Mahangar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Dangane Da Jihadi
A TakaiceJihadi yana nufin gwagwarmaya don cimma wata manufa mai girma kuma abar girmamawa. Yana da fagage daban-daban; daya daga cikin wadannan fagage ita ce kasantuwa a fagen yaki da amfani da makami. Kamar yadda kuma yake da fage na siyasa, yana kuma da fage na ilimi, kamar yadda kuma yake da fage na kyawawan dabi'u. Abin lura cikin tabbatuwar sunan jihadi (a kan wani aiki) shi ne cewa wannan yunkurin da za a yi, ya zamanto yana da mahanga da ya kuma zama yana fuskantar ababen da suke kafar ungulu, wanda ake bukatar himma wajen kawar da wadannan abubuwa masu kawo cikas, to wannan shi ne yake zama gwagwarmaya. Jihadi yana nufin irin wannan yunkuri da gwagwarmaya wacce a lokacin da ta zamanto tana da mahanga da kuma manufa ta Ubangiji, to a irin wannan yanayi ne wannan jihadi yake iya samun bangare na tsarki.
Ni dai ina kiran matasanmu abin kauna zuwa ga jihadi da kokari na hakika. Jihadi dai ba shi ne kawai yin yaki ba. Kokari a fagen ilimi, kyawawan dabi'u, alaka da aiki kafada da kafada na siyasa da bincike, a na kirga dukkan wadannan abubuwa a matsayin jihadi. Samar da al'adu da ingantattun tunani cikin al'umma shi kansa wani jihadi ne. Saboda mai yiyuwa ne makiya su shagaltar da mu, su batar da tunaninmu mu dinga yin kuskure; duk wani mutumin da ya yi wani yunkuri a tafarkin inganta tunanin mutane, ya kawar da irin bata da wasa da hankalin da ke tattare da su, ya kuma kawar da yiyuwar mummunan zato, sannan kuma ya kasance a fagen fada da makiya ne, to sunan wannan kokari da ya yi ‘jihadi'. Dukkan wadannan abubuwa jihadi ne a tafarkin Allah kuma fisabilillahi. Bangaren da ake wannan jihadin a kansu su ne ma'abota girman kai, makiya da kuma wadanda suke adawa da zaman lafiya, da Iran, da mutumci, ‘yan kasanci, riko da Musulunci da siffofi na Musulunci. Alkur'ani mai girma yana cewa: musulmi masu tsanani ne a kan kafirai. A ina wadannan kafiran suke? Ba wai kowane mutumin da bai yi imani da Musulunci ne za a nuna masa tsanani ba. Duk wani mutumin da bai nuna muku adawa ba, bai kulla muku makirci ba sannan kuma bai daura damarar ganin bayanku da zuriyarku ba, koda kuwa mabiyin wani addini ne na daban ba Musulunci ba, to wajibi ne a kyautata alaka da shi da kuma nuna masa kyawawan dabi'u, ba su ne kafiran da ya zama wajibi a tsananta musu ba. Mutumin da wajibi ne a tsananta masa shi ne mutumin da yake fada da mutumcinku, Musulunci, ‘yan kasanci, kasa, iyakokin kasarku, daukaka da al'adu da ababenku masu kima. Wannan ita ce al'adar da ya kamata ta yadu a cikin al'ummarmu. Wajibi ne a tabbatar da fahimtar juna da sulhu tsakanin musulmi.
Daya daga cikin fitattun siffofin da suke cikin al'adun Musulunci, wanda aka fi ganin babban misdakinsa cikin tarihin farko-farkon Musulunci wanda da wuya a same shi tsawon tarihi, shi ne "al'adar yaki da jihadi". Jihadi ba shi ne kawai kasantuwa a fagen yaki ba, saboda duk wani kokari da tsayin daka a gaban makiyi ana iya kiransa jihadi. Koda yake mai yiyuwa ne wasu su yi wani aiki, su sha wahala sannan kuma su bayyana wannan aiki na su a matsayin jihadi. Amma hakan ba daidai ba ne. saboda daya daga cikin sharuddan jihadi shi ne ya zamanto wajen fuskantar makiyi ne. Wannan fuskantar makiyi, a wani lokaci ya kan kasance ne a fagen daga ne da makamai wanda ake kiransa da ‘jihadi na makami'; wani lokacin kuma a fagen siyasa ne, wanda ake kira da ‘jihadi na siyasa'; a wani lokaci kuma ya kan kasance ne a fagen lamurran da suka shafi al'adu, shi ne ake kiransa da sunan ‘jihadin al'adu', wani lokaci kuma a fagen sake gina kasa ne wanda ake kiransa da ‘jihadin sake gina kasa'. Koda yake dangane da jihadi, akwai wasu jihadin ma a fagage na daban. A saboda da haka, jihadi ba wai kawai ya takaita ne da fagen yaki da amfani da makami ba, abin lura shi ne gwagwarmaya, wanda a kowace gwagwarmaya akwai abubuwa guda biyu da suka zama wajibi. Na farko shi ne a sami kokari na gaskiya da yunkurawa, na biyu kuma shi ne ya zamanto wajen fuskantar makiyi ne.
A jihadi, wuce gona da iri da take hakkokin mutane ba su halalta ba. A jihadi fakewa da wani abu da kuma kashe wannan da wancan bai halalta ba. Babu batun kashe duk wani mutumin da ba musulmi ba cikin jihadi. Ba wai duk wani mutumin da bai yi imani da Musulunci ne ake tsananta masa da gallaza masa ba. Face wadanda ake gallaza musu su ne mutanen da suke adawa da kuma yakan mutumcinmu, Musulunci, ‘yanci, akida, al'adu, kan iyakoki da ababe masu kima na musulmi. A irin wannan yanayi ne ake kirga jihadi a matsayin hukumci na Ubangiji wanda aka same shi to al'umma ta kan samu daukaka da girma.
Abin da juyin juya halin Musulunci ya koyar da al'ummarmu shi ne al'adar jihadi. Al'adar jihadi a dukkanin fagage, a fagen ayyukan gina tushen ayyukan gona da kiwo da makamantansu wadanda tun a farko farkon juyin juya halin Musulunci a ka sanya wannan ruhi da al'ada ta jihadi. Saboda shi kansa juyin juya halin Musulunci ya samar da wasu cibiyoyi da wadanda a zatinsu akwai yunkuri da kumaji na juyin juya hali da jihadi.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved