Mallaka Ta Kashin Kai A Musulunci
‘Yancin Tattalin Arziki A MusulunciDa akwai ‘yanci na gudanar da ayyukan tattalin arziki a cikin al’ummar musulmi, duk da cewa ba wai sakakken ‘yanci ba ne, yana da iyakoki, domin ayyuka ko wadanne iri ne suna da iyakoki. Wadannan iyakokin a Musulunci na musamman ne. A cikin al’ummun da suke bin tsarin tattalin arziki na al’umma – socialism - suna da wani nau’i na iyakoki a kan mallakar dukiya da haja, wadannan iyakokin suna da bambanci da na Musulunci. Gwargwadon yadda mahangar Musulunci take da bambanci da mahangar tsarin gurguzu da ta markisanci, to za a iya cewa da akwai wannan irin bambancin a tsakaninsu da tsarin jari hujja da ya ke iko a yammacin turai, wanda kuma a ke aiki da shi. Tsarin da ake da shi a yammacin turai a wannan lokacin ba karbabbe ba ne a wurin Musulunci, kuma tsarin jari hujja da ake da shi a yammacin turai Musulunci bai amince da shi ba, kuma ma yana matukar fada da shi ne ta fuskar hukumce-hukumce. Abin da Musulunci ya ke gabatarwa a matsayin abin koyi ta fuksar tsarin tattalin arziki babu shi a cikin tsarin jari hujja na yammacin turai. A cikin al’ummar Musulunci iyakokin ‘yancin gudanar da ayyuka su ne wadanda suka zo a karkashin yin sana’a ta haram da sauran ayyukan da aka haramta a cikin littatafan fikihu, wato mu’amala ta riba (kudin ruwa), mu’amala wacce ta samo asali daga jiji da kai da jahilci da sauran harkoki na yaudarar wasu da cutar da wasu, da hulda wacce ta samo asali daga ayyukan da ba a halalta ba, da boye kayayyaki domin tara dukiya da wasu suke yi da tushensu haramun da sauran abubuwan da suka zo a cikin shari’ar Musulunci da ake kira dokokin mu’amala da kuma ‘yancin ayyukan tattalin arziki a cikin al’ummar musulmi.
Yin mu’amala (saye da sayarwa) da wasu daga cikin haja da kaya haramun ne. Kamar giya da sauran abubuwan da suke haramun da najasa idan ba a cikin abubuwan da aka yi togiyar haramcinsu ba, to mu’amala da su haramun ne; ko kuma wata dukiyar wacce ba mallakin mutum ba ce, mallakin hukumar Musulunci ne kamar ganima, wacce idan ba a cikin wasu wurare da aka yi togiya ba, sarrafa su da daidakun mutane za su yi haramun ne, da kuma wasu abubuwa makamantansu da suka zo a bayyane a cikin fikihun Musulunci, wadanda ko da hukuma ba ta sanya idanu a kansu da kuma hana su ba, an riga an bayyana abubuwan da suka halarta daga cikinsu da kuma wadanda ba su halarta ba da wadanda aka hana da wadanda suke haramun.
‘Yancin gudanar da ayyukan tattalin arziki a cikin al’ummar Musulunci shi ne cewa hukumar Musulunci ta dauki wasu matakai da kuma yin wasu dokoki, ta yadda dukkan daidaikun mutane a karkashin al’ummar musulmi za su iya gudanar da ayyukan tattalin arziki cikin ‘yanci kuma kowane bangare na mutane su zamana za su iya amfana da ayyukansu na tattalin arziki. Wannan shi ne daya daga cikin abubuwan da suka bambanta tsarin Musulunci ta fuskar tattalin arziki da kuma sauran tsari na yammacin turai. Hanyar da ke kaiwa ga samar da ayyukan tattalin arziki cikin ‘yanci ga al’umma, ita ce a yi kokarin magance dabi’ar takaita zuba jari ga wadansu mutane kawai. A samar da kayan aiki a cikin al’umma ta yadda mafi yawan mutane, mafi yawan bangarori daban-daban na al’umma ko kuma dukkan wadanda suke da karfin yin aiki, ya zamana za su iya amfana da wadannan kayan aikin wajen sarrafa albarkatun kasa da ruwa da ganima da sahara da dausayi.
Amirul Muminin (tsira da aminci su tabbata a gare shi) yana fadin cewa: “Banga wata wadatacciyar ni’ima ba sai a kusa da ita na ga wani hakki da aka salwantar”. Wannan hadisin yana da ma’ana mai zurfi, ta yadda wasu suke zaton cewa ma’anar wannan hadisin shi ne cewa duk inda ni’ima mai yawa ta ke to da akwai sata da kwace da wasu tsiraru suka yi, a kusa da wannan mai kwacen da akwai wasu mutane masu rauni. Wasu sun kawo ishkali cikin wannan hadisin da cewa ko kadan ba haka ba ne, muna ganin wasu mutane wadanda suke da dukiya kuma ba ta hanyar sata ko kwace suka same ta ba, sun same ta ne ta hanyar kokari, saboda haka ba abin da wannan hadisin ya ke nufi ba kenan. Ma’anar wannan hadisin tana nufin duk inda ake da ni’ima mai yawa da dukiya mai yawa, da akwai dama mai yawa, ita kanta dukiyar da ita kanta ni’imar, tana bai wa mai ita dama mai yawa ta samun kudaden shiga, kuma akan haka ne wannan damar take nesantar wasu. Wanda ya ke da jari mai yawa a cikin al’umma yana da dama mai yawa ta yin sana’a da samar da karin dukiya, kuma zai fi zama mai dama wajen raya dukiyar da ba’a amfani da ita ta mutane, zai fi talaka samun dama, saboda haka a duk inda ake da ni’ima mai yawa da akwai dama mai yawa da mai ita ya samu, yana kuma da kayan aiki. An share masa fagen yin ayyukan tattalin arziki, kuma a cikin mafi yawancin kasashe ana yin dokoki ne saboda mutane irinsa, saboda haka ana raba mafi yawancin mutane da dama - wadanda ba su da dukiya - saboda haka wannan hadisin idan daga Amirul Muminin ya ke, ko kuma ba daga gare shi ya ke ba, yana kunshe da ma’ana ta gaskiya. Saboda haka hanya ingantacciyar ta gudanar da ayyukan tattalin arziki cikin ‘yanci a cikin al’umma musulma ba ta nufin cewa wadanda kadai suke iya magudi na tattalin arziki ne kadai za a baiwa dama, dole ne a ba da dama ga daidaikun mutanen da suke da karfin yin fadi tashi ta fuskar tattalin arziki. Dole yanayin al’umma da tsarin al’umma da dokokin al’umma da yanayin sadarwa a cikin al’umma su kasance yadda dukkan mutane - wato dukkan mutanen da suke da karfin gudanar da ayyuka - su zamana za su iya gudanar da ayyukan tattalin arziki su kuma amfana daga ayyukan da suke gudanarwa.
Iyakar Mallakar Haja Ta Kashin Kai A MusulunciA Musulunci ana girmama mallakar haja ta kashin kai, amma kuma iyakar da ta ke da ita a bayyane ta ke. Wannan haddin na mallakar haja ta kashin kai ba ya nufi adadin riyal ko dala ko dinari. Kima ba ta zama daidai da daidai a kowane lokaci. Mallaka tana da haddi ne daga rashi. Wato gwargwadon yadda zai zama babu cuta babu kuma cutarwa. A bisa dokar “Babu cuta babu cutarwa” idan mallaka ta kashin kai, za ta zama mai cutar da al’ummar musulmi ko kuma wasu daga cikin musulmi, to za a iya yi wa wannan mallakar iyaka.
