SALLAH A MAHANGAR JAGORAN JUYIN JUYA HALIN MUSULUNCI
A Takaice:Dukkanin ababen bakin cikin da bil'adama suke fama da su sun samo asali ne daga gafala daga Allah da kuma takaita kai da ababen son zuciyar na daidaiku. Salla tana ‘yantar da mutum daga dukkanin wadannan takunkumi na duhu da suka yi masa dabaibayi. A saboda haka a dukkanin addinan Ubangiji (saukakkun addinai), yin salla shi ne asalin abin da ke nuni da riko da addini sannan kuma fitacciyar alama ta imani. Ita kuma salla ta Musulunci ita ce sallar da tafi cika da kamala cikin sallolin sauran addinan Ubangiji.
Kalmomin da zikirorin da ake yi a cikin salla, kowane guda daga cikinsu wani bangare ne da ke nuni da wani sashe na masaniyar addini sannan kuma hakan a koda yaushe ba tare da katsewa ba yana tunatar da mai salla wadannan abubuwa ne. Sallar da aka yi cikin tunani da sanin ma'anonin (abin da ake karantawa) sannan kuma ba tare da mantuwa da gafala ba, to a kowace rana tana sanar da mutum ilmummuka da masaniya ta Ubangiji sannan kuma da ci gaba da kusata zuciyarsa zuwa ga wadannan abubuwa.
A duk lokacin da aka yi salla cikin tsanaki da dawo da zuciya waje guda da kuma jin cewa a gaban hallarar Ubangiji ne, to ba wai kawai zuciya da ran mai sallar ba, a'a hatta ma yanayin da yake ciki zai zamanto mai taushi da haske da kuma kamshi sannan kuma zai sanya gida da yanayi na iyali da wajen aiki da fagage na abokantaka da dukkanin inda ake taruwa da gudanar da rayuwa za su zamanto cike da ababen jin dadi da annashuwa. Sallar da take cike da tuntuni da kuma jin cewa ana gaban Ubangiji ne ita ce dai wannan salla da take cike da zikiri da ambaton Allah, sallar da take karantar da mutum mafi girma da daukakar masaniya ta Ubangiji. Irin wannan salla ce ta ke ‘yantar da mutum daga rashin sanin madafa da manufa da kuma rauni sannan kuma ta ba shi himma da irada da kuma manufa sannan kuma ta bayyanar masa da koli na rayuwa a gaban idanuwansa ta kuma tseratar da zuciyarsa daga munanan abubuwa. A saboda haka ne a koda yaushe mutum yake bukatar sallar, sannan kuma wannan bukata ta kan fi tasowa ne a lokacin da mutum yake fuskantar wani hatsari. A hakikanin gaskiya salla ita ce mafi kyawun jigo na addini da a duk lokacin da mutum yake son amfanuwa da ita to wajibi ne ya yi aiki da hikima da kwarewarsa da kuma jin shaukin aikata hakan.
Salla ita ce matakin farko na tafiya zuwa ga Allah; to amma fagen wannan aiki na Ubangiji wanda idan ya samu damar cika da kamala yana iya sanya fuka-fukin tashi saman mutum su karfafa, ta yadda hata mafi daukakan mutane tsawon tarihi wato Annabin Musulunci mai girma da daukaka yake cewa: "Salla hasken idanuwa na ne". Kai ana ma iya cewa babu wani aiki na ibada na daban da yake da tasirin gaske a dukkanin matakan cikan dan'adam da kuma ba shi karfin gwuiwa a wannan bangaren (kamar salla).
Salla rukuni ne na asalin addini a saboda haka wajibi ne ta zamanto tana da matsayi mafi girma cikin rayuwar mutum. Rayuwa ta dabi'a ta mutum za ta kasance ne karkashin inuwar hukumci na addini ne a lokacin da mutane suka damfara zukatansu ga zikirin Allah da ambatonSa sannan kuma ta hakan ne za su iya fada da dukkanin kyale-kyale da ababen jan zuciya dake cikin fasadi da sharri sannan kuma su ruguza dukkanin gumaka sannan kuma su gutsure hannuwan dukkanin shaidanu na ciki da waje daga cikin rayuwarsu. To za a iya samun irin wannan zikiri da hallara ta har abada ce ta hanyar salla; a saboda haka salla ita ce wannan karfafaffiyar garkuwa sannan kuma rumbun da ba ya karewa na mutum a gwagwarmayar da yake da shaidanin da ke tattare da shi da yake jan sa zuwa ga lalata da kuma shaidanu masu karfi wadanda ta hanyar amfani da karfin da suke da shi suke tilasta masa mika kai da zama cikin kaskanci.
A wannan lokacin da duniya take karkashin ikon injuna, mutum da dan'adamtaka suna cikin tsananin matsin lamba. Wannan yanayi ya tilasta wa dukkanin bil'adama wajen sanya rayuwarsa ta daidaiku da ta al'umma wajen tafiya tare da wadannan injuna. A saboda haka ne a yau al'ummomin duniya sama da shekarun baya suke bukatuwa da samun alaka da Ubangiji Ma'abocin tausayi, ita kuwa salla ita ce mafi girma da kyawun hanyar tabbatar da wannan bukata da ake da ita.
Akwai wadansu siffofi guda uku na asasi cikin salla wadanda suke da tasirin gaske wajen tsarkake zuciya da karfafa tunanin dan'adam.
Ta farkonsu ita ce cewa salla, ta irin yanayin da Musulunci ya tsara kuma ya yi bayaninsa, wato wadannan motsi da zikirori na musamman, to a dabi'ance suna janyo hankalin mai salla ne zuwa ga nesantar zunubi da sabo.
Na biyu ita ce cewa ta kan sanya wa mutum ruhin bauta da kankan da kai a gaban Allah Madaukakin Sarki wanda Shi ne abin kauna na hakika da fidira ta dukkanin bil'adama, salla ta kan sake rayar da wannan ruhi.
Na uku ita ce cewa tana ba wa mai salla irin wannan kwanciyar hankali wanda shi ne sharadin samun nasarar mutum cikin rayuwa sannan kuma ta nesantar da irin damuwar da yake fama da ita wacce take hana mutum ci gaba da kuma daukan matakin da ya dace da dukkan karfinsa wajen kyautata dabi'unsa daga gare shi.
Mutum yana fuskantar matsaloli da bala'oi daban-daban ne. Don kuwa kowane mutum yana da mantuwa da kura-kurai, sannan kuma zunubai sukan bijiro masa. Idan har mutum yana son ya samu nasara a tafarkin rayuwa, to kuwa salla tana iya zama hanyar da za ta lamunce masa hakan. Wata ayar Alkur'ani mai girma tana cewa: Kuma ka tsai da salla a gefe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan kwarai suna kore munanan ayyuka. Salla tana da wani irin haske, tana kawar da duhu daga kan hanya, tana kawar da munanan halaye daga sannan kuma ta kan kawar da alamun zunubai daga cikin zuciya. Don kuwa ai mutum yana iya fuskantar ababen da za su bakanta masa rayuwa. Matukar ya lizimci salla to wannan haske da kuke da shi zai ci gaba da zama sannan kuma zunubi ba zai sami damar kutsuwa cikin rayuwarka ba.
To yana da kyau a san cewa masallaci ba wai waje ne kawai na salla ba; a kan gudanar da na'oi daban-daban na ibada a cikin masallaci. Daga cikin wadanan ibadu akwai tunani ta yadda mutanen da suke tafiya masallaci za su iya samun wannan tunani ta hanyar jin jawabi da wa'azin da wani malamin zai yi a masallacin. A saboda haka, masallaci wata makaranta ce, wata jami'a ce, haka nan kuma wata cibiya ce ta tunani, sannan kuma wata cibiya ce ta tsarkake zuciya kamar yadda kuma wata cibiya ce ta tsarkake niyya da kuma samun kusancin bawa ga Ubangijinsa. Waje ne na kulla alaka ta kasa da sama. Wani waje ne da mutum yake kulla kansa da wannan mabubbuga mara katsewa da kuma karfi. Mutum a masallaci yana iya kusata kansa da Ubangiji.
Tsayar da salla shi ne tasiri da amfani na farko sannan kuma alama ta hukumar salihan bayi. Daya daga cikin manyan ayyukan Imaminmu mai girma (Imam Khumaini - yardar Allah ta tabbata a gare shi) shi ne dai irin wannan samarwa da kuma assasan sallar juma'a da ya yi. Shi ne ya samar wa wannan al'umma sallar juma'a. Shekara da shekaru kenan aka haramta mana yin sallar juma'a.
A gani na daya daga cikin mafi muhimmancin abubuwan da suka kiyaye imani da ruhin mutane su ne wadannan salloli na juma'a da wadannan hudubobi na sallar juma'a da kuma irin halartar fagen sallar juma'a da mutane suke yi. Wato a samu wani mutum amintacce wanda mutane suka yarda da shi ya tsaya a gaban su cikin gaskiya a ko wata juma'a yana musu bayanin yanayin da kasa take ciki sannan kuma ya yi musu nasiha sannan kuma ya gyara musu irin fahimta da matsayarsu kan lamurran da suka taso. A saboda haka wajibi ne sallolin juma'a su zamanto wani waje ne na janyo hankali da nasiha da koyarwa. Limaman juma'a masu girma bisa taimakon masu shirya bukukuwan sallar juma'ar su ba da dukkanin kokarinsu wajen tabbatar da hakan.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved