Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Zababbun Jawaban Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Dangane Da Auren Matasa:

Ali Khamenei5

Ubangiji ba ya son mace da namiji su zauna su kadai.
Ubangiji madaukaki ba ya son mace da namiji su kasance su kadai, musamman wadanda suke matasa kuma a karon farko. Lamarin bai kebanta da matasa su kadai ba. Ubangiji madaukaki yana son rayuwa ta tarayya da kuma aure. Mutumin ya zauna shi kadai, namiji shi kadai da macen ita kadai, su gudanar da dukkan rayuwarsu su kadai, a mahangar Musulunci ba abu ne da a ke so ba. Kamar wani bakon abu ne a cikin gangar jikin mutane. Musulunci yana son iyali su zama tushen da tsarin zamantakewa zai ginu akansa ba daidaikun mutane ba.

Dukiya da kyau ko kamala? Mene ne dalilin?
Idan ya zamanto mutum ya yi aure ne saboda dukiya ko kyau, kamar yadda ya zo a cikin wata riwaya mai yiyuwa ne Allah ya sa shi ya samu wannan dukiyar da kuma kyawun kuma mai yiyuwa ne ya hana shi. Amma idan mutum ya yi auren ne saboda takawa da kame kai, Allah madaukaki zai kuma ba shi dukiya da kyawu. Mai yiyuwa ne wani ya ce kyawu ba abu ne da ake yin baiwarsa ba, ko dai mutum yana da kyau ko kuma ba shi da shi! Abin nufi shi ne cewa saboda kyawu abu ne da ya ke a cikin idanunka da kuma cikin zuciyarka da kuma mahangarka, koda mutum (da kake so) ba shi da kyau sosai to amma saboda son da kake masa sosai sai ka ga yana da kyau. Idan kuma ya zamanto ba ka son wani mutum to duk yadda ya kai da kyau ba za ka ga kyawunsa ba.
Namiji mai tsayuwa ne mace kuma mai dadin kamshi
Musulunci yana daukar namiji a matsayin mai tsayuwa mace kuma mai taushi. Wannan kuwa ba rashin girmama mace ba ne kuma ba rashin girmama namiji ba ne. Ba rashin kula da hakkin mace ba ne kuma ba rashin kula da hakkin namiji ba ne, siffata hakikanin dabi'arsu ne. Ma'aunin aikinsu kuwa daidai da daidai ya ke. Wato idan mace da take ma'abociyar taushin hali da kyawu kuma mai sa a sami kwanciyar hankali da kawatawa a cikin fagen rayuwa aka dora ta akan daya tafin ma'auni, sannan kuma aka dora wannan ma'abocin tafiyar da ayyuka wanda kuma mace ta dogaro da kuma jingina da shi akan daya tafin ma'aunin to wadannan tafukan za su yi daidai wa daida. Ba wannan ko wancan da zai rinjayi wani.

Ma'anar Sa'ada.
Sa'ada tana nufin nutsuwa da jin dadi da samun tsaro. Yin shagali da israfi da yawan sarrafa abubuwan rayuwa ba su bai wa wani sa'ada. Sadaki da kayan daki ba su baiwa wani sa'ada. Zama da juna cikin amana da aiki da shari'a ne ke baiwa mutane sa'ada.

Sa'ada tana nufin nutsuwa da jin dadi da samun tsaro. Yin shagali da israfi da yawan sarrafa abubuwan rayuwa ba su bai wa wani sa'ada. Sadaki da kayan daki ba su baiwa wani sa'ada. Zama da juna cikin amana da aiki da shari'a ne ke baiwa mutane sa'ada.
Soyayya Ce Tushen Komai
Idan aka sami soyayya a cikin rayuwa, to wahalhalun da suke wajen gida za su zama masu sauki. A wajen mace ma wahalhalun cikin gida za su zama masu sauki.
A cikin aure, soyayya ita ce tushen komai. Wajibi ne 'yan mata da samari su san wannan. Ku kare wannan soyayyar da Allah ya sanya a cikin zukatanku.

Hudubar daurin aure ranar 17/10/1374
'Yan mata da samari, amarya da ango su kaunaci juna: domin wannan kaunar tana a matsayin danko ne da rike su, wanda kuma za su kiyaye shi, su kula da shi a kusa da su kada su rabu da shi. Soyayya abu ne mai matukar kyau. Idan da akwai soyayya to da akwai cika alkawali.

Manya Ma Su Taimaka
Dole ne a shiryar da matasa, amma bai kamata a rika shiga cikin kananan abin da ya shafe su ba wanda zai zama matsala ga rayuwarsu.
Kada ya zama saboda tsoma bakin wasu, wasu kuma ta hanyar rashin dacewa da kuma halayya ta yara, su girgiza wannan gini mai karfi. Idan ku ka ga cewa tsoma bakin da suke yi zai sa zukatan mace da miji su gurbata, to ba su da hakkin da za su sake tsoma baki.


Rayuwa Mai Sauki Da Tsaka-Tsaki

Ku dauki rayuwa da sauki, koda yake mu ba ma'abota zuhudu da takawa mai yawa ba ce. Kada ku zaci haka. Sassaukar rayuwar da mu ke magana ba ta masu zuhudu da ma'abota ibada ba ce. Sassauci akan abin da mutane a wannan lokacin suke yi, idan kuwa ba haka ba idan da ace mutanen Allah za su zo su ga yadda mu ke rayuwa to watakila za su ci gyaranmu sau dubu akan abin da mu ke kira rayuwa sassauka.

Wadatuwa Ta Zuci Tana Da Amfani Ga Kowa
Ku zama masu wadatuwa ta zuci. Kada ku ji kunyar wadatuwa. Wasu suna daukar cewa wadatuwa ta marasa abin hannu ce da talakawa, idan kuwa mutum yana da wadata to ba wajibi ba ne a wurinsa ya zama mai wadatuwa ta zuci. Ko kadan, wadatuwa tana nufin mutum ya wadatu gwargwadon bukata kuma da wanda ya isa.
Dogon fata na abin duniya yana jefa rayuwa cikin kunci da kuma rashin dadin mutum. Idan mutum yana da takaitaccen fata daga rayuwa to zai sami sa'ada. Ba wai kawai lahirar mutum ce za ta yi kyau ba, duniyar mutum ma za ta yi kyau.


Ku Fara Tun Daga Bukin Angwanci

Ku dauki komai da sauki a cikin dukkanin rayuwarku. Farkonsa kuma ya zama daga bikin aure: daga nan ne a ke farawa. Idan ku ka fara yinsa cikin sauki mataki na gaba ma zai zama da sauki idan kuwa ku ka shirya taro mai girma irin na manyan mutane da masu matsayi na dagutu, to daga baya ba za ku iya tafiya cikin karamin gida da takaitattun kayayyaki ku rayu. Haka ba za ta yiyu ba. Domin kuwa na riga an bata, an kuma yi rashi. Tun da fari ku sanya harsashin rayuwa a zama mai sauki saboda rayuwarku da ta mutanenku da sauran mutane na al'umma ta kasance mai sauki da yardar Allah.

Shirye-Shiryen Biki Masu Sauki Na Auren Musulunci
Idan ku ka dubi shirye-shiryen bikin aure a tsakanin al'ummu daban-daban za ku ga cewa shirye-shiryen aure a Musulunci yana da sauki. Tabbas yin biki da murna ba su da wani aibu, kowa zai iya yi gwargwadon yadda ya ke so, amma wadannan shirye-shiryen ba su cikin abin da addini ya tsara a cikin aure. Duk wanda ya ke so zai iya yi, duk wanda baya so ba zai yi ba, ba wai dole ne sai ka tafi zuwa wani wurin bauta ka tsuguna bisa gwuiwowinka ba a gaban wani ka yi wasu abubuwa da kuma wasu shirye-shiryen a wasu wurare, babu wannan a Musulunci. A cikin shari'a da akwai a hudubar da dole ne a karanta ta. A cikin mu'amala a Musulunci wacce muhimmancinta bai kai na aure ba ana bukatar sheda. A wannan lokacin da akwai tanadin yin rajista da ajiyata a kotuna. Cibiya ce ta adana bayanai wanda ba ya da wasu al'adu da ake yi; zai iya zama mai saukaka yin aure ba tare da wani dogon shiri ba.

Ku Yi Koyi Da Iyalan Annabi (S.A.W)
Mafificiyar budurwa a duniya ita ce mai girma Zahra (aminci ya tabbata a gare ta). Saurayi da ya ke mafifici a duniya kuma siriki mafifici shi ne Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Ku duba ku ga ni yaya suka yi aure? Dubban samari masu kyawu da asali da nasaba na duniya ba su kai darajar gashi daya na Aliyu Bin Abu Talib (aminci ya tabbata a gare shi) ba. Dubban ‘yan mata masu kyawu da asali da nasaba ba su kai kwayar gashin Zahra (aminci ya tabbata a gare ta) ba. Su suna da matsayi na koli a addini. Kuma sun kasance daga cikin manyan zamaninsu. Ta kasance diya a wurin Ma'aiki (tsira da amincin su tabbata a gare shi da iyalansa), wanda shi ne shugaban al'ummar musulmi ma'abocin sakakken iko. Shi kuwa ya kasance soja mai daraja ta daya na Musulunci. Ku duba ku ga yaya suka yi aure? Yaya sadakinsu kadan ya ke, yaya kayan dakinsu kadan suke. Kowane abu ya kasance da sunan Allah da kuma tunawa da shi. Su suna a matsayin abin koyi ne a wurinmu. A lokacin jahiliyya sadakin ‘ya'yansu mata yana da yawan gaske ga misali rakumi guda dari. Shin su sun fi diyar Ma'aiki (tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa)? Kada ku yi koyi da su (jahiliyya) ku yi koyi da diyar Ma'aiki (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa). Ku yi koyi da Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi).

Tufafin Aure Na Jinga!
Wasu suna sayen tufafin aure mai tsada. Ko kadan bai dace ba! Me zai sa haka ya zama dole. Yanzu da ake bukatar tufafin aure, wasu suna zuwa su dauki jingar tufafin aure. Me ya ke nufi? Abin kunya ne? Ko kadan! Wane abin kunya? Me ya ke nufi? Wasu suna daukar wannan a matsayin abin kunya. Abin kunya shi ne mutum ya bada kudade masu yawa ya sayi abin da zai yi amfani da shi sau daya, sannan daga baya ya aje shi gefe daya. Abin da ake amfani da shi sau daya! Kuma ya kasance a cikin wannan irin halin da mutane suke ciki. Tabbas da akwai mabukata.

Annabi Mai Girma (s.a.w.a) Ya Karya Sunnar Jahiliyya Ta Sadaki.
Mutumin da ya shar'anta tsarin sadaki - wato Annabi mai girma, tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa - wanda ya ke da daraja ta koli sama da dukkan halittu diyarsa ma'abociyar tsarki kuma abin kaunarsa wacce take da daraja ta koli sama da dukkan matan farko da karshe, wanda mijinta kuma shi ne Amirul Muminin aminci ya tabbata a gare shi wanda kuma ya ke sama da dukkan halittun farko da karshe bayan Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa, amma kun ga yadda Annabi ya ayyana sadakin wadannan mutanen biyu wadanda suke masu kyawu, sanannu, masu girma kuma mutanen farko da suka zauna a Madina?
Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya zo ya rusa dukkan wadannan abubuwan, saboda suna hana a yi aure. Su ne suke hana 'yan mata da samari yin aure. Ya fadi cewa ku yi watsi da wadannan abubuwan. Farkon aure abu ne mai sauki. Ta fuskar abin duniya ya fi zama mai sauki. Abin da ya fi zama mai muhimmanci a aure shi ne kulawa irin ta 'yan adamtaka.

Me Ya Sa Ake Nacewa Akan Sisin Gwal 14?
Da ku ke ganin muna fadin cewa ba za mu daura auren da aka bukaci sama da sisin gwal 14 ba, ba wai saboda sama da sisin gwal goma sha hudu yana haifar da matsala ba ne a cikin aure, ko kadan! Ya ma zama sisin gwal dubu goma sha hudu, babu matsala a cikin auren, babu wani bambanci. Muhimmi shi ne cewa bangaren addini ya fi bangaren abin duniya yawa. Kada ya zama kamar kasuwanci. Kada ya zama amfanuwa ce ta abin duniya. Idan kuka rage yawan shirye-shiryen biki to bangaren addini da takawa zai yawaita.
Gwargwadon yadda sadaki ya zama kadan gwargwadon yadda yake kusantar dabi'ar aure, domin kuwa dabi'ar aure ba kasuwnaci ba ne, ba saye da sayarwa ba ne. Ba kuma ba da jingina ba ne. Rayuwa ce ta mutane guda biyu. Wannan alakar kuwa ba ta da alaka da abin duniya, sai dai shari'a mai tsarki ta ayyana sadaki wanda dole ne a bada wani abu. Amma bai kamata ya zama mai yawa ba. Dole ne ya zama wanda ya dace ta yadda kowa zai iya yi.
A cikin aure, abin da ya ke faruwa shi ne kulla alaka a tsakanin mutane, ba wai kasuwanci ba na kudi da dukiya. Duk da cewa da akwai batun kudi a ciki to a cikin shari'a wannan kudin yana a matsayin wata ala'ama ce. Ba ciniki da saye ba ne.

Daukakar Buduruwa Yana Da Alaka Ne Da Halayenta Ba Kayan Daki Ba.
Kayan daki ba su ne su ke baiwa budurwa matsayi ba. Daukakar budurwa yana da alaka ne da kyawawan halayenta da mutuntakarta. Wasu daga cikin iyalan amarya suna cutar da kawunansu da kuma wahalar da kansu idan kuma ba su da kudi suna samun kudi cikin karfi. Idan ba su da kudi suna yin israfi saboda su tanadi kayan daki na kyale-kyale su baiwa 'yarsu.
Sadaki da kayan daki masu yawa ba su sa wata mace ta sami sa'ada kuma ba ya bai wa wasu iyalai nutsuwa da kwanciyar hankali da suka dace. Wadannan wasu abubuwa ne na gefen rayuwa. Gyara ne a cikin rayuwa kuma suna daga cikin abubuwan da suke jawo wahala da kuma matsaloli da ba su da amfani.

Hudubar daurin aure ranar 18/09/1375
Kada ku je ku ci bashin kudi saboda sayen kayan daki. Kada ku jefa kanku cikin wahala. Kada ku jefa iyalai a cikin matsala. Kada ku zaci cewa idan akan kaiwa yarinya kayan daki kasa da makwabta da kuma dangi da 'yan'uwanta to zai sa ta jin kunya. Ko kadan! Babu jin kunya ciki.

Gasa Da Matsalar Kayan Daki.
Iyalan da suke gasa akan abin da suka ga wasu da shi, suna mai da kayan daki su zama musu wata matsala. Baya ga sanya kansu cikin wannan matsalar suna kuma jefa wasu a cikin matsalar. Saboda idan ka tanada wa 'yarka wadannan kayan daki idan wani ya gani me zai yi? Har zuwa yaushe za'a ci gaba da yin wannan gasar? Wadannan ne matsalolin da za su rika faruwa. Musulunci ba ya son wannan ta kasance.

Kayan Dakin Mafificiyar Mace A Duniya.
Ku duba ku gani diyar Annabi mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa, ita ce mafificiyar mace a duniya, wato Fatima Zahra (amincin Allah a gare ta). Mafifiyar mace daga farkon duniya zuwa karshe ita ce Fatima Zahra (amincin Allah a gare ta). Babu wata mace kamarta a kyawawan halaye da daukaka da girma. Dukkan matan duniya daga farko har karshe idan aka kwatanata su da ita to suna a matsayin masu yin hidima ne a gare ta. Sun yi kama da kwayar zarra a gaban rana da take haskaka duniya ne. Mijinta kuwa shi ne Amirul Muminin (amincin Allah a gare shi) wanda ya ke mafificin mutum na duniya. Idan mu ka hada dukkan falafolinsa da karamominsa wuri guda, to dukkan mutanen duniya ba za su kai darajar farcensa guda daya ba; wadannan mutanen biyu ma'abota girma da kyawu da falala sun yi aure. Kayan dakinsu wasu abubuwa ne masu araha wanda ya zo a cikin littatafai: tabarma guda daya da daurin dabino da gado guda daya da dutsen nika da tulu da kwano guda daya. Idan aka hada su a wuri guda kimar kudinsu a wannan zamanin to mai yiyuwa ba za su wuce 'yan dubban Tuman ba.
Wadannan kayan ne Amirul Muminin (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya saya ya kuma bada kudinsu domin shirya takaitattun kayan daki zuwa gidan aure. Ba wai muna cewa a wannan lokacin 'yan mata su zama kamar Fatima Zahra' (amincin Allah a gare ta) ba ne ta wajen yin kayan daki. 'Ya'yanmu ba su da matsayi irin na Zahra, mu kanmu ba mu da matsayi irin mahaifinta kuma 'ya'yanmu ba su da matsayi irin na Amirul Muminin amincin Allah ya tabbata a gare shi da ya auri Zahra. Ina matsayinmu ina nasu? Da akwai bambanci kamar na sama da kasa. Sai dai abu ne da ya ke sananne cewa wannan ce hanya. Wannan ce alkibla. Ku sami takaitattun kayan daki. Kada ku rika dubin wannan da wancan. Kada ku kashe kudade masu yawa. Kada ku kirkiro matsala a cikin abin da mutum ba shi da shi.
Kayan dakin Fatimatuz-Zahra' (amincin Allah ya tabbata a gare ta) gwargwado ne ta yadda watakila mutane biyu za su tattara su su dauka daga wannan gidan zuwa wancan. Ku duba ku ga wadannan abubuwan na alfahari. Wannan shi ne kima. Shi Annabi mai tsira da aminci da iyalansa ba za iya hada kayan daki hadaddu ba? Idan Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) ya yi ishara da musulmin da suke a zagaye da shi da wasu daga cikinsu suke da hali, suna da kudi suna kuma fatan su je su baiwa kyauta, su kuma yi taimako, amma ba su yi ba. Me ya sa ba su yi ba? Saboda ni da ku mu dauki darasi. Amma idan ya zamanto za mu zauna mu bada labari mu ji dadi sannan daga baya ba mu dauki wani darasi ba, mene ne amfaninsa? Ba mu amfanuwa da shi. Idan mutum ya zo da takardar magani ta likita ya ajeta a kan teburin domin ya rika kallo. Dole ne mu yi aiki da shi domin amfanuwa da shi. Dole ne mu yi aiki da tsarin cin abinci domin mu ga amfaninsa. Wannan tsarin abincin ruhi ne, tsarin abinci ne lafiyar al'umma ne. Lafiya ce ta iyali wacce dole ne a yi aiki da shi. Ku yi shi cikin sauki.

Amare Mata! Kada Ku Bada Dama.
Kada ku bari ayi kayan daki masu yawa. 'Yan mata kada ku bari. Amare kada ku bari. Ku ma iyaye maza da mata kada ku bari ko da kuna so. Me za ku yi da wadannan kayan masu tsada?
Iyayen amare su rike hannu wajen sayen kayan daki, kada ku wuce gona da israfi. Kada ku fadi cewa 'yar mu ce za a kashe mata zuciya. Ko kadan! 'yan mata suna da halin kwarai. 'Yan mata ba su son wannan. Kada mu kashe musu zuciya ba tare da wani dalili ba ta hanyar sayo musu duk wani abu mai kyau da na shagwaba.
Wadannan 'yan matan da suke son sayen kayan daki suna zuwa shaguna masu tsada a wasu wurare da ke Tehran domin sayen kayan aure, wadannan shagunan masu tsada da suke sannanu - ba ni son in ambata suna - na san a wuraren da suke domin shaguna ne sanannu da tsadar kaya. Kada ku nufi inda suke. Ku tafi wurin da ba'a san shi da tsada ba. Kada ya zamanto an tasa ango a gaba zuwa wurin sayen kayan amarya da kayan aure. Abin takaici abin da suke yi kenan.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Old school Swatch Watches