WAYEWAR MUSULUNCI A MAHANGAR JAGORAN JUYIN JUYA HALIN MUSULUNCI
A Takaice:Wayewar Musulunci ta samo asali ne sakamakon yunkuri na ilimi da aka faro shi tun ranar farko na Musulunci. Ba a gama cika cikakkun karnoni biyu daga bayyanar Musulunci ba har sai da aka samar da irin wannan gagarumin yunkuri na ilimi na Musulunci, hakan kuma a irin yanayi na wancan lokacin. Idan har kuna son ku kwatanta irin wancan yunkuri na ilimi na wancan lokacin da irin na yau ne, to wajibi ne ku yi la'akari da irin yanayi na ilimi da ci gabansa da aka samu a duniya a yau, daga nan kuma sai ku dauka cewa wata kasa ce wacce take wani bangare na duniya mai nisan gaske wacce ta yi nisa da duk wani irin ci gaba; amma wannan kasa ta fado fagen ilimi da wayewa da ci gaba sannan kuma bayan tazara da shekara dari ko dari da hamsin, amma ta yi fintinkau wa sauran wayewa (na duniya) a banaren ilimi; lalle wannan yunkuri ya yi kama da mu'ujiza, lalle lamari ne da ma ba za a iya tunanin faruwarsa ba. Hakan kuwa ba zai taba samuwa ba idan ba don Musulunci ya kasance addini ne mai kwadaitarwa zuwa ga ilimi da nemansa da karantar da shi da kuma rayuwa irin ta ilimi ba.
Jauharin wayewar Musulunci, yana tattare da shi ne. Koda yake wayewar da ke raye ya kan amfana da wayewar sauran mutane ma. Abin tambaya a nan shi ne cewa wannan duniya wacce ta ci gaba; wannan kokarin amfani da kuma aiki da ilimi, wannan ci gaban da aka samu wajen gano wannan duniya samammiya - wato dai wannan duniya da ake ganinta - wacce aka samo ta ta hanyar musulmi; wannan irin amfani da tunani da kwakwalwa da irin wadannan gagaruman ayyuka na ilimi da kuma samar da gagarumar jami'oin wancan lokacin a irin wancan yanayin da duniya take ciki; da samar da gomomin kasashe ma'abota dukiya da kuma tsayawa da kafafunsu a wancan lokacin da kuma irin karfi na siyasa maras tamka tsawon tarihi da ake da shi, dukkanin wadannan abubuwa daga ina aka samo su? Ba ku taba ganin wata kasa tsawon tarihi wacce take da irin wannan karfi na siyasa tun daga tsakiyar Turai har zuwa wannan yanki na Asiya; wato ta tabbata a matsayin wata kasa guda sannan kuma wata hukuma guda ta zamanto tana mulkinta! A zamanin jahiliyyar Turai, lokaci ne na jahilci da wahalhalu da bala'oi na kasashen Turan. Su kansu turawan suna kiran wannan zamani na jahiliyyar Turan da sunan ‘bakin zamani da ke cike da duhu". A daidai wancan zamanin na jahiliyyar Turai da Turan take cikin duhu, amma a wancan zamani lokaci ne na ci gaban ilimi da yaduwarsa a kasashen musulmi, daga cikinsu kuwa har da Iran. Dukkanin irin wadannan karfi na siyasa da irin wannan karfi na ilimi da irin wannan bayanar da kai da irin samar da irin wannan kasa da kuma irin amfani da dukkanin rayayyen karfin da ake da shi da kuma ayyukan bil'adama, dukkanin wadannan abubuwa an samo su ne sakamakon koyarwar Musulunci.
Karni na hudu na hijira, karfi ne na kolin ci gaban wayewar Musulunci. A wannan karni na hudu na hijira - wato karni na sha daya miladiyya, lokacin da turai take cikin kolin jahilci da duhunta babu wani abin da take da shi - to irin gagarumin ci gaban Musulunci yana tattare da Iran ne. Masanan da ake da su - in banda ‘yan wasu ‘yan kadan - kusan dukkaninsu Iraniyawa ne. A wani lokaci wadannan mutanen yammaci su kan samo iliminsu ne daga gabashi daga wannan Iran din, mafi yawa daga cikin ilmummukan da ake da su a duniya a yau tushensu dai su ne Iraniyawa. Kusan dukkanin ilmummukan Turai tarjamomi ne ilmummukan da suka samo su daga yankuna da kuma kasashe na musulmi. Alhali kuwa a wancan lokacin ma riko da addinin da ake yi a Iran bai gaza irin wanda ake yi a turai ba, kai ya ma dara shi. A saboda haka, ba addini ne ya ke hana samar da ilimi ba; wani abin ne dai na daban yake hana ci gaban ilimi. To abin tambaya shi ne cewa mene ne wannan abin? Shi ne kuwa jahilci daban-daban da dan'adam yake fama da shi, shi ne irin camfe-camfe na mabiya addinin kirista na wancan lokacin. Ba a taba ganin wani malami a duniyar musulmi da aka wulakanta saboda ilimin da yake da shi ba, alhali kuwa a Turai an kashe wasu saboda ilimi, an jefe wasu, an rataye wasu, wasu kuma da dama an kona su. Wato irin abubuwan da suka faru a can din sun samo asali ne daga addinin kiristancin da aka riga aka gurbata shi da kuma irin jahilcin da suke fama da shi, wanda ya mamaye duniya. To a halin yanzu mene ne laifin Musulunci? Mene ne laifin musulmi? Mene ne laifin al'ummar musulmi?
Duk da cewa Musulunci ya kasance wani yunkuri ne na addini da kuma kyautata dabi'u, to amma ko shakka babu ci gaban ilimi da daukaka ta tattalin arziki suna daga cikin manufofin Musulunci. Ba a riga da an ketare shekaru hamsin daga bayyanar Musulunci ba sai ga shi sama da kashi hamsin cikin dari na kasashe da yankunan da suka ci gaba na wancan lokacin suna karkashin tutar Musulunci ne sannan kuma tsawon karnonin biyu na farko na duniyar musulmi mai girma na wancan lokacin, ta zamanto koluluwa ta bil'adama a bangaren ilimi da nau'oi daban-daban na masaniya da kuma nau'oi daban-daban na ci gaban kasa da tattalin arziki. Hakan ba abu ne mai samuwa ba idan ba don albarkacin koyarwar Musulunci wanda ya ke ba da muhimmanci ga ci gaba na kyawawan dabi'u kafada da kafada da ci gaban duniya ba.
Ci gaba na duniya na kasashen yammaci, yana kwadaitar da dukkan mutane ne zuwa ga son duniya da riko da abin duniya, sannan kuma kudi da cika ciki da biyan sha'awa su ne babbar himmarsa. Sannan kuma tsarkin zuciya, daidaito, yafuwa, sadaukarwa a sassa da dama na duniya sun koma baya da kuma barin fage ga son zuciya, makirce-makirce, kwadayi, hassada, rowa da sauran munanan dabi'u. A yau an kai ilimi wani waje da ya kauce wa hanyar (wayewa na hakika) ta yadda a halin yanzu duniyar yammaci ba za ta iya ‘yantar da bil'adama ba, wannan dai shi ne abin da yake ci wa bil'adama tuwo a kwarya. A duk inda ilimi yake, amma sai aka rasa addini da kyawawan dabi'u da ‘yan'adamtaka da tausayawa, to kuwa dan'adam ba zai amfana da irin wannan ilimin ba. Ilimi ba tare da addini da kyawawan dabi'u ba ya kan zama wani bom ne na atom da ya kan fada kan rayukan mutanen da ba su ci ba su sha ba; ya kan zama makami, da zai fada kan fararen hula a kasashen Labanon da Palastinu da sauran yankuna na duniya. Ya kan iya zama sinadari mai guba, sannan ya kashe mata da kananan yara, mazaje da matasa da dabbobi a yankin Halabja da sauran yankuna na daban.
Mu dai a wayewar Musulunci da kuma a tsarin Jamhuriyar Musulunci mai tsarki wanda muka kama hanyar wannan wayewar, mun dauki hakan a matsayin manufa, wato ilimi tare addini da kyawawan dabi'u su tafi kafada da kafada da junansu. Abin da ya sa ku ke ganin kasashen yammaci suna nuna tsananin damuwarsu saboda riko da addinin da muka yi, suna kiran wannan riko da addini da muka yi da sunan tsaurin ra'ayi da kuma koma baya, sannan kuma suna kiran rikon da muka yi da tushe na kyawawan dabi'u da dan'adamtaka a matsayin take hakkokin bil'adama, hakan saboda wannan tafarki da muka rika ya saba wa tafarkinsu ne. A saboda haka a daidai lokacin da muke kokarin amfanuwa da irin ci gaba na ilimi da aiki da aka samu, wajibi ne kuma, don isa ga tafarki tsira da magance matsalolin da ake da su, mu shuka tsiron ci gaban duniya da na lahira da hannunmu sannan kuma mu sanya ido har su nuna kuma kada mu kasance masu koyi (ido rufe) da wannan da wancan.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved