Pair of Vintage Old School Fru
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hakikanin Sakon Aiko Manzon Allah (s.a.w.a)

Ali Khamenei5

Tunawa da ranar aiko Ma'aiki (s.a.w.a), kafin ya zamanto girmama wani abu na tarihi, gabatar da manyan darussan aiko Manzon Allah (s.a.w.a) ne wanda a yau dukkanin bil'adama - musamman al'ummar musulmi - suke bukatarsu. A yau bil'adama suna fuskantar matsaloli da wahalhalu daga dawagitan duniya da suka hada da zalunci, nuna wariya, fasadi da mulkin mallakar wasu ‘yan tsiraru. A yau rayuwar bil'adama, tana hannun wasu mutane ne wadanda ba su shaki kamshin imani ba kuma wadanda soyace-soyacen zuciya ne yake iko da su. A yau bil'adama suna bukatar sakon aiko Ma'aiki (s.a.w.a) sama da kowane lokaci.
A matakin farko, aiko Manzon Allah (s.a.w.a), kira ne zuwa ga tauhidi (kadaita Ubangiji). Tauhidi ba wata nazariyya ta falsafa ba ce, face dai wata hanya ce ta rayuwa ga bil'adama. Sanya Ubangiji ya zamanto mai iko cikin rayuwa da kuma katse tasirin wasu abubuwa daban-daban masu iko a cikin rayuwar mutum. "La'ilaha Illallah" (Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah) wanda shi ne asalin sakon manzonmu da kuma dukkanin Annabawa yana nufin cewa bai kamata dawagitan duniya da shaidanu su yi tasiri a cikin rayuwa da tafarkin mutum wajen zabar tafarkin rayuwarsa ba sannan kuma su sanya rayuwarsa ta zamanto karkashin ikon soyace-soyacen zukatansu ba. Idan har tauhidi da wannan ma'ana tasa wanda Musulunci ya fassara sannan kuma dukkanin Annabawa suka kasance masu dauke da wannan sakon, to idan ya sami gindin zama a cikin rayuwar al'ummar musulmi da sauran al'ummomi, to kuwa dan'adam zai samu sa'ada ta hakika ta duniya da lahira, sannan kuma rayuwar bi'adama za ta kyautatu; duniya kuma za ta kasance cikin yanayin da zai sa mutum ya kai ga kamala da daukaka na hakika. A mahangar Musulunci duniya wata hanya ce ta zuwa lahira. Musulunci ba ya kore duniya; ba ya ganin ababen jin dadin duniya a matsayin ababen kyama; yana ma kiran dan'adam ne da ya ba da himma wajen gudanar da ayyukansa a fagen rayuwarsa; sai dai wajibi ne dukkanin wadannan abubuwa su zamanto domin bada karfin guiwa da kuma kyautata imanin mutum ta yadda rayuwa za ta zamanto mai kyau da dadi a wannan duniya. A irin wannan duniyar, zalunci da jahilci da nuna fin karfi ba su da matsuguni. Hakan aiki ne mai wahalan gaske da yake bukatar kokari, wannan jihadi (kokari) Manzon Allah (s.a.w.a) ne ya fara shi tun ranar farko na aiko shi.
Abin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya kira (mutane) zuwa gare shi, su ne wadannan abubuwan da tsawon tarihin rayuwa, dan'adam yake bukatarsu. Annabi (s.a.w.a) ya kirayi mutane ne zuwa ga ilimi. Ayar farko ta Alkur'ani mai girma ta girmama matsayin ilimi ne: "Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. Ya halitta mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka Shi ne Mafi karimci. Wanda Ya sanar (da mutum) da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba"(Suratul Alak 96: 1-4). Tun farko ya gabatar da batun koyarwa ne. Ilimi, hanya ce ta samun ceto da shiryar da mutum. Hakan bai ta'allaka da wani zamani ko wani bigire ba, yana da alaka ne da dukkan lokacin rayuwar mutum. Manzon Allah (s.a.w.a) ya kirayi mutane ne zuwa ga yunkuri da tsayuwa kyam. Allah Madaukakin Sarki cikin ayoyin farko-farko da ya sauko wa Annabi (s.a.w.a) Yana cewa: "Ka tashi domin ka yi gargadi"(Suratul Muddatthir 74:2). Wato tsayawa, yunkuri, fita daga yanayin zama kawai da tsayawa waje guda da kuma jin nauyin da ake dauke da shi. "Ka ce, ‘Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! Wato ku tsayu domin Allah..."(Suratus Saba 34:46). Tsayuwa da yunkuri domin Allah lamari ne mai amfanarwa a dukkanin yanayi na rayuwa. Ba tare da tsayuwa ba babu abin da za a iya, sannan kuma ba za a cimma ko da daya daga cikin manufofi na koli ba.
Manzon Allah (s.a.w.a) ya kirayi mutane zuwa ga tsarkake kai da zuciya da kuma tarbiyya: "Shi ne Wanda Ya aiko manzo daga cikin ummayai (wadanda ba su rubutu ba su karatu ) yana karanta ayoyi a gare su, yana tsarkake su yana sanar da su Littafi da hikima"(Suratul Juma'a 62:2). Tsarkake zuciya shi ne sharadi na farko. Ba tare da tsarkin zuciya ba, to ilimi ma ya kan zama wani makami wajen yada fasadi da bata da kaucewa hanya na mutum; kamar yadda kuke gani a yau a duniya ilimi ya zamanto wani makami na faduwar ‘yan'adam, ana amfani da ilimi wajen cutar da al'ummomi da take hakkokin bil'adama da sanya al'ummomi cikin tsananin yunwa. Allah kadai ya san yawan mutanen da suke a kusurwowi daban-daban na duniya da aka danne da kuma shimfida iko a kansu saboda amfani da makamin ilimi da ‘yan mulkin mallaka suka yi, aka kuma haramta musu ababen da rayuwa take bukata, suna kuma rayuwa cikin talauci, rashin matsuguni da wahalhalu. A yau ma haka lamarin yake. A yau ma'abota girman kan duniya - sabon mulkin mallakan duniya - ta hanyar dogaro da ilimi da amfani da shi a matsayin makami sun jefa mutane cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, suka sa su cikin yanayin wahala suna fuskantar mutuwa da karewa. Wannan shi ne sakamakon ilimin da ba ya tare da tsarkin zuciya.
Musulunci yana kiran mutane ne zuwa ga ‘yan'uwantaka, yana daukar mutane a matsayin abu daya; ba ya nuna wariya a tsakaninsu, kabila ba ta zama dalilin fifikon mutane akan wasu, ba ta daukaka wata al'umma a kan wata. Musulunci yana kira ne zuwa ga girmama masu tsoron Allah. Mizanin fifiko shi ne tsoron Allah (takawa). Takawa tana nufin kula da halaye, sanya ido kan iyakokin Allah da yi wa rayuwa tsari. Dukkan wadannan abubuwa ba su takaita ga wani zamani ba, dan'adama na yau ma yana bukatar hakan. Duk yadda ilimi da wayewar mutum za su karu, to wadannan abubuwan ne dai za su ba shi sa'ada. Wajibi ne al'ummar musulmi su kula da wadannan abubuwa, su kuma yi kokari domin kaiwa gare su. Wadannan abubuwa suna da bukatar nufi da azama mai karfi tsakanin al'ummomin musulmi da jami'ai da shugabannin kasashe - wato mutanen da suke rike da madafun iko a kasashe -.
Ya zo cikin addu'ar da aka ruwaito ta wannan rana cewa: ‘Na san cewa mafi girma da daukakan guzurin mai tafiya zuwa gare Ka (shi ne) azama da irada ga wanda ya zabe ka". Koda yake akwai wahalhalu cikin wannan hanya; amma tare da azama da tsayin dakar mutum ya kan zama mai sauki. Wadannan abubuwa ne da Musulunci ya koya mana. A duk inda muka kwatanta hakan cikin rayuwarmu, mun gansu a aikace. Wato yau da gobe sun tabbatar da hakan.
A farko-farkon Musulunci, wata al'umma wacce take nesa da wayewa da ilimi kuma wacce ba ta da duk wani abu na kyautata rayuwa, amma sakamakon albarkacin wadannan ka'idoji da kuma riko da wannan karfafaffen tushe sun yi nasarar samar da ci gaba mafi girma a tsawon karnuka a duniya kuma duniya ta amfana daga irin wannan ilimi da ci gaban da su ke da shi. Wannan shi ne abin da yau da gobe ta koya mana a baya. A yau ma mu a Jamhuriyar Musulunci a duk inda muka yi amfani da nufinmu da dogaro ga Allah, sannan kuma a duk inda muka yi amfani da irin karfin da muke da shi da watsi da son zukatanmu da kuma fahimtar manyan manufofin da muke da su, to lalle mun yi nasara.
A fili yake cewa gina al'umma da samar da ci gaba - suna daga cikin manyan manufofin Musulunci - ba tare da nuna kiyayya ba ba abu ne mai yiyuwa ba. A farko-farkon Musulunci ma an nuna kiyayya da kafa tsari da al'umma; a yau ma haka lamarin yake. A yau a duniyar musulmi, al'ummar musulmi sun sake jin daudakar Musulunci a tare da su, kuma saboda Musulunci suna jin daukaka da girma. Wayewa da farkawa ta Musulunci lamari ne na hakika da aka samar da shi, ko makiya al'ummar musulmi sun so hakan ko kuma ba su so ba. Ci gaba da tafiya akan wannan tafarki yana bukatar azama mai karfi daga jami'an gwamnatoci....
Wajibi ne mu kula da kawukanmu kada mu zame; mu lura kada kyale-kyalen duniya su yaudaremu, kuma kada mu fada cikin yaudarar makiya kada kuma mu bari farfagandarsu ta yi tasiri a kanmu. Wajibi ne mu ci gaba da karfafa hadin kan da ke tsakaninmu a kowace rana sannan kuma mu nesanci damuwa da ababe na gefe. A yau batu na asasi, shi ne kiyaye siffar jamhuriyar Musulunci da wannan kasa. Duniyar musulmi da al'ummar musulmi sun zuba idanunsu akan wannan; Kun yi nasarar nunawa duniya wani kyakkyawan misali (da ku ka kafa.); abin da makiya suke so shi ne rusa wannan kyakkyawan abin koyin. Rusa Iran ba shi ne manufa ba; abin nufi shi ne ruguza duniyar musulmi.
Ana iya binciko sakon aiko Ma'aiki (s.a.w.a) cikin Alkur'ani da sauran fitattun bangarori. A nan zan yi ishara ne da wasu sassa biyu na wannan sako mai girma ta yadda za ku ga irin muhimmancin da yake da shi ga mu musulmi sannan kuma ta yadda ya tsara mana wani tsari da kuma bude mana hanya:
Na farko shi ne cewa wannan sako wanda aka yi ishara da shi cikin wata aya daga cikin ayoyin Alkur'ani. Daga cikin wadannan ayoyi akwai cewa: "Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Littafi ne da mu ka saukar da shi zuwa gare ka domin ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske.."(Suratu Ibrahim :1). Sako ne na ficewa daga cikin duhu zuwa ga haske. Haske da duhu ba abubuwa ne da a bangarori daban-daban za su zamanto abin da mutum zai yi kuskure kansu ba.
Addinin Musulunci da sakon aiko Ma'aiki (s.a.w.a) suna fitar da mutum ne daga duhun jahilci, duhun munanan dabi'u, munanan halaye, fitina tsakanin bil'adama, camfe-camfen da suke iko da tunani da kwakwalan mutane, wadanda suke zama shamaki ga mutane da kawar da su daga mikakken tafarki, duhun zalunci da girman kai - dukkan wadannan abubuwa duhu ne - sannan kuma su shiryar da shi zuwa ga hasken da ya ke kalubalantar wannan.A cikin ayoyi da dama na Alkur'ani mai girma an yi ishara da wannan ma'ana tare da maimaitawa; wato samar da wani sauyi ne cikin rayuwar dan'adam a bangaren zamantakewa, da bangaren zabar manufa, a kuma bangaren rayuwar daidaiku; da kuma dukkan fuskoki.
Wani batu kuma mai muhimmanci shi ne akan kyawawan dabi'u da tsarkake zukata, wadanda su ma an yi magana kansu cikin ayoyi da dama na Alkur'ani da kuma maimaitawa su cikin hadisin annabi wanda kuma ya ke a cikin littatafan dukkan kungiyoyin musulumi da ya ke cewa: "An aiko ni don in cika kyawawan dabi'u" (Mir'at al-Ukul, juzu'i na 7, shafi na 347)

Ranar Aiko Ma'aiki, Rana Ce Ta Haihuwar Mafi Girma Da Daukakar Ma'anoni Da Ababe Masu Kima
Ranar ‘aiko Ma'aiki', a hakikanin gaskiya rana ce mafi girma cikin tarihin bil'adama. Rana ce ta haihuwar mafi girma da daukakan ma'anoni da ababe masu tsarki. Aiko Annabi mai girma (amincin Allah ya tabbata a gare shi) wani yunkuri a aikace ne na kai daidaikun mutane zuwa ga matsayi na kamala da na ruhi da imani a bangare guda, a bangare guda kuma zuwa ga daukaka ta rayuwa ta al'umma da gyara yanayin rayuwar al'umma.
Yadda lamarin ya ke shi ne cewa, kyautar da aka baiwa mutane a cikin aiko manzo ba ta takaita a cikin wasu busassun ma'anoni ba da ba su nuni da hanyoyin da za'a bi, kuma babu wani wanda ya ke a matsayin mai yi wa mutane jagora. Tun a matakin farko, manufar da take tattare da sakon aiko Ma'aiki ta yi tasiri a cikin rayuwar shi kansa wannan ma'abocin girman (Annabi) sannan kuma cikin ruhi da rayuka da ayyukan wadanda suka yi imani da wannan sako. Sannan kuma tun a wannan matakin farkon ne jahiliyya ta sha kashi a hannun wannan sakon da kuma yin fito na fito da ita. Wannan shi ne abin da aiko Annabawa ya kebanta da shi.

Hakan kuwa bai takaita da annabcin cikamakin annabawa ba (s.a.w.a). Annabawa suna yunkurawa sannan kuma abin da suke karantar da mutane da shiryar da su ana ganinsa cikin ayyukansu. Su ne na farko da suke fara bin wannan tafarki...

Albarkatun Aiko Ma'aiki (s.a.w.a)
Kafa al'ummar musulmi da irin wadannan siffofi da suka kebanta da wannan mutum, daya ne daga cikin albarkatun da wannan aike mai girma ya ke da shi. Al'ummar musulmi ba ta takaita kawai a cikin cewa wani gungun mutane ba ne da suka hadu a kan wata akida, su musulmi - kamar yadda Annabin Musulunci mafi girma da kuma koyarwar Alkur'ani suka zama masu tsara musu rayuwa - to kuma al'ummar musulmi sun kasance wani gungu ne na mutane ma'abota ilimi da kyawawan halaye da hikima da kyakkyawar alaka da kuma haduwa wacce take tattare da adalci wanda sakamakon dukkan wadannan shi ne isar mutum ga kamala ta koli wanda dama Ubangiji ya halicce shi da wannan damar. Al'ummar musulunci wani hoto ne na tarbiyyyar Musulunci; Annabin Musulunci mafi girma ya fara yi musu wannan tarbiyyar ne daga tushe cikin matsaloli.
A wancan ranar da kira zuwa ga tauhidi ya fito daga bakin Annabin Musulunci mai tsarki bayan aiko shi, duniya - da dukkan bangarorinta - ta kasance duniya ce ta kafirci da zalunci wacce ta yi nisa daga dukkanin kyawawan dabi'u da fadawar dan'adam cikin nau'oi daban-daban na matsaloli da fasadi. Wannan gagarumin yunkuri na Ma'aiki (s.a.w.a) ya faru ne a cikin wani yanayi da yai kama da mu'ujiza cikin tsawon shekaru goma sha uku, bayan wadannan shekaru goma sha uku ne aka dasa tushen al'ummar musulmi a garin Madina.
Dalilin da za mu iya sani wanda ya haddasa gagarumin sauyi a cikin wannan karamar cibiya da mai da ita ta zama al'ummar musulmi a karni na hudu da kuma biyar na hijira shi ne bayanannen imani, koyarwar da take a fili wacce ta shafi kowane bangare, tsayayyar azama da jihadi da aka ci gaba da yi; wadannan su ne abubuwan da suka sauya wata karamar al'umma ta dubban mutane a Madina a shekarun farko-farko na hijira zuwa ga gagarumar al'umma, tsayayya ma'abociyar sani da ilimi a karni na hudu zuwa biyar hijiriyya wanda tarihi ya yi mana bayaninsa.

Gafala Daga Koyarwa, Dalilin Shan Kashi Da Koma Bayan Al'ummar Musulmi
Al'ummar musulmi a lokuta daban-daban a duk lokacin da ta yi watsi da kuma gafala da wadannan koyarwa (ta Musulunci) to ta sha kashi da fuskantar koma baya. A duk inda al'ummar musulmi ta yi sakaci da ilimi, kyawawan dabi'u, kyakkyawar alaka ta zamantakewa, tsayin daka, daukaka, hadin kai da kuma uwa uba aiwatar da adalci, to kuwa ci gabanta ya kan tsaya da kuma fuskantar koma baya. Yanayin ya kan kai ga yadda makiya da masu hadama da wuce gona da iri za su sami damar yagalgala wannan al'umma, da raunana karfinta da samun iko a kanta da kuma washe albarkatun da take da su.
A wannan zamani da muke ciki tun daga gomomin shekarun da suka gabata zuwa yau sakamakon wadannan koyarwa da riko da su, farkawar Musulunci ta fara sannan kuma aka sake daga tutar tauhidi sama wanda kolin wannan farkawa shi ne kafa gwamnatin jamhuriyar Musulunci a wannan yanki mai tsananin muhimmanci na duniyar musulmi wanda ya dawo wa dukkanin musulmi jin daukaka da mutunci. A yau ma muna fuskantar irin yanayin da al'ummar musulmi suka fuskanta a karnukan da aka sami koma baya da kuma gushewa. A yau ma an kaddamar da yaki a kan al'ummar musulmi don raunana karfin wannan jaririn yunkuri. A yau ma masu takama da karfi da girman kai da shan jinin al'umma sun fito da maitarsu a fili a kan dimbin albarkatun karkashin kasa da na mutane da duniyar musulmi take da shi - kamar yadda su da kansu suke fadi - sun shelanta yaki suna masu fakewa da tutar demokradiyya da tutar ‘yanci; amma hakikanin lamarin wani abu ne na daban. Hakikanin lamarin shi ne ruguza ababen da suke tabbatar da daukakar al'umma musulmi - wato Musulunci - ne. Hakikanin lamarin shi ne ruguza tushen gwagwarmaya ta yadda babu wani abin da zai hana wadannan mashaya jini zama a wannan yanki.

Musulunci, Magani Ne Na Dukkan Zamunna
Yayin da muke karanta wannan aya ta Alkur'ani cewa:"Shi ne Wanda Ya aika, a cikin ummiyai, wani Manzo daga gare su yana karanta ayoyinSa a kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar da su Littafi da hikimarsa..."(Suratul Juma'a 62: 2) hakan ba yana nufin cewa da zuwan addinin karshe da Manzon karshe shi kenan zukatan dukkanin mutane za su tsarkaka ba ne ko kuma sun tsarkaka ba ne; ba wai yana nufin bayan bayyanar Alkur'ani shi kenan mutane za su yi watsi da zalunci da nuna bambanci da bata su kama tafarkin kamala ba ne. Haka nan idan muka ce Annabi da addinin Musulunci sun zo don tabbatar da adalci da ‘yantar da raunana da kawar da gumaka masu rai da marasa rai ne, hakan ba yana nufin kenan bayan bayyanar wannan haske shi kenan mutane ba za su yi zalunci ba; ba za a sake samun dagutu ba sannan kuma ba za a samu gumaka wadanda za su doru a kan rayuwar mutane ba ne. Hakikanin lamari ma yana tabbatar da cewa bayan bayyanar Musulunci, a cikin wasu wurare na duniya, hatta a duniyar musulmi - ko da yake bayan gushewar wasu shekaru - an samu gumaka, an samu dawagitai, an zalunci bil'adama da kuma koma bayan da ya ci dunun dan'adam, dukkan wadannan abubuwa za a sake ganinsu cikin rayuwar mutane.
Don haka, ma'anar cewa manufar aiko Ma'aiki ita ce ceto dan'adam wani abu ne na daban. Ma'anarsa ita ce cewa abin da Annabi da Musulunci suka gabatar da su ga mutane wani magani ne na dukkan zamunna. Magani na fuskantar jahilcin mutum, na fuskantar hana tsayuwar zalunci, domin fuskantar nuna bambanci, fuskantar mika masu rauni ga masu karfi da kuma fuskantar matsalolin da bil'adama suke fuskanta tun farkon halitta. Tamkar sauran magunguna, matukar aka yi aiki da su, to kuwa za a ga sakamako. Idan kuma aka yi watsi da su ko kuma aka yi musu mummunar fahimta ko kuma babu jaruntar fuskantar hakan to kuwa zai zamanto tamkar babu shi ne. Idan likitocin da suka fi kwarewa suka rubuta wa mutum magani amma sai mutum ya gagara karanta takardar maganin ko kuma mutum ya karanta bisa kuskure ko kuma ya ki aiki da abin da aka rubuta din ya yi watsi da shi, wani abu ne zai sami mara lafiya sannan kuma mene ne laifin shi wannan kwararren likitan?
A cikin littafin Nahjul Balagah akwai wadansu kalmomi da jumloli da suke magana kan yanayin da ake ciki lokacin bayyanar Musulunci da aiko Ma'aiki (s.a.w.a). Daga cikinsu akwai: " Hasken duniya ya dushe kuma jiji da kanta ya bayyana." ko kuma fadinsa a wani wajen: " Suna a cikin fitina da ta take su da kafafunta, ta kuma dannesu da faratanta." A duk lokacin da mutane suka kasance a cikin fitina, to ‘yan'adamtaka za ta fuskanci matsaloli da kuma shiga tsaka mai wuya, a duk lokacin da mutum bai zama mai tsarkin zuciya ba to zalunci zai tabbata ya kuma zama mai iko, masu takama da karfi kuma su rika nunawa raunana fin karfi, da kuma kashe-kashe tsakanin ‘yan'uwa. Halaye za su gurbata. A cikin wannan rana ne ya zama wajibi a yi aiki da wannan magani. Ba zai taba tsufa ya lalace ba.....

Yanayi Da Siffofin Lokacin Jahiliyya
Aiko Annabin Musulunci (s.a.w.a) mafari ne na sabuwar hanya mai haske ga bil'adama. Duniyar da take kewaye da wannan sako da wajen da sakon ya bayyana, wata mummunar duniya ce wacce ba za a iya jure mata ba. Duniya ce ta son abin duniya, duniya ce irin ta dabbobi, duniya ce da babu jin kai a cikinta, duniya da ma'abota nuna karfi da girman kai suke baza kolinsu, duniya ce ta nuna bambanci da yada fasadi da zalunci da sha'awar da ba ta da linzami. Wadanann siffofi ba su kebanta da yankin Hijaz kawai ba; su kansu wadannan manyan dauloli da suka kewaye yankin Hijaz - wato kasar Iran ta Sasaniyawa da daular Rumawa - suna da irin wadannan matsaloli.
Irin jahiliyyar lokacin bayyanar Musulunci, wacce ta sanya rayuwar mutane cikin yanayin tsanani da matsin lamba, jahiliyya ce da ta kame ko ina. A wancan lokacin, akwai fitinar nuna karfi da zalunci a dukkan yankunan da suke kewaye da yankin Hijaz. Akwai ilimi da ci gaba - gwagwardon irin na wancan zamanin, haka nan tsari da shirye-shirye na hukumomin sarakuna akwai su, haka nan akwai tarbiyya da suka samo asali daga irin karfi da ake da shi a wadannan kasashe. Amma abin da babu shi ne hasken ‘yan'adamtaka da mutunci. Abin da babu shi ne dai wannan abin da dan'adam yake bukatarsa, wato yanayi na daukaka da mutuncin dan'adam, yanayi na rahama da mutumci da adalci. Abin da mutanen wancan lokacin suka rasa shi ne adalci. Wato yanayin da mai rauni ba zai zai wulakanta a hannun mai karfi ba, wato kada albarkatun kasa da ake da su su zamanto a hannun wasu 'yan tsirarru kawai masu karfi sannan sauran mutane kuma su kasance cikin yanayi talauci da rashi. Wadannan su ne manyan abubuwa da suke ci wa dan'adam tuwo a kwarya. Irin wannan yanayi ne ya kasance a karkashin hukumar Sasaniyawa. Shi ne kuma yanayin da ya kasance a karkashin daular Rumawa; sai dai kowane daya daga cikin ta wani salo. A Hijaz ma wacce a wancan lokacin ake rayuwa irin ta 'yan kauye, lamarin ya kasance ta wani salo daban. A irin wannan yanayi ne Musulunci ya bayyana. To amma wannan sako ba na wancan lokacin ne kawai ba, na dukkanin bil'adama ne. "Bai kasance ba face tunatarwa ga dukkan talikai"(Suratu Sad: 87). Ta haka Manzon Allah (s.a.w.a) ya iya tsayawa kyam wajen fuskantar wannan yanayi mai daci sannan kuma ya kawo karshensa. Manzon Allah (s.a.w.a) ya sami nasarar haifar da gagarumi gibi cikin katangar rashin adalci da sauran bala'in da suke fuskantar bil'adama. Ya rusa wasu daga cikinsu wasu ya yi musu raunin da za su rushe a kowane lokaci. Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci mafi wahalan yanayi. A lokacin da munanan ayyuka da fasadi suka sami daurin gindin iko da makami da nufi da siyasa, to hakan gagarumin hatsari ne ga bil'adama.
A yau mutanen karni na ashirin da daya tare da dukkanin abubuwa da suke riyawa cewa suna da shi, sakamakon wasu rauni da ake da su, sun doshi hanyar da ma'abota karfi na duniya ko kuma wani gungu na masu takama da karfi wadanda suke takama da kwanji da makaman da suke da su, suke kuma baiwa kansu gaskiya a kan abin da suke yi, gaskiyar da babu ita. Wannan shi ne irin yanayin da ake ciki a lokacin da aka aiko Ma'aiki (s.a.w.a). Manzon Allah (s.a.w.a) ya tsaya kyam; bai ce tun da wannan wani lamari ne da ake da shi a kas wanda babu yadda za'a yi da shi. Wasu masu rauni da rashin himma suna fakewa da haka suna fadin cewa: Wannan wata hakika ce a kasa me za mu iya yi? Wannan ba shi ne yanayin da ya ke wajibi a mika kai gare shi ba. Yanayi na dabi'a, yanayin da ba za a iya maganinsa ba, yanayin da ba an tilasta shi ne a kan mutum ba, su ne yanayin da wajibi ne mutum ya hakura da su ya yi kokarin tafiya tare da su. Amma yanayin da wasu mutane suka tilasta su akan wasu ta dogaro da tsinin mashi da karfi, dole ne a hargitsa su. Lalle ya saba wa hankali mu ce ma'abota girman kai na yau wani yanayi ne da babu yadda za mu iya da shi. Ai wannan wani lamari ne da aka tilasta mana shi. Manyan mutane, saukakkun addinai da manyan ma'abota tunani sun tsaya kyam a gabansu, sun fuskance su don su sauya su, kuma abu ne da za'a iya sauyawa. Wannan shi ne hakikanin sakon aiko Ma'aiki. Ranar da wannan sako ya shigo fagen garin Makka, cewa ya yi: "Ku ce La'ilaha illallah ku samu rabo"
Idan har mutum ma'abocin adalci ne ba zai iya bugun kirji ya yi tsammanin cewa wata rana wadannan kalmomi za su yi nasara ba, Saboda babu ma yanayin yiyuwar hakan. Irin manyan gumakan da aka sanya su a jikin katangun (dakin) Ka'aba, ga kuma masu kare wadannan gumaka, ga kuma masu bakin kishin kabilanci na jahiliyya da kuma manyan garin Makka da iyalansu, amma a yi tunanin kalmar 'Lailaha illallah' za ta iya gamawa da dukkan wadannan abubuwa sannan kuma a gefensu ga manyan dauloli na Sasaniyawa da daular Rom. Shin akwai wanda zai iya bugun kirji ya kuma karbi cewa a matakin farko ana iya gabatar da wannan sakon da kuma ci gaba da yinsa? Mutane masu rauni tun da farko ma za su ja da baya. Amma nauyi da sako da annabci, sun sanya Annabi ya ci gaba da wannan sako. Aike yana nufin farfadowa, kuma wannan aiken ya zo a matakin farko ya sauya yanayin Hijaz, daga baya kuma ya sauya dukkanin duniyar da ta ci gaba a wancan lokacin cikin shekaru ashirin da wani abu.
Ba a wuce rabin karni da bayyanar Musulunci da sakon aiko Ma'aiki ba sai ga shi sama da rabin duniyar da ta ci gaba a wancan lokacin tana karkashin tasirin Musulunci. Kada ku taba tsammanin manyan hukumoki kamar dauloli masu karfi ba su da ilimi da hankali da tsari da dakaru da hanyoyin farfaganda da girman kai da jiji da kai; me yasa (suna da shi). To amma idan bayyanannen imani wanda ya dogara da hujja mai karfi ta hankali, idan ya shiga cikin zukatan mutane ya kuma hadu da himma da kyakkyawar niyya da sadaukarwa, to za su iya kawar da dukkan wannan cikas din. A yau ma haka lamarin yake: imani na Musulunci, imanin da ya ginu bisa hankali da kuma hujjoji wanda kuma ya kumshi alheri da sa'ada ga bil'adama...makaranta ta Musulunci, makaranta ce ta bada kariya ga ‘yan'adamtaka da abubuwa masu kima na ‘yan'adamtaka; makaranta ce ta yada tausayi da mutuntaka; makaranta ce ta kwadaitar da 'yan'uwantaka a tsakanin mutane; makaranta ce da wadannan ne ka'idojinta a cikin hakkokin zamantakewa" "Babu wata al'umma da za zama mai kima matukar ba'a karbarwa mai rauni hakkinsa daga mai karfi ba tare da ya wahala ba." Idan aka sami wata al'umma wacce wani daga cikin 'ya'yanta maras karfi zai iya karban hakkinsa daga wajen wani mai karfi - mai son amfani da karfi da tursasawa - ba tare da wata matsala ba, to wannan shi ne sakon Musulunci. Wannan al'umma ta Musulunci ce; a yau wannan sako shi ne yake janyo hankula al'ummomi. A ina ne a duniyarmu ta yau ake samun hakan? Wane tsarin demokradiyya, wane tsarin demokaradiyya mai sassauci ne, wani ikirari na kare hakkokin bil'adama a yau zai iya gabatar da wannan sannan kuma ya yi yunkurin tabbatar da shi? A yau sabanin hakan ake aiwatarwa.
A yau ma Musulunci yana da wannan rayayyen sako wanda ya ginu bisa karfafaffiyar hikima. Musulunci ya nuna irin karfin da yake da shi, a kasar Musulunci ta Iran ya nuna kansa, a wurare daban-daban a wannan yankin ya nuna kansa.

Nauyin Dake Kanmu Dangane Da Yaduwar Musulunci Da Al'adun Musulunci
Ko shakka babu daya daga cikin abubuwan da ke tabbatar da ci gaban Musulunci shi ne dogaro ga Allah da dokokin Ubangiji: "Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga wajen Ubangijinsa haka nan muminai, dukkansu sun yi imani da Allah da mala'ikunSa da littatafanSa da ManzanninSa"(Suratul Bakara :285) Shi kansa Annabi da Muminan farko sun yi imani mai zurfi a cikin zukatansu da sakon Musulunci da taken Musulunci, da kuma gaskiyar dake tattare da Musulunci da karfin da Musulunci yake da shi wajen ceto bil'adama. Wannan imani, lamari ne mai muhimmancin gaske. Wani abin na daban alal akalla a saman wannan yunkuri shi ne rashin kula da kai - abin da yake komawa ga shi kansa mutum da ababen duniya wadanda suke komawa ga shi kansa mutum. Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci. Dukkan wadannan abubuwan da suka zo a cikin riwayoyi na (Bihar Al-Anwar, juzu'i na 73, shafi na 113 da kuma Nahjul Balagah (wasika ta 27 da 59; da kuma huduba ta 34) sannan kuma a cikin kalaman Ma'aiki (s.a.w.a) da sauran magabata akan rashin nuna kwadayin duniya da rashin nuna kwadayin kyale-kyalen duniya, wanda ni ma ina yi wa kaina wasiyya da jaddadawa, saboda gagarumin tasirin da wannan batun ya ke da shi ne. Koda yake makiya Musulunci da musulmi masu karkatacciyar fahimta, suna zato ko kuma zun dauka cewa yayin da Musulunci yake magana kan zuhudu (gudun duniya) yana nufin yin watsi da ababen duniya na zahiri ne, alhali lamarin ba haka yake ba, face dai abin nufi shi ne mummunar duniyar abar zargi ita ce ni da ku mu zama mun mai da neman abin duniya ya zama shi ne manufa,wannan shi ne abin da a ke nufi. Wannan shi ne abin da yake ruguza mutum da lalata shi kuma shi ne tushen bala'oi.
Waliyan Allah - mutanen da suka sami nasarar rike wannan tuta hannu biyu sannan kuma suka ci gaba da bin wannan tafarki mai cike da wahalhalu cikin sauki ba tare da nuna gajiyawa ba - su ne mutanen da suka tsallake wannan tarkon. Saboda haka ne cikin addu'ar nan mai cike da ma'ana ta Nudba (Al-Ikbal Sayyid bn Tawus, juzu'i na 1, shafi na 504) inda a farkonta waliyan Allah suke gode wa Allah Madaukakin Sarki kan irin ni'imomin da ya yi musu. Wanda daya daga cikinsu shi ne abin da ya zo cikin farko wannan addu'a, inda yake cewa: " "Bayan ka shardanta musu zuhudu cikin mukaman wannan duniya wulakantatta da ababen kyale-kyalen da ke cikinta". Ka isar da su zuwa ga mafi girma da daukakan matsayi na cika da kamala ta ma'anawiyya, ka ba su wadannan ni'imomi da ba sa gushewa. Ka ba su wadannan ni'imomi, ka zabe su; sai dai ka kafa musu sharadi. Ma'aikin Allah yana matsayi mafi girma da daukaka na samuwar bil'adama. Hakan kuwa ba mai yiyuwa ba ne in ba tare da taimakon Allah ba; ba mai yiyuwa ba ne idan ba tare da share fage na Ubangiji ba. Allah Madaukakin Sarki ya ba da wadannan abubuwa ne bisa wani sharadi "zuhudu cikin mukaman wannan duniya wulakantatta da ababen kyale-kyalen da ke cikinta suka karbi wannan sharadin naka". Na yarda da hakan kuma na yi aiki da shi. Saboda haka ne mutanen irin su Manzon Allah da Amirul Muminin suka bayyana, suka tsaya kyam ba tare da gajiyawa ba. Wadanda kokarinsu baya karewa. Suka dau nauyi a kafadunsu wanda wannan nauyi ba kawai ya kebanta da lokacinsu ba ne; sun samar da wani yunkuri wanda bai kawo karshe da karshen rayuwarsu ba.Wannan yunkuri ya ci gaba.
A yanzu ku duba ku gani, bayan gushewar karnuka goma sha hudu amma har yanzu Musulunci yana ci gaba da haske da haskakawa. Dukkan wadannan abubuwa sun ginu ne bisa wannan samuwa mai girma da kuma wannan kokari. Wadannan su ne abubuwan da za su sanya wannan yunkuri dawwama. Koda yake abubuwan da musulmi da muminai da magabata suka aiwatar a kan wannan tafarki, ya taimaka. Fatan da muke da shi shi ne cewa manyan duniyar musulmi - 'yan siyasarsu da malaman addininsu - kada su sanya manufa da amfaninsu a matakin farko na muhimmanci. Fatan da muke da shi daga wajen mutane da manyan zamaninmu, ba fata ne wanda ayyukan Annabi suka haifar cikin zukatanmu; ina, akwai gagarumar tazara. Mu kanmu wannan shi ne fatan da muke da shi daga gare mu. Haka nan muna da wannan fata daga sauran mutanen da suke duniyar musulmi da kada su sanya manufofin kashin kansu su zamanto kolin manufa, kada su dora su kan komai. Su sanya Musulunci da karfin Musulunci da daukaka da kamalar Musulunci a sama da komai. Idan har aka samu hakan, to ko shakka babu da yanzu wani sashi mai girma na karfin badini da zati na Musulunci ya dawo ga al'ummar musulmi. A nan ma, wannan mutumin da ya iya daukan wannan gagarumin nauyi na lura da imani da nuna kauna da kuma yunkuri na al'umma sannan kuma ya isar da lamurra zuwa wannan wurin da suke a yanzu - wato Imaminmu mai girma - babban abin da ya dogara da shi shi ne ya yi watsi da son kansa sannan ya sanya nauyi a matsayin abin da ya sa a gaba; don haka ya yi nasara. Koda yake akwai wadansu siffofi kuma na daban da yake da su. Wannan shi ne asasin aiki. Mu a nan Jamhuriyar Musulunci cikin wadannan shekaru ashirin, a duk inda muka samu damar gabatar da nauyin da ke kanmu da manufofinmu a gaba, muka yi watsi da kanmu da soyace-soyacen zukatanmu, to mun ci gaba. Amma a duk inda muka aikata akasin haka, to mun ci kasa. A tsawon lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas wadanda suke cikin lamurran da kyau sun san cewa a duk inda ruhin sauke nauyi ya wuce gaba sannan kuma masu rike da madafun mulki suka rage burinsu; to mun ci gaba. Amma a duk inda kwadayi ya wuce gaba, to kuwa shan kashi yana tattare da shi. A yau ma haka lamarin yake...
Tun daga farkon lokaci ya zuwa yau, wadannan makiyan da aka shammata, ba su daina nunawa wannan tsarin kiyayya ba, kuma iyakacin karfinsu sun yi kokarin ganin sun toshe duk wata hanya da za a sake samun irin wannan yunkuri da farkawa a sauran kasashen musulmi; saboda kuwa a yanzu babu irin wannan shammatar da aka yi a baya. A cikin irin wannan yanayi ne wannan tsarin ya samu, wannan gagarumin nauyi ne a wuyanmu.
Nauyi na farko yana wuyanmu ne. Kowane guda daga cikinmu wanda yake da wani nauyi da mukami a gwamnatin Musulunci - nauyi ne na gudanarwa ko kuma na shawara, ko na bincike ko kuma na yin dokoki - wajibi ne dukkanin kokarinmu ya zamanto wajen ganin mun yawaita wadannan ababen da suke tabbatar da karfin da muke da shi cikin tarihin Musulunci sannan kuma mu kwatanta hakan cikin rayuwarmu. Wato shi ne wannan dogaro da Allah, dogaro da abin da muka samu daga Musulunci; da kuma cire son zuciya daga cikin zukatanmu, wato rage bukatu na kashin kai, bukatu irin na kabila da kungiya da jam'iyya ta siyasa. Mu kama hanyar hadin kai na hakika karkashin inuwar dokokin Ubangiji. Wannan hadin kai da sharadinsa shi ne imani guda, kauna guda da manufa guda.
Akwai wadansu abubuwa guda biyu a nan da wajibi a kula da su. Wajibi ne ni da ku, wato gungun mutanen da muke da wani nauyi na shugabanci a kanmu, mu kula da wannan lamari. Wannan abu kuwa shi ne cewa bai kamata mu dauki kanmu a matsayin wani manaja ko shugaba kawai ba, wajibi ne mu dauki kanmu a matsayin masu gabatar da wani sabon tunani ga duniya, wajibi ne mu san kawunanmu kuma bisa hakan ya kamata mu gudanar da ayyukanmu. Haka ya kamata mu yi tafiya, haka ya kamata mu kwatanta ayyukanmu gwargwadon yadda Musulunci ya tsara, sannan kuma mu kiyaye tsarki da ‘yancin wannan tunani.
Wani lamarin kuma ya shafi al'ummar duniya ne. Kafafen watsa labaran ma'abota girman kan duniya suna bayyana jamhuriyar Musulunci (ta Iran) a matsayin mai wuce gona da iri da take kokarin kawar da dukkanin gwamnatocin duniya. To amma lalle lamarin ba haka yake ba. Kowane mutum a duniyan nan yana rayuwa ne gwargwadon yadda yake so. Mu dai abin da muke yi shi ne bayyanar da abubuwan da bil'adama suke bukatarsu. Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana cewa: "Likitan da ya shirya magungunansa sannan kuma ya dumama kayayyakin aikinsa" (Nahjul Balagah, huduba ta 108). Akwai magungunar cututtukan da suke damun bil'adama a yau cikin jakar da muke dauke da ita a bayanmu. Duk wanda ba ya so ba dole ba ne ya dauka. Mu dai ba ma fada da wani. Idan har bil'adama suna fuskantar matsalar rashin matsaya, suna fuskantar matsalar rashin riko da addini, suna fuskantar matsalar rashin girmama al'adun bil'adama, Uba ba ya tausayawa dansa, da ba ya girmama mahaifinsa, basu riko da al'adun baya, basu ganin kimar wani abu idan ba kashin kansu ba, to lalle hakan babbar matsala ce. A yau kasashen yammaci matsalar da suke fuskanta kenan, maganinsa kuwa yana cikin Musulunci ne. A yau dukiyan masu dukiya sai karuwa take yi, kamfanoninsu sukan samu biliyoyin kudade a kowace rana kamar almara, amma a bangare guda kuma akwai wasu mutane da suke kwana a cikin gidan kara da gefen hanya; wadannan suna daga cikin matsalolin kasashen yammaci. Duk da irin dubban wasiyoyi da sanarwar da ake yadawa dangane da batun aure da gina iyali da makamantan haka, amma a kowace rana tushen iyali sai dada rugujewa yake yi a kasashen yammaci; yara maza da mata suna cikin damuwa, su kansu wadanda su ne ummul aba'isin din irin wadannan ayyuka suna cikin damuwa, idan har tushen iyali yana tangal-tangal sannan yara duk suna cikin fushi da damuwa; haka nan yayin da matsaloli na kwakwalwa suka zama ruwan dare, mene ne dalilin hakan? Wadannan kisan kai da ake fama da su mene ne dalilinsu?....a lokacin da bil'adama suke fama da wadannan cututtuka marasa magani, to abin da muke cewa shi ne: maganinsu yana nan, maganinsu shi ne Musulunci. Shi ne sake jaddada sakon aiko Ma'aiki (s.a.w.a) a wannan duniya tamu. A yau ku ne gwarzaye. Al'ummar Iran ita ce gwarzo. Wajibi ne ta yi aiki, wajibi ne a yi wannan aiki tare da dogaro da kai, don kuwa duniya tana bukatarmu.....
Sakonmu sako ne na Musulunci. Daya daga cikin abubuwan da na fadi a baya yana daga cikin ababen da suka tabbatar da yaduwar Musulunci, wato sassauci da tausayi. "Sassauci bai shiga cikin wani abu ba sai ya kawata shi." Tausayi yana nufin saukin hali, ba wai nuna rauni ba. Sassauci ba yana nufi mutum ya bari a taka shi ba ne. Sassauci yana nufi nesantar yanayin rashin ladabi, kyautata mu'amala. Wannan shi ne ma'anar sassauci da rangwame. Ga misali ku shafa wani abu mai karfi kamar karfe, hannuwanku ba za su tabu ba. Wannan shi ne ma'anar sassauci. Tabuwa wacce ta dace shi ne abin da ake nufi da sassauci. Abu ne mai yiyuwa a wani lokacin ka taba wani abin da zai sa ka ji kaikaiyi a hannunka; abin da bai kai karfe karfi ba. Ga misalin katako wanda za'a iya goge shi. A wani lokacin wasu mutanen suna yin maganar da babu gaskiya cikinta magana mai rauni wacce ba ta da ma'ana wanda hakan zai sa kowa da kowa ya fusata. Abu ne kuma mai yiyuwa a sami wani tunani mai cike da ma'ana, wani tunani na gaskiya wani tunani mai karfi ta yadda bayaninsa ya ke da karfi kuwa ya wofinta daga aibu. To haka musulunci ya ke. Haka Alkur'ani ya ke.

Wajibi ne wannan ya zama shi ne darasin aiko Ma'aiki a gare mu ya ku 'yan'uwa maza da mata abin kauna! Wajibi darasin Alkur'ani ya zamanto haka wato mu zamanto mu ne masu kawo sabon zancen, sannan kuma wajibi ne mu kiyaye wannan sabon zancen. "Don ya bayyanar da shi a kan dukkanin addini"(Suratut Tauba 9:33). Ya zo ne don addini ya yi galaba a dabi'ance. A lokacin da rana ta fito idan da za ka kunna kyandir guda dubu ko da wasa ba za a ga haskensu ba. Aiko Ma'aiki, haka yake bayyana da kuma galaba. Wannan tamkar kyandir din ne. Wannan shi ne wannan fitilar. Wannan shi ne mai haskawa. Wajibi ne ku girmama shi. Wajibi ne mu raya batun aiko Ma'aiki cikin rayuwarmu.
Wajibi ne mu nemi taimakon Ubangiji, kuma tabbas Ubangiji zai taimaka.

Karnin Da Muke Ciki, Karni Ne Na Kwarewa Da Aiki
Wajibi ne al'ummar musulmi su dawo ga Musulunci. Tabbas kofar hakan a bude take. Karni da ya wuce - wato karni na sha uku hijiriyya - karni ne na shelanta kalmar Musulunci. Tun daga farkon karnin da Mirza Shirazi - babban marja'in Musulunci - ya fitar da fatawar nan ta fuskantar kamfanonin Ingila wacce ta motsa al'umma, har zuwa batun nan na tsarin mulki a Iran, har zuwa yunkure-yunkuren Musulunci a kasar Indiya, har zuwa farkawar Musulunci da aka samu a yammacin duniyar musulmi - a yankin gabas ta tsakiya da yankin arewacin Afirka - da manyan magabata da suka yi maganganu da irin su Sayyid Jamaluddin da sauransu. A takaice dai karni ne na rera take da gwagwarmaya. Karnin da ya biyo baya kuma karni ne na kwarewa. Wannan karni da muke ciki a yanzu, karni ne na kwarewa. Karni na sha hudu hijiriyya, karni ne na daga murya da wayewa da isar da sako. Sannan wannan karni na sha biyar - tun daga farkonsa - karni ne na kwarewa da aiki.
Muna ganin cewa al'ummomin musulmi sun sami kwarewa sannan suna ci gaba da aiki. Daya daga cikin misalan hakan shi ne jamhuriyar Musulunci, wannan shi ne misali na farko. Saboda mun kasance misalin farko, don haka mun fuskanci matsaloli masu yawa. Wajibi ne musulmi su dau darasi daga wannan kwarewar. Al'ummar da suke son ganin an tabbatar da yunkurin Musulunci a kasarsu, za su iya aiwatar da ayyukan da suka fi cika sama da wanda al'ummar Iran suka aikata da kuma bayyanar da kansu, matukar Allah Ya taimaka sannan kuma suka yi himma.
Musulmi ba su da wata mafita da ta wuce komawa ga Musulunci; (ba su da mafita) in ban da kafa hukumar Musulunci da aiwatar da hukumce-hukumcen Musulunci. Bai kamata a yi tsammanin wani abu mai kyau daga tsohon makiyi wanda zuciyarsa ta ke cike da gaba da Musulunci ba. Fatan juriya ma bai kamata a yi ba. Ku duba ku ga a cikin wadannan shekaru goma sha uku da cin nasarar juyin juya halin Musulunci - cikin wadannan kwanaki muna gudanar da bukukuwan shekaru goma sha uku da kuma shiga shekaru na goma sha hudu - yadda suka cutar da wannan al'umma da kuma abubuwan da suke fadi da abubuwan da suka rubuta da irin mu'amalarsu. Dukkan wadannan abubuwan darasi ne ga al'ummar musulmi.
....koda yake akwai wahalhalu cikin hakan da wajibi ne a jure masu; to sai dai wadannan wahalhalu mafari ne na samun sauki. Wato 'yanci, daukaka, samun nasara, samun dadin hukumar Musulunci da tsira daga hannun ma'abota girman kai da zalunci, koda yake yana da wahalhalu wadanda wajibi ne a jure musu. A farkon Musulunci irin wadannan wahalhalu ne aka fuskanta, sakamakon hakan shi ne jagoranci da karfi mara tamka da musulmi suka samu a duniya na tsawon karnuka. Duk da cewa daga baya an samu lalata cikin jami'an gwamnatocin Musulunci, to sai dai wannan karfafaffen tushe na farko da aka gina ya samu nasarar daukan wannan gagarumin nauyi tsawon karnuka. Saboda haka wajibi ne mu jure. Wajibi ne al'ummar musulmi su yi sadaukarwa don su sami nasarar tsallake matsaloli da ababen da suke kawo cikas. Haka zai rage kaifin ma'abota karfi da girman kan duniya kowace rana.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din