Polaroid
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali
Wasu Bangarori Na Jawaban Ayatullah Khamene'i Dangane Da Rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a)

Ali Khamenei5

* Samuwar Annabi mai girma kuma Manzon Musulunci mai girma, ita ce mafi muhimmancin wajen tabbatar da hadin kai (tsakanin musulmi). A baya ma mun fadi hakan cewa duniyar musulmi tana iya haduwa da juna a wannan wajen; wannan waje wani waje ne da dukkanin so da kaunar dukkanin al'ummar musulmi take komawa gare shi. Wannan wani waje ne da so da kaunar duniyar musulmi ya tattaru a wajen. A saboda haka ne a halin yanzu kuke ganin wadanda suka karbi kudade daga wajen yahudawan sahyoniya suke ta koari wajen cutarwa da kuma cin mutumcinsa (Manzon Allah); saboda a hankali a hankali su kawar da muhimmanci da musulmi suke ba wa batun cin mutumcin al'ummar musulmi da kuma wulakanta duniyar musulmi daga zukatansu. Wannan shi ne batu na asali. Wajibi ne ‘yan siyasarmu, masananmu na bangaren ilimi da al'adu, marubuta, mawaka da masu fasaharmu su ba da muhimmanci ga wannan batu sannan kuma dukkanin musulmi su yi amfani da shi wajen tabbatar da hadin kai da kusatar juna a tsakaninsu. Kada su damu da ababen da ake da sabani kansu, kada su dinga tuhumar junansu; kada su dinga kafirta junansu sannan kuma kada su fitar da junansu daga da'irar addini. Zukatan dukkanin al'ummar musulmi sukan sami karfin gwuiwa da jin nishadi saboda tunawa da Manzon Allah (s.a.w.a) da kuma kaunarsa.; don kuwa dukkaninmu masu so da kaunar wannan ma'abocin girman ne.

* A wannan lokacin, suna da kuma tunawa da Manzon Allah mai girma ya fi zama a raye sama da lokutan da suka gabata; hakan kuwa daya ne daga cikin boyayyiyar hikima da tausaya ta Ubangiji. A yau al'ummar musulmi da al'ummarmu suna bukatuwa da Manzon Allah (s.a.w.a) sama da dukkan lokutan da suka gabata; suna bukatar shiryarwarsa, da bushara da gargadinsa, da sako da koyarwarsa, da rahamar da ya koyar da bil'adama ita da kuma koyarwarsa. A yau koyarwar Manzon Musulunci ga al'ummarsa da kuma dukkanin bil'adama darasi ne na zama masani, samun karfi, darasin kyawawan dabi'u da karama, darasin rahama, darasin jihadi da daukaka, da kuma darasin gwagwarmaya da tsayin daka ne. A saboda haka, a dabi'ance sunan wannan shekarar zai zamanto sunan Manzo mai girma ne. A karkashin wannan suna da wannan ambato na Manzon Allah (s.a.w.a), wajibi ne al'ummarmu ta bi diddigin darussan da Manzon Allah ya bayar sannan kuma su mayar da su darussan rayuwa da tsare-tsarensu. Al'ummarmu tana alfahari da kasancewa dalibar makarantar annabi da darasin (Annabi) Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa). Al'ummarmu sun daga tutar Musulunci tsakanin al'ummar musulmi cikin tsayin daka da karfi; sun jure wa wahalhalu, sun ga dukkanin ababen amfanin da suke cikin wannan fage na daukaka da alfahari, sannan kuma cikin ikon Allah da falalarSa irin wadannan nasarori da ababen amfani za su ci gaba da zuwa. Wajibi ne mu sanya darussan kyawawan dabi'u na Manzon Allah, darasin daukaka na Manzon Allah, darasin koyarwa da darasin rahama da karama da darasin hadin kai da ya koya mana da darasin rayuwarmu cikin tsare-tsaren rayuwarmu.

* Ambaton suna mai tsarki na Annabi mafi girma (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa) da kuma yin sharhi kan wani bangare na rayuwar wannan mai girma a hakikanin gaskiya ya kasa sannan kuma irin shaksiyya abar haske ta wannan madaukakin bawan Allah wanda babu kamarsa cikin halittu ba ta fito fili kamar yadda ya dace ga mafi yawa daga cikin mutane. Haka nan tarihin rayuwar wannan mai girma ba, haka nan kyawawan dabi'unsa, haka kuma halayensa na daidaiku da na siyasa.

