da kalma guda ta wannan wasiyya ta Amirul Muminin (a.s). Ku dubi irin zaluncin da al'ummomi musamman al'ummar musulmi suke fuskanta. Idan da a ce an yi aiki da wannan wasiyya guda ta Amirul Muminin (a.s), da da dama daga cikin zalunci da masifun da suka samo asali daga zalunci ba su faru ba.
"Kana mai taimakon wanda aka zalunta", a duk inda aka sami wanda aka zalunta, ku taimaka masa. Ba wai an ce ku zama mai goya masa baya ba ne. A'a! wajibi ne ka taimaka masa. Ta duk yadda za ka iya ta kuma kowace hanya.
Na'am wannan wasiyya ta Imam Ali (a.s) yana magana ne ga Imam Hasan da Imam Husaini, amincin Allah ya tabbata a gare su. Amma tabbas wadannan maganganu ba su kebanta da Imam Hasan da Imam Husaini amincin Allah ya tabbata a gare su ba kawai. Maganar da su ake yi, amma ta dukkan mutane ce.
Jumla ta gaba cikin wannan wasiyya ta Amirul Muminin (a.s) yana magana ne da dukkan mutane, yana cewa: "Ina muku wasici, da kuma dukkan ‘ya'yayena da iyalaina da dukkan wanda rubutuna ya isa gare shi".
Bisa wannan lissafin, ku da kuke zaune a nan da ni da nake karanto muku wannan wasiyya, dukkanmu muna cikin wadanda Amirul Muminin (a.s) yake magana da su. Yana cewa: "Dukkanku ina muku wasici", da wani abu? "Da tsoron Allah". Maganar farko da ta karshe ta Amirul Muminin (a.s) ita ce takawa (tsoron Allah). Daga nan kuma sai ya ci gaba da cewa: "da tsara al'amurranku". Me ake nufi da tsara lamurranku? Wato dukkan ayyukan da kuke yi a cikin rayuwarku, su zama tsararru? Wannan shi ne abin da ya ke nufi? Abu ne mai yiyuwa wannan ya kasance shi ne ma'anarsa. Bai ce ‘tsara al'amurra' ba. Cewa ya yi: "da tsara al'amurranku". Mutum ya kan iya fahimtar cewa abin nufi da wannan sigar zancen ita ce al'amurra da dukkan mutane suka hadu a kansu. Daga dukkan alamu "tsara al'amurranku" yana nufin tsayar da gwamnati da hukuma da wilaya ta Musulunci. Ma'anarsa ita ce ku tsara lamurranku na hukuma da gwamnati su yi daidai da tsari, ka da su zamanto cikin rashin tsari......

Kyautata Alaka Tsakanin Mutane.
Abu na uku dake cikin bangare na biyu na wasiyyar shi ne fadinsa cewa: "kyautata alaka tsakani". Wato ku zamanto masu kyakkyawar alaka da juna. Zukata su zamanto tare. Maganganunku su zamanto daya, kada a samu rikici da sabani a tsakaninku. Sai kuma ya kawo wani shaida daga cikin maganganun Ma'aikin Allah (s.a.w.a). Abu ne da ya ke a fili cewa yana ba shi muhimmanci kuma yana tsoronsa, ba wai saboda cewa kyautata tsakani ya fi tsara al'amurra muhimmanci ba ne; sai dai saboda kasantuwar kyautata alaka tsakani zai fi samun koma baya. Saboda haka ne ya nakalto wannan magana daga wajen Ma'aiki (s.a.w.a) cewa: "don kuwa na ji kakanku (Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Kyautata tsakani ya fi salla da azumi". Idan kuna so ku je ku yi salla da azuminku. To amma akwai wani aiki wanda falalarsa ta fi dukkan wadannan abubuwa guda biyu. Mene ne wannan abu? Shi ne kyautata tsakani. Idan a wani lokaci kuka ga tsakanin al'ummar musulmi an samu rikici da sabani, to ka tafi ka toshe wannan baraka da aka samu. Falalar hakan ta fi ta salla da azumi.

Kula da Yanayin Marayu
Bayan ya yi bayanin wadannan jumloli, sai kuma ya yi bayanin wadansu ‘yan kalmomi masu cike da ma'ana da kuma sosa rai: "Ina hada ku da Allah cikin al'amarin marayu", wato duk abin da za ku iya ku yi wajen biyan bukatun marayu. Kada ku taba mancewa da su. Lalle wannan lamari ne mai muhimmancin gaske. Ku duba ku ga yadda wannan mutumin masanin bil'adama, masanin Allah, masanin yanayin bil'adama yadda yake ganin wannan lamarin. Na'am, biyan bukatun marayu. Ba wai kawai jin kai a zuci da kuma tausayawa ba ce. Yaron da ya rasa mahaifinsa, tamkar mutumin da ya rasa daya daga cikin tushen abin da yake bukata ne, wanda shi ne mahaifi. Wajibi ne ku cike wannan gurbi ta wata hanya. Duk da cewa ba za a iya cikewa ba, to amma wajibi ne matashi da samari da yaron da ya rasa ransa kada ya shiga cikin muguwar wahala. "Ina hada ku da Allah cikin al'amarin marayu, kada ku bari su shiga cikin wahala", kada ku bari su kasance cikin yunwa. Kada yanayi ya zamanto yau su samu gobe su rasa. Wato a kula da su cikin abubuwan da rayuwa take bukatarsu. "sannan kada a cutar da su a gabanku", wato kada ku bari wani abu ya same su kuna gani. Idan har ba ku nan, ba ku sani ba; amma kada ku bari kuna nan a cutar da wani maraya - kowane irin maraya ne kuwa. Bai kamata mutum ya sa lamurransa kawai a gaba ba alhali yara marayu su zama su kadai.

Kula Da Hakkokin Makwabta
"Ina hada ku da Allah cikin al'amarin makwabtanku". Lalle kada ku dauki batun makwabtaka da sauki. Lamari ne mai matukar muhimmanci. Wani lamari ne na kyautata alaka ta zamantakewa wanda Musulunci ya ba shi gagarumin muhimmanci wanda kuma ya yi daidai da dabi'a ta dan'adam. Ko da yake wannan lamari mai girma ya yi karanci cikin ci gaba da al'adun da suka yi nisa da dabi'a ta dan'adam....wajibi ne ku kula da makwabtanku. Ba wai kawai a bangare na kudi da tattalin arziki ba - duk da cewa hakan lamari ne mai muhimmanci - face dai ta dukkan bangarori na rayuwa. Idan aka samu hakan, za ku ga irin so da kaunar juna da zai yadu cikin al'umma sannan kuma yadda cututtukan da ba su da magani za su sami magani. "Domin kuwa sun kasance wasiyyar Annabinku" ta yadda: "Ya kasance yana yawan magana a kansu har sai da muka tsammaci zai ba su wani sashi na gado".

Ina Hada Ku Da Allah Cikin Alkur'ani
"Ina hada ku da Allah cikin lamarin Alkur'ani, kada ku bari waninku ya wuce gabanku wajen aiki da shi". Kada ku bari wasu wadanda ba su yi imani da ma'anonin Alkur'ani ba su wuce gabanku, ku da kuke da imani da shi, wajen aiki da Alkur'ani har ku kasance a baya. Wato hakan ta riga ta faru! Mutanen da a duniya suke gaba, sun ci gaba din ne ta hanyar aiki da bin diddiginsa da yinsa yadda ya kamata da kuma misaltuwa da siffofi masu kyau wadanda Allah Madaukakin Sarki Yake so. Ba wai ta hanyar fasadinsu ba da shan giyansu ko kuma zaluncin da suke aikatawa...

Jan Kunne Kan Kauracewa Dakin Allah
"Ina hada ku da Allah dangane da Dakin Ubangijinku (Ka'aba), kada ku kaurace masa matukar dai kuna raye, don kuwa idan aka bar shi ba za ku tsira ba". Akwai ma'anoni daban-daban cikin wadannan jumloli.

Kada A Bar Jihadi
"Ina hada ku da Allah kan jihadi saboda Allah da dukiyoyinku, kawukanku da harsunanku". Wannan jihadi shi ne dai wannan jihadin da a duk lokacin da al'ummar musulmi suka rike shi za su zamanto abin koyi na duniya, idan kuma suka yi watsi da shi za su kaskanta....
Jihadi da irin wannan kama ta shi ta Musulunci - wanda yake da iyakoki - ba zalunci ba ne. A jihadi, babu wuce haddi kan hakkokin mutane. A jihadi, babu batun fakewa da wasu dalilai marasa kwari domin kashe wannan da wancan. A jihadi babu maganar kawar da wani mutum don ba musulmi ba ne. Jihadi wani hukumci ne na Ubangiji wanda yake da girman gaske. Matukar aka riki jihadi, to al'ummomi za su daukaka.
Daga nan kuma sai ya ce: "(Ina) gargadinku da kiyaye zumunci da biyan bukatun al'umma, sannan kuma ku nisanci kauracewa juna da kuma yanke zumunci. Kada ku bar umurni da ayyukan alheri da kuma hani da munana", don idan kuka bari "sai mafiya sharrin cikinku su doru a kanku". Matukar mutane ba su kasance masu ganin munin muggan mutane ba, to mafi sharri al'umma za su doru a kan mutane su rike madafun ikonsu. Sannan "kuma ku yi addu'a", wato ku mutanen kirki za ku yi addu'a kuna cewa: 'Ya Ubangiji ka cece mu daga hannun wadannan muggan mutane', amma "a ki karba".

NAUYIN DA KE KANMU WAJEN FAHIMTAR HUKUMAR AMIRUL MUMININ (A.S)
Daukar Nauyi Saboda Allah kadai.
Fadin cewa wajibi ne mu dau darasi daga wajen Amirul Muminin (a.s) ba wai hakan yana nufin za mu iya kaiwa ga matsayin da yake kai ba ne - babu wani wanda ya isa ya kai wannan matsayi - face dai ma'anar hakan shi ne duk wani mutumin da yake aiki karkashin tsarin jamhuriyar Musulunci, a duk inda yake aiki, wajibi ne ya kula da wannan lamari, kada ya mance da shi, ya yi iyakacin kokarinsa wajen ganin cewa duk wani aiki da zai yi ya yi shi ne don Allah. Duk wani nauyi (mukami) da zai karba ya karbe shi ne don Allah, sannan duk wani yunkuri da zai yi, ya zamanto ya yi shi ne don Allah....
Idan abin da mutum zai fada da wanda zai aikata da kuma wani nauyi da zai dauka, suka zamanto saboda Allah ne, to ayyukan mutum za su zama masu sauki. Kasantuwarsa saboda Allah ne son zuciyar mutum ba zai zama yana da tasiri a ciki ba. Babu abin da ke haifar da son zuciya cikin wannan fage. A saboda haka karbar wani mukami yake da sauki, hakan nan ajiye wannan mukamin yake da sauki. Aiwatar da wani kuduri yake da sauki, fadin abin da ya kamata a fadi yake da sauki, rashin fadin abin da bai kamata a fadi ba shi ma yake da sauki. Daukan mataki yake da sauki, kurbar guba ya ke da sauki, fuskantar dukkan duniya da kuma ma'abota karfin duniya shi ma yake da sauki.
Abin da yake sanya lamurra su zama masu wahala, mu ne da kanmu, soyace-soyacen zukatanmu da son duniyarmu. Idan har muka zama haka, to me zai faru? Wata cutarwa ce za ta same mu? Wasu abubuwa ne za mu rasa? A duk lokacin da muka yi watsi da 'ni' da 'kaina' da son zukatanmu, muka sanya dukkanin abubuwan da za mu aikata suka zama don Allah ne, to dukkanin ayyuka masu wahala za su zama masu sauki. Idan har kuna son ganin wannan shafi da wannan kwarewa mai girma, to ku dubi rayuwar Amirul Muminin (a.s). A lokacin da ya ji cewa wajibi ne ya yi watsi da wani abu, hakan ya yi kamar jefar da kwallon dabino daga baki. A lokacin da yake jin cewa akwai nauyi a kansa - saboda nauyin da ke kai ba wai don wani ba - ya tafi nemansa sannan kuma ya amince da shi. Ya ji cewa nauyi ne a kansa. Saboda kare addini da fada da makiya addini ya sanya ya gudanar da kusan dukkanin lokacin halifancinsa cikin yake-yake. Idan da a ce batu ne na son zuciya da wani abin zai aikata. Amma lamarin ba son zuciya ba ne. Haka nan lokacin da ya so sadaukar da ransa saboda wannan tafarki da wannan manufa, cikin sauki ya ba da shi.

Abin Koyi Cikin Hukumar Amirul Muminin (A.S)
Hukumar Amirul Muminin (a.s) a fagen tsayar da adalci, ba da kariya ga wadanda ake zalunta, fada da zalunci da goyon bayan gaskiya cikin kowane irin yanayi abin koyi ne wanda wajibi ne mu yi koyi da ita. Ba lamari ne da ya tsufa ba, a dukkan yanayi na ilimi da zamantakewa na duniya za ta iya zama abin koyi ne domin samun jin dadi da kuma sa'adar bil'adama. Mu ba muna so ne mu yi koyi da irin tsarin gudanarwa na wancan lokacin ba ne mu ce sun hada da irin sauye-sauye na zamani da aka samu. Abin da muke cewa shi ne a yi koyi da hanyar gudanar da ayyuka na wancar hukumar wadanda har karshen duniya suna raye. (a matsayin misali) kare wadanda aka zalunta har abada lamari ne dake raye. Rashin zama inuwa guda tare da azzalumi, rashin karbar rashawa wajen rufe gaskiya, dukkan wadannan abubuwa ne da babu wani lokaci da za a ce sun tsufa. A lokuta da yanayi daban-daban wadannan abubuwa har abada abubuwa ne masu kima. Wajibi ne mu nemi wadannan abubuwa; wadannan su ne asasi.

A kan wannan ne masu takama da karfi a duniya suke jin haushi. Suna cewa me ya sa Iran take goyon bayan al'ummar Palastinu da ake zalunta ko kuma mutanen Afghanistan ko kuma me ya sa ba sa tafiya daidai da wancan gwamnati wacce ta zalunci ce. Yadda kuke ganin kalmar 'yan mazan jiya take yawo a bakin makiyan wannan al'umma a matsayin abin muzgunawa saboda hakan ne. Saboda wadannan asasai su ne suke damun wadannan azzalumai masu amfani da karfi na duniya, don haka suke adawa da su. A wancan lokacin ma saboda wadannan abubuwa ne suka yaki Amirul Muminin (a.s). wajibi ne dukkan kokarinmu a matsayin gwamnati ya zamanto kan wannan....
....shi kansa wanda yake tamkar mutumin da ya fi sauran mutane fakirci yana cewa: Ni din nan da nake a matsayin shugabanku, haka nake rayuwa. Ya gaya wa Usman bin Hunaif cewa: Kai din nan ba za ka iya irin wannan rayuwar tawa ba, wato ba a ma sa ran hakan "To sai dai ku taimaka mini da tsoron Allah da kokari". Wadannan su ne abubuwan da Amirul Muminin (a.s) yake bukata daga wajenmu. Ku nesanci duk wani abin da ya ke sabo ne kuma zunubi ne sannan kuma ku yi iyakacin kokarinku wajen nesantarsa, iyakacin iyawanku...
A wajen Amirul Muminin (a.s) yin adalci da kare wadanda aka zalunta da tsanani ga azzalumi - ko da kuwa wane ne shi; wato azzalumi ko wane ne shi haka nan wanda aka zalunta ko wane ne shi - lamari ne mai muhimmanci. Amirul Muminin (a.s) yayin ba da kariya ga wadanda aka zalunta bai sanya sharadin Musulunci ba. Wannan Amirul Muminin din wanda ya kasance mai riko da Musulunci, wannan mumini mai daraja ta farko, wannan babban jarumin yake-yaken Musulunci, to amma bai sanya sharadin Musulunci ba wajen kare wadanda aka zalunta....
Yayin da muke girmama sunan Amirul Muminin (a.s), wajibi ne mu daura damarar aiki. Mu ba za mu iya ce wa mutane ku yi aiki tamkar Amirul Muminin (a.s) ba. Mu din nan da a yau muke rike da mukamai a tsarin jamhuriyar Musulunci, muna da mafi girman nauyi a wuyanmu. Ina fatan jami'an jamhuriyar Musulunci za su sami wannan dacewa tamkar Amirul Muminin (a.s) wajen bin wannan tafarki, mu kama tafarkin wannan babban bawan Allah. Ko da yake Amirul Muminin (a.s) ya sha wahalhalu masu tsanani a wannan tafarki.....A cikin sananniyar addu'ar nan ta Kumail - wacce insha'i ce ta wannan mai girma - yana magana da Allah Madaukakin Sarki cewa: "Ya Ubangijina da Shugabana da kuma Mamallakin 'yancina...(hakikanin gaskiya wadannan suna daga cikin abubuwan da suke janyo hankalina sosai): "Ya Wanda gare Shi nake kai kukan halayen da nake ciki" yana mika kukansa ga Allah, zuciyarsa cike take da cutarwa. Damuwar Amirul Muminin (a.s) ta ginu kan yanayin da mutane suke ciki da kuma makomar addini da matsayar addini a wannan jaririn tsari na Musulunci na wancan lokacin da kuma irin nauyin da yake jin yana kansa. Ko da yake Amirul Muminin (a.s) ba ya rufe ido kan kashi daya cikin dari na wannan nauyi.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din