Mallaka ta kashin kai abu ne abin girmamawa a Musulunci matukar ba ta haddasa boye kayayyaki domin a ci riba mai yawa a gaba da tatsar ma’aikata da nuna bambanci da cin zarafin mutum da kuma dagawa. Abin da yake da muni shi ne tatsar ma’aikata, dagawa cutarwa da almubazzaranci. Saboda wadannan abubuwa ne mallaka ta kashin kai take zama mai muni, amma ita kanta mallakar ba abu ne mai muni ba. A saboda haka wadannan su ne iyakokin mallaka ta kashin kai. Musulunci yana magance wadannan abubuwan, yana yin tir da masu almubazzaranci da kuma almubazzarancin kuma halartaccen shugaba na shari’a da shugaban musulmi yana da hakkin ya hana almubazzaranci da tatsar ma’aikata da nuna bambanci da jiji da kai da dagawa da boye kayayyaki domin cin riba mai yawa da sauransu. Saboda haka an bai wa halartaccen shugaban musulmi da shugaban daular Musulunci wannan dama ne domin ya magance wannan irin hadama.
Tsarin Musulunci ya amince da mallaka ta kashin kai, haka nan kuma ya amince da ayyukan tattalin arziki da kokari na mutane a hakikanin gaskiya kuma yana yin ayyukan da suke son samar da jin dadi da wadatar da marasa shi. A karkashin ‘yanci tsarin tattalin arziki na Musulunci a bisa ‘yancin gudanar da ayyukan tattalin arziki nauyin gudanar da ayyukan tattalin arziki yana wuyan al’umma ne.
Ciyarwa A Karkashin Tsarin Tattalin Arziki Na MusulunciMutane suna da hakkin gudanar da ayyukan tattalin arziki cikin ‘yanci, kuma su ba ma’aikatan gwamnati ba ne. Dukkan mutane za su iya gudanar da ayyukansu, su yi kokarin da za su iya, su samarwa kawukansu kudin shiga, saboda haka wajibi ne mutane su cike gurbin da ake da shi ta fuskar tattalin arziki. Idan mutane sun samarwa kawunansu kudaden shiga to kuma dole ne su kula da bukatun mutane, su cike gibin da ake da shi. Ita kanta ciyarwa tana nufin cike wannan gibin da ake da shi.
Batun ciyarwa wani abu ne mai zaman kanshi a Musulunci. Ciyarwa da bayar da dukiya da abin da mutum ya mallaka na duniya da bukatu na tattalin arziki da cike gibin da ake da shi na tattalin arziki wani nauyi ne da ya ke wuyan al’umma da mutanen da suke gudanar da ayyukan tattalin arziki. Wani hatsari zai iya faruwa a cikin al’ummar musulmi wanda zai sa hukuma ta bukaci kudi, mutane ne wadanda ya zama wajibi su samar da wannan kudin. Al’umma za ta iya fuskantar yaki, za ta iya fuskantar wata barna, wata cuta za ta iya bulla, wani bala’i mai hastari zai iya faruwa, mahangar Musulunci ita ce cewa dole ne mutane su cike wannan gibin da ake da shi gwargwadon damar da suke da ita. Kasantuwar cewa mutane ba matsayinsu guda ba, mutumin da ya ke da dama mafi yawa da mallakar abubuwa mafi yawa to yana da nauyi mafi yawa a wuyansa.
Tara dukiya da kuma rashin ciyarwa wani hali ne mara kyau a mahangar Musulunci kuma sabo wanda watakila zai iya zama sabo mai girma. Ba haka lamarin ya ke ba saboda an halarta zuba jari shi ke nan sai ya zamana mutum yana da hakkin ya tara dukiya ko da kuwa ta hanyar halaliya ce ya rike ta alhali al’umma tana da bukatar dukiyarsa da abin da ya mallaka, yaki bayar da ita ga al’umma da kuma ciyarwa akan tafarkin Allah. Ciyarwa tana da matsayi mai zaman kansa a Musulunci. Dole ne a yi ciyarwa akan tafarkin Allah. Ba a hana yin kasuwanci da tara dukiya ba. Ku yi amma kuma ku ciyar. Musulunci yana sabawa mutane da su yi amfani da abin da suka samu iya gwarwgadon bukatar rayuwa, matsakaicin bukatar rayuwa ba wai a takurawa kai ba, matsakaicin bukata ko da kuwa ya hada da jin dadi da wadatar da kai, sannan kuma abin da ya karu akai ya ciyar da shi ga al’umma. Idan mutum ya tara dukiya sannan ya kashe ta ta hanyar almubazzaranci da yin kawa ko kuma ta jin dadi irin na sarakai da cin abinci na azo a gani da sanya tufafi na alfahari ko abin hawa na azo a gani ko matsugunni na takama, to abin zargi ne a Musulunci duk da cewa shi ne ya tara wannan dukiyar. Rashin ciyarwa abin zargi ne a Musulunci idan kuwa ya hadu da tara dukiya to haramun ne.
A cikin Alkur’ani Ubangiji Madaukaki yana fadin cewa: “Allah ba Ya son duk wani mai ha’inci mai alfahari, wadanda su ke rowa su ke kuma umartar mutane da su yi rowa.” Wanda ya ke yin rowa kuma ya ke kiran wasu da su zama masu rowa, ya ke hana wasu su ciyar akan tafarkin Allah, su kansu ba su bayar da dukiyarsu akan tafarkin Allah. Rowa ba tana nufin mutum ya ki ba da hakkin shari’a ba ne, fiye da hakkin shari’a, fiye da abin da aka ayyana cikin shari’ar Musulunci, idan yana da dukiya mai yawa kuma ya zamana al’umma tana da bukata to dole ne ya ciyar.
Wasu mutanen sun sami dukiyarsu ne ta hanyar damar da ake da ita a cikin al’umma, ta hanyar da aka saba da ita da ta halalta, to ba abu ne karbabbe a Musulunci ya zamana sun rike dukiyarsu alhali al’umma tana da bukatuwa da ita. Wannan ba shi da matsayi a cikin Musulunci sai dai sabanin haka. Akwai sananniyar ayar da ta ke fadin cewa: “Wadanda suke jibge zinari da azurfa ba su ciyar da su saboda Allah to ka yi musu bushara da azaba mai radadi.” Watakila zinari da azufa ba su kebanta da wasu sabanin wasu ba, wadanda suke tara kudi da dukiya da boye su a lokacin da zai zamana mutane a cikin al’umma suna da bukatuwa da su, kuma baya yin ciyarwa akan hanyar Allah, to shi ma zai shiga a karkashin wannan ayar “Wadanda su ke jibge zinari da azurfa” wacce kuma ta ci gaba da cewa: “ka yi musu bushara da azaba mai radadi” Idan wannan ba sabo ba ne mai girma, to me ya kawo batun cewa “ka yi musu bushara da azaba mai radadi”? Ka ba su bushara da azaba mai radadi, wato ka fada musu cewa ku saurari azaba mai zafin gaske ta Ubangiji, kuma wannan azabar mai radadi za ta iya zama sakamako na dabi’a na munanan ayyuka a duniya, wanda kuma sakamakonsa ba zai takaita a gare su ba, zai shafi dukkan al’umma kuma zai iya zama azabar lahira, abu ne kuma mai yiyuwa ya zamana duka biyun baki daya. Wato a duniya da kuma lahira ya zamana akwai azaba saboda wannan aikin, saboda haka ciyarwa wani abu ne da ya ke wajibi.
Amfani Da Bangarori Masu Zaman Kansu Wajen Samar Da Abubuwan BukataDole ne a karfafa mutane wajen kafa kamfanoni masu zaman kansu. Kaso mafi girma na masana’antu a cikin kasa suna karkashin gwamnati ne. Ko da yake tsarin mulki ya ayyana wani sashe wanda iya gwargwado sun kasa akan hakan. Mummunar wani sashe na siyaya ne ya sa ake da cunkoson kamfanoni a karkashin gwamnati. Bangarori masu zaman kansu – ban da wadanda tsarin mulki ya ayyana a kai tsaye cewa dole ne su kasance a karkashin gwamnati kuma dole ne gwamnati ta zama mai tafiyar da su - to dole ne ya zamana wani fage ne na aiki da samar da abubuwan bukata a cikin kasa. Sai dai ya kamata a san cewa mai da kamfanoni zama masu zaman kansu ba ya nufin ta kowane hali kuma ta kowace fuska kuma a karkashin kowace irin siyasa ba tare da la’akari da bukata ta kasa ba, shi kenan sai a mai da su wadanda ba na gwamnati ba. Dole ne a karkafa masu zuba hannun jari su fito a kuma ba su dama da kayan aiki domin karfafa kamfanoni masu zaman kansu. Dole ne a yi wannan aikin cikin tsari da kuma tantancewa kamar yadda ya dace, tare kuma da yin la’akari da cewa wadannan kamfanonin sun dace sannan suna da ikon samar da abubuwan bukata, kuma shin za mu iya kara yawan abin da suke samarwa ko kuma a’a. Idan za su iya yin wannan aikin to dole ne a ba su dama. Saboda haka dole ne tantancewa ta zamana bisa la’akari da dacewa ne, ba bisa alaka ta kusanci ba, alakar ta abota ce ko kuma ta siyasa. Idan har aka yi wannan irin la’akari to shakka babu za a karafafa kafa bangarori masu zaman kansu, kuma za su fito fili.
Sa Idanu Da Lura Da ‘Yancin Tattalin ArzikiDukkan nau’oin ‘yancin da ake da su a cikin al’ummar musulmi dole ne a gudanar da su bisa sa idanun shugaban musulmi da kuma lura da su. Me ya za a gudanar da wannan sa idanun? Saboda kada wannan ‘yancin ya kare da haifar da barna. Kada wannan ‘yancin ya zamana sanadin raba wasu da ‘yanci. Haka lamarin ya ke a cikin ‘yancin tofa albarkacin baki da ‘yancin siyasa da ‘yancin al’adu. Idan ‘yancin tattalin arziki ya zamana duk wanda ya ke da karfin yin kasuwanci yana da sakakken ‘yancin samar da abin da suka ga dama da gabatar da abin da suka ga dama da rarraba kayansu na kasuwanci a duk lokacin da suka ga dama da sayar da abin da suka ga dama to shakka babu wannan ba zai zama karbabbe a mahangar Musulunci ba. A wurin Musulunci baya ga ba da ‘yancin tattalin arziki da hakkin mallaka ta kashin kai - wanda ya bayar ga dukkan daidaikun mutane - to kuma ya wajabta sanya idanu ga masu tafiyar da mulki a kan komai. Wato dole ne masu tafiyar da mulki su sanya idanu saboda kada a yi mummunan amfani da wannan ‘yancin. Hatta akan yadda ake amfani da abubuwan da aka samar dole a sanya idanu, saboda kada a yi almubazzaranci. Ko da yake ya zuwa wani haddi almubazzaranci wani sabo ne da mutum a kashin kansa ya ke yi. Idan a cikin gida aka yi amfani da wani abu bisa almubazzaranci to wannan haramun ne kuma sabo ne. Amma idan ya zamana wannan aikin na haramun ya yi tsanani ta yadda ke yin barazana ga tsarin tattalin arziki na al’umma, to talauci zai yadu a cikin al’umma, ya kuma zama musabbabin da wasu mutane masu yawa za su rasa abubuwan da ake samar da su cikin wahala sannan kuma ta hanyar aikin da mutane masu yawa suka yi, za su kare sannan kuma su fuskanci barazana, to a yanayi irin wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar Musulunci ta dauki matakin hana almubazzaranci da kuma barna.