* Annabin Musulunci mai girma (s.a.w.a) ya fara ne da gina mutum; da farko dai ya fara tsai da wannan tushe ne, don ya sami damar dora musu nauyin wannan gini. Tsawon dukkanin wadannan shekaru goma - wanda ayyukan shekaru dari ne suka taru cikin wadannan shekaru goman - Manzon Allah a dukkanin bangarori, a lokacin wahala na yaki ne, a lokacin gina kasa ne, a lokacin yin ibada ne, a lokacin tattaunawa da magana da mutane ne, bai taba mantawa da gina mutumci da shaksiyya ta mutanen da yake magana da su ba. Manzon Allah (s.a.w.a) hatta a lokacin yakukuwa masu tsanani da wahala irin su Ahzab da Badar da Uhudu ya kasance yana gina dan'adam. Ku duba ayoyin Alkur'ani mai girma mana ku gani, za ku ga cewa ‘gina mutum' ita ce manufar wannan sako, hakan kuwa yana daga cikin manyan ayyuka.

* Manzon Allah (s.a.w.a) tun a lokacin yarinta, mutum ne ma'abocin tsafta. Sabanin yaran garin Makka sannan kuma sabanin sauran yaran larabawa, ya kasance mutum ne mai son tsafta da kuma zama cikin tsari. Haka nan a lokacin kuruciya, ya kasance mai kula da kansa, sannan kuma lokacin samartaka mutum ne mai kula da tsafta da kyautatawa. Bayan bayyanar Musulunci, bayan da ya wuce lokacin samartaka, ya kai lokacin da ya girma - kimanin shekaru hamsin zuwa sittin - a lokacin ma ya kasance mutum ne mai tsananin kula da tsafta. Gashinsa abin daukaka wanda ya kasance har zuwa wajen kunnuwansa, a ko da yaushe cikin tsafta yake; haka nan jikinsa a ko da yaushe a tsaftace yake ga kuma kamshi. Na taba karantawa cikin wata riwaya cewa a gidansa yana da wani kwano na ruwa wanda yake zuwa yana kallon fuskarsa mai albarka a ciki - saboda a wancan lokacin madubi bai yadu sosai ba - "Ya kasance ya kan gyara rawaninsa da gemunsa idan yana son fitowa zuwa wajen sahabbansa", wato a duk lokacin da yake son fitowa wajen musulmi da abokansa, babu makawa ya kasance ya kan gyara rawaninsa da kuma jikinsa sosai, daga nan kuma sai ya fito waje. A ko da yaushe ya kasance yana sanya turare a jikinsa da zama cikin kamshi. A lokacin tafiya kuwa duk da irin rayuwar gudun duniya da yake yi - a nan gaba zan yi karin bayani kan yadda rayuwarsa ta kasance cikin tsananin gudun duniya - ya kasance ya kan dauki matsefin kai da turare tare da shi. Ya kan dauki kwalli don shafawa a idonsa saboda a wancan lokacin a bisa al'ada maza suna sanya kwalli. A kowace rana ya kan goge bakinsa sau da dama. Sannan kuma ya kan kirayi sauran mutane zuwa ga wannan tsafta da wannan goge baki da kuma irin zama cikin wannan tsari. Kuskuren da wasu suke yi shi ne cewa tsaftace jiki da kuma kyautata yanayin jiki yana tafiya ne tare da almubazzaranci; ko da wasa. Ana iya zama cikin tsafka da tsoffin tufafin da ake da su. Tufafin Manzon Allah (s.a.w.a) tsoffi ne (ba wai sabi ba ne); amma dai a tsaftace suke da kuma zama cikin tsari. Wadannan abubuwa ne da suke da tasirin gaske cikin dabi'u, mu'amala da kiwon lafiya. Wadannan abubuwa ne da a zahiri suke a matsayin kananan abubuwa, to amma a badininsu abubuwa ne masu tasirin gaske.

* A lokacin da aka haifi wannan mai girma, fadojin Kisra duk sun ruguje, wajen (bautan) wutan (da ke Farisa) wanda karnuka da dama ta yi tana ci, ta mutu; mabubbugar ruwan Sabeh wacce a wajen da dama daga cikin mutanen wancan lokacin tana da wani tsarki, ta bushe, haka nan kuma gumakan da suke cikin dakin Ka'aba sun girgiza; sun ruguje. Wadannan abubuwa ne da suke nuni da wani lamari, suna nuni da bangaren irada da sunna ta Ubangiji da take tattare da wannan abin halitta mai girman gaske sannan kuma wannan shaksiyya wacce ba ta da tamka. Ma'anar wannan lamari shi ne cewa sakamakon bayyanar wannan abin halitta mai tsarki karshen wulakancin da ake yi wa bil'adama, shin ta hannun sarautan azzaluman sarakuna da masu mulkin kama-karya ne - irin mulkin da ya kasance a wancan lokacin a Iran da Rum - ko kuma ta hanyar bautan wanin Allah, wajibi ne a kawo karshensa. Wajibi ne ta hanyar wannan abin halitta mai albarka, dan'adam ya samu ‘yanci; shin daga cikin kangin zalunci ne da azzaluman sarakuna suke yi wa mutanen da ake zalunta tsawon tarihi, haka nan kuma daga kaidin camfe-camfe da akidu marasa tushe wanda hakan ya kan sanya mutum kankan da kai ga wani abu wanda bai kai shi daukaka ba ko kuma a gaban wani mutum na daban, ya zamanto kaskantacce da kuma daukaka shi.

* Wannan haihuwa mafarin rahama ce ta Ubangiji ga tarihin bil'adama. A cikin Alkur'ani mai girma an bayyana samuwar Annabi (s.a.w.a) da cewa "Rahama ce ga dukkan talikai". Wannan rahama kuwa, ba a kayyade ta ba; ta hada da tarbiyya, tsarkake zuciya, koyarwa da shiryar da mutane zuwa ga mikakken tafarki da kuma ci gaban bil'adama a fagen rayuwa ta duniya da kuma ta lahirarsa. Haka nan kuma wannan rahamar ba wai ta takaita ga wancan zamanin ba ne, ta dukkanin zamunna ne. "Da wadansu mutane daga gare su wadanda har yanzu ba su riske su ba". Hanyar isa ga wannan manufar, ita ce aiki da koyarwa da dokokin Musulunci wadanda suke a fili ga bil'adama.

* Annabinmu mai girma - wanda aka sanya wa wadannan ranaku sunansa sannan kuma ranakun haihuwarsa suka zamanto abin koyi ga dukkanin muminai da dukkanin musulmi - a lokutan wahala, ba ya damuwa da cewa irin kankan da kai da neman taimakon Ubangiji da yake yi mai yiyuwa ne ya sanya wani tunani cikin zukatan wadanda yake magana da su da kuma wadanda suke ganinsa cewa lalle shi gajiyayye ne. A fili yake fadin cewa lalle ni gajiyayye ne, idan ba don taimakon Ubangiji ba babu wani abin da zan iya. A lokacin yakin Ahzab, a daidai lokacin da makiya suka kewaye dukkanin Madina da kuma shi kansa Manzon Allah da muminai da nufin su kawar da Musulunci da Alkur'ani da wannan sabon addini gaba daya, amma Manzon Allah (s.a.w.a) a gaban dukkan wadannan sojoji, a gaban dukkanin irin matakan da aka dauka da suke cike da hikima, a gaban kumajin mutane da suke son a kwama, a gaban idanuwan mutane haka ya sanya gwuiwoyinsa a kas (yana rokon Allah). Ba sau daya ba hakan ta faru, akwai bayanansu cikin littafan tarihi. Manzon Allah (s.a.w.a) ya kan daga hannuwansa sama, yana mai kaskantar da kansa, yana zubar da hawaye yana cewa: Ya Ubangiji! Ka taimaka mana, ka samar mana da nasara, Ka ba mu dacewa.

* Yunkurin Musulunci a Iran karkashin jagorancin babban mai ‘yanto al'umma na wannan zamani, (wato) mai girma Imam Khumaini (yardar Allah ta tabbata a gare shi) bisa riko da tafarkin Annabi mai girma kuma Manzon karshe sannan kolin halittun duniya da kuma bil'adama, mai girma Muhammad al-Mustafa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa), ya bayyanar da kansa a matsayin wani cikakken juyi, wannan shi ne dabi'ar juyi wanda idan ya tsayu bisa ingantaccen asasi da tsayayyiyar hikima, haka zai haifar da ababen mamaki a dukkan bangarori da kuma yin tasiri cikin rayuwar kowa da kowa da motsa su.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din