Kyawawan Halaye A Mahangar Jagoran juyin juya halin Musulunci
A TakaiceA duk wata al'ummar da kyawawan halaye suka yadu a cikinta, sannan kuma suka zamanto masu kyawawan halaye - da suka hada da yafuwa da kau da ido, kyautatawa, adalci, ilimi da neman hakki - , sannan kuma aka samu adalci a tsakaninsu, sannan kuma munanan halaye suka zamanto babu su a tattare da su, to kuwa mutane za su samu kyakkyawar rayuwa da take cike da jin dadi. Hakikanin yanayi na kowace al'umma, shi ne irin yanayin kyawawan halayenta. Wato a hakikanin gaskiya asasi na asali na kowace al'umma shi ne yanayin kyawawan dabi'u na wannan al'umma sannan kuma dukkanin komai zai ginu ne bisa asasin hakan. A lokacin da wata al'umma ko kuma wata kasa ta rasa irin wadannan kyawawan dabi'u, to kuwa za ta rasa yanayinta na hakika.
A cikin shari'ar Musulunci mai tsarki an yi cikakken bayani kan kyawawan dabi'u na Ubangiji da kuma kyawawan halaye; shin abubuwan da suke da alaka da shi kansa mutum ne - irin su hakuri, godiya, ikhlasi da kuma wadatuwar zuci - ko kuma wadanda suke da alaka da sauran mutane irin su kau da kai, tawali'u, sadaukarwa da kuma girmama ‘yan'adam - ko kuma abubuwan da suke da alaka da al'umma ce ta Musulunci. Kyawawan dabi'u na Musulunci suna da fadin gaske. Wadannan su ne dai abubuwan da mafi girma daga cikin kokarin Annabawan Allah da waliyai da sauran manyan mutanen addinan Ubangiji suka kumsa - sannan kuma a addinin Musulunci dukkanin kokarin Manzo mai girma da tsarkakan Imamai - duk sun ginu ne bisa tushen samar da wadannan abubuwa. A hakikanin gaskiya daya daga cikin kan iyaka da kuma abubuwan da suke bambance Musulunci da jahiliya shi ne wannan batu na kyawawan halaye.
Dukkanin bata da kauce wa hanyar da suke faruwa cikin wata al'umma, tushe da asasinsu suna komawa ne ga dabi'u da halayenmu. Siffofi na kyawawan halayen mutane, su ne suke ba wa ayyukanmu fuska da kuma jiha sannan su kuma tsara su. Idan har muka ga wasu munanan dabi'u da halaye suna yawo cikin al'umma da kuma a fagen kasa da kasa (duniya), to wajibi ne mu nemi tushe da dalilansu cikin munanan halaye da dabi'u. Idan muka duba za mu ga cewa dukkanin bala'oin da suka fadawa bil'adama sun samo asali ne daga munanan halaye da fasadi daban-daban da suke cikin halayen mutane. Ko da yake bai kamata mu mance da dalilai na siyasa da tattalin arziki ba. Amma idan kuka yi dubi cikin dukkanin tushen wadannan abubuwa, to za ku ga cewa akwai wani tushe da dalili na munanan dabi'u cikin hakan. A yau idan muka dubi bala'oin da suke damun duniyar bil'adama, bala'oin da suka samo asali daga girman kai da babakere na siyasa a duniya, duk suna komwa ne ga tushe na dabi'u, kamar yadda da dama daga cikin bala'oi da wahalhalun da mutane suke fuskanta, mafi yawansu suna komawa ne ga jahilcinsu.
A yau idan har akwai zalunci da mulkin kama-karya a duniya sannan kuma munanan dabi'un kasashen yammaci sun mayar da duniya ta zamanto wani fage na amfani da karfi da zalunci da amfani da tursasawa da kuma fadin rashin gaskiya - tursasa ikon masu karfi kan al'ummu da kuma satan dukiyar al'umma da manyan cibiyoyin kudi na duniya suke yi - sun cika duniya, hakan ya samo asali ne sakamakon rashin ruhi na kusaci da Ubangiji da kuma kyawawan dabi'u. A lokacin da aka rasa ababen da suke kusata mutum da Allah da kuma kyawawan halaye, to kuwa sharri da fasadi za su yi galaba sannan kuma kudi da amfani da karfi za su samu gindin zama, haka nan kuma masu mulki da dukiya za su yi duk wani abin da za su iya wajen cimma wannan manufa ta su, sannan kuma duniya za ta zama kamar yadda ta zama a yau.
A tsarin demokradiyya na yammaci, a kan ba da kulawa ga wani matsayi na musamman wanda a mafi yawan lokuta ana kula da batun kungiyanci da jam'iyya ne. A tsarin jamhuriyar Musulunci baya ga batun ilimi da dacewa ta siyasa, har ila yau kuma ana kula da dacewa ta kyawawan dabi'u da akida. Bai kamata wasu su ce ai kyawawan dabi'u da akida batu ne na daidaikun mutane ba. Na'am, kyawawan halaye da akida lamari ne na daidaiku da suke da alaka da mutum; to amma a wajen wani jami'i akida da kyawawan dabi'u ba lamari ne na daidaikun mutane ba; lamari ne na jama'a da kuma al'umma; yana da iko ne kan makomar mutane. Shi wannan mutum baya ga batun kwarewa da dacewa ta zati da kuma ilimi na zati, yana kuma bukatar jaruntaka da halaye, tsoron Allah na addini da siyasa da ingantacciyar akida.
Batun kyawawan halaye batu ne mai muhimmancin gaske. A saboda haka tsarin Musulunci ba zai iya rufe ido kan al'adu da kyawawan halaye na mutane ba. Tsarin Musulunci ba tsari ba ne wanda abin da kawai zai ba shi muhimmanci shi ne kiyaye ikonsa (kan mutane) amma kuma mai nuna rashin damuwa da ayyukan mutane ko da kuwa hakan ba shi da alaka da batun kyawawan halaye ba. Tsarin Musulunci dai yana damuwa da duk wani abin da zai batar da mutane da kawar da su daga kan tafarki na kwarai. Wannan tafarki ne na Manzo mai girma (s.a.w.a) don haka wajibi ne tsarin Musulunci ya zamanto yana da irin wannan tafarki da kuma riko da shi. Tsarin Musulunci dai ba zai iya zuba ido da nuna halin ko in kula dangane da wahalhalu na ruhi da jiki da abubuwan da suke kokarin batar da al'umma da kuma tunaninsu ba.
Haka nan kuma wajibi ne halaye da dabi'unmu su zamanto daidai da abubuwan da muke fadi sannan kuma mu ke kira zuwa gare su. Ko shakka babu idan har muka sanya kafafunmu da tsayin daka kan abubuwan da muka yi imani da su sannan kuma muke kira zuwa gare su, sannan kuma a aikace muka tabbatar da su, to kuwa wadannan maganganu na mu za su yi tasiri a fagen da muke. Idan har aka samu hakan to a wannan lokacin ba ma tsananin bukatar matsin lamba da tursasawa sosai ba. Face dai shi kansa wannan abu mai janyo hankula cikin ayyuka zai janyo hankulan sauran mutane.
Ko da yake a wani sauyi cikin al'umma abin da shi ne na karshe da za a yi kokarin gyara shi shi ne halaye.... Abin da ake samun jinkiri wajen sauya shi su ne dabi'u da halaye na mutane, shin halaye ne na daidaiku ko kuma halaye na al'ummance wanda kowace al'umma akwai wani irin hali da aka santa da shi: wata al'umma an fi saninta ‘yan garanci, wata al'ummar kuma an san su ne da son jin dadi da rayuwa cikin sauki da dai sauransu, wadannan abubuwa a kan dauki lokaci kafin a sauya su.
Abin farin cikin shi ne cewa a cikin shekarun baya-bayan nan al'ummarmu musamman ma matasanmu sun sami ci gaban gaske a bangaren kyawawan halaye da kyautata ruhi. To sai dai wadannan abubuwa ba su ne kawai sauyi na halaye ba. Mai yiyuwa ne ana iya cewa sauyi na halaye ga al'umma lamari ne mai wahalar gaske. A saboda haka ne dangane da batun sauyi na halaye, wadanda ake magana da su a matakin farko su ne matasa wadanda dukkanin abubuwa a gare su lamari ne mai sauki. Zukatan matasa suna cike ne da haske, haka nan fidira da tunaninsu lafiyayyu suke wadanda ba a taba su ba. Lalacewarsu da son ababen duniya, wadanda suke sanya mutum zaman mai son kudi da neman matsayi da kuma iko da makamantan hakan, ba su da yawa. A saboda haka sauya halayen matasa yake da saukin gaske. Ko da yake su ma masu matsakaicin shekaru bai kamata su yanke kauna daga yiyuwar sauya halayensu ba. Sauyi na halaye yana nufin mutum ya yi watsi da dukkanin muggan halaye - dukkanin muggan dabi'u, dukkanin wani ruhi maras kyau wanda zai haifar da cutarwa ga sauran mutane ko kuma ya janyo koma baya ga shi kansa mutum din - sannan kuma ya yi dukkanin kokarinsa wajen ganin ya samar wa kansa kyawawan halaye.
A lokacin da hassada da mugun fata suka kawu daga cikin halayen wata al'umma. Sannan kuma wani mutum ma'abocin wani tunani ya nesanci yin amfani da wannan tunani na sa wajen kulla makirci ga sauran mutane da cutar da su da yaudara da ha'intarsu. Haka nan kuma wani mutum ma'abocin ilimi da masaniya ya zamanto bai yi amfani da wannan ilimi nasa wajen cutar da mutane da kuma taimakon makiya ba, maimakon hakan ma sai ya zamanto mai fatan alheri ga dukkanin mutane, sannan kuma lamarin ya zamanto cewa dukkanin mutanen wata al'umma suka zamanto masu fatan alheri ga junansu, ba sa kulla makirci ga junansu, ba sa yin hassada ga juna, ba sa kokarin karfafa rayuwarsu da nufin kawar da sauran mutane sannan kuma ba sa neman sai sun mallaki dukkan komai. To wannan shi ne sauyin halaye sannan kuma mafi karancin lamarin.
A saboda haka ne tushen juyin juya halin Musulunci na Iran ya zamanto ya ginu ne bisa kokarin gina mutum a matakin farko da kuma gyara da gina rayuwar mutum. Kwanciyar hankali da zaman lafiyan mutum ya ginu ne bisa halaye na kwarai wanda wajibi ne a samo su daga koyarwa ta addini. Wannan batu na gina mutum shi ne manufa da kuma abin da dukkanin juyin juya hali na Ubangiji da kuma aiko annabawa suka ginu a kai. Saboda kuwa matukar mutane suka sauya, to kuwa duniya ma za ta sauya.