Tabbas wannan mahangar ba ta takaita cikin wata al’umma guda ba kadai, mahangar Musulunci ce ta duniya baki daya. Kasashen da a wannan lokacin suke almubazzaranci na abinci - wato wasu daga cikin kasashe masu wadata da arziki a duniya da suke amfani da kaso saba’in cikin dari na kayan abinci. Kasashen da suka ci gaba wadanda kaso talatin da biyar ne - na mutanen duniya - idan da akwai adalci a cikin tsarin duniya na tattalin arziki, to da dole ne Majalisar Dinkin Duniya da dukkan cibiyoyi masu karfi su hana su. Idan da ace akwai kungiyoyi a duniya da kuma hukumomin da suke da rayayyen lamiri kuma suke son su yi amfani da karfin da suke da shi domin amfanar da mutane da al’ummu to dole ne su hana yadda Amurka take hana ayi amfani da miliyoyin eka na kasarta domin noma saboda kawai ta hana raguwar farashin kayan abinci, alhali kuwa da akwai dubban kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar da suke mutuwa a duniya saboda yunwa da rashin abinci mai gina jiki; kaso goma zuwa goma sha biyar na mutanen duniya suna rayuwa a karkashin fari; kaso mai yawa na mutanen duniya suna da karancin abinci. A matsayin misali ko dai su hana afkuwar abin da ya ke faruwa a kasuwannin turai a wasu shekarun da suka shude inda suka zuba wani adadi mai yawa na abinci cikin teku saboda su hana raguwar farashin kayan abinci, don kada su bari farashin kayan abinci a duniya da kuma a kasuwannin kasa da kasa ya fadi. Saboda haka fada da almubazzaranci da barnata dukiyar al’umma da yin fada da barnata dukiya a cikin tattalin arziki a fagen kasa da kasa wani abu ne da ake da shi a cikin tsarin Musulunci.
Saboda haka ‘yancin tattalin arziki da hakkin mallaka na kashin kai baya nufin cewa mutum yana da hakkin ya sarrafa abin da ya ga dama ko da kuwa wannan sarrafawar za ta haddasa wasu mutane su mutu saboda yunwa, wasu su kamu da cutuka, ya zamana mutane sun kasa samun abubuwan da za su biya bukatunsu na yau da kullum. Wannan abu ne da bai dace ba a mahangar Musulunci. An hana yin hakan.
‘Yancin Tattalin Arziki Da Kuma Makokar Siyasa Ta Al’ummaBabu wani wuri a Musulunci da za a ba da dama ya zamana ‘yancin tattalin arziki ya zama dalilin tsoma baki a kan makomar al’umma da tsarinta na siyasa. Tsarin tattalin arziki na al’umma wanda a wannan lokacin a kasashen jari jujja na yammaci ya ke da matukar karfi, sai dai a hakikanin gaskiya manyan ‘yan kasuwa wadanda su ne ke sarrafa siyasa ta bayan fage su ne suke juya hakan. Wasu daga cikinsu sun shiga cikin tsarin gwamnati, kamar hukumomin da ake da su a wannan lokacin. Gwamnatin Amurka da makamanciyarta da ‘yan jari hujja ne ke tafiyar da ita. Su ne da kansu suke da hannun jari a cikin manyan kamfanonin man fetur da wadanda ba na man fetur ba. Ko kuma su zamana ba su cikin gwamnati amma ta bayan fage su ne ke tafiyar da ita. Da taimakonsu ne ake nada shugaban kasa. Su ne ke kawo ko gusar da wani mutum a fagen siyasa, a cikin majalisar dattijai da majalisar wakilai duk suna hannunsu ne. Dokokin da ake yi suna dacewa ne da mahangarsu da kuma manufarsu. Wajibi ne ma a kira kasashen Yammacin turai da sunan duniyar jari hujja. Sunan jari hujja ba zai ba da ma’ana ta hakika ba. ‘Yan jari hujja da attajirai da masu kamfanoni da masu dukiya da masu kudi a cikin al’umma su ne wadanda suka samar da sashe mai girma na tsarin jari hujja na yammacin turai a wannan lokacin. Wannan kuwa abu ne wanda Musulunci bai amince da shi ba, kuma duk wani abu da zai kai ga hakan dole ne a magance shi.
Ma’anar Jari Hujja Kamar Yadda Ya Ke A Wannan Lokacin A DuniyaJari hujja yana nufin yin amfani da dukiyar da ta taru ta hanyar tatsar mutane, wato jarin da zai zama an yi amfani da shi domin tatsar mutane. Jarin da wanda ya mallake shi ba ya iya yin komai idan ba ya zama dalilin zai tatsi wasu ba ta hanyar dogaro da shi. Tatsