80s toys - Atari. I still have
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Isar Da Sakon Maras Karfi Ga Shugaba

Ali khamenei3

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce:

أبلغوني حاجة من لايستطيع إبلاغي حاجته، فإنه من أبلغ سلطاناً حاجة من لايستطيع إبلاغها ثبت اللّه قدميه على الصراط يوم القيامة


"Ku isar min da bukatar wanda ba zai iya isar da bukatarsa ba. Domin duk wanda ya isar wa (wani) shugaba da bukatar wanda ba zai iya isa gare shi ba, Allah zai tabbatar da dugadugansa a kan siradi ranar kiyama".
(Tahaful-Ukul shafi na 47).
Abin da ake nufi da kalmar "سلطـان" (shugaba) da ta zo cikin wannan ruwaya shi ne duk wani mai matsayi da iko. Wato duk wanda yake da wani mukami (jami'i) a wajen aikinsa kuma yana da wani iko, misalin shugaban wata ma'aikata ko alkalin wata kotu ko kuma jami'in wata cibiya da makamantansu. A takaice dai duk wani mutum da yake da wani matsayi da iko, sai aka samu wani mabukaci ko wani da yake da aiki da shi amma ba zai yiyu ya samu isa gareshi ba, to duk wanda yake da halin mika koke da bukatar mutane zuwa gare shi, Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi masa wannan alkawari na lada mai girma na ketare siradi a ranar kiyama.



.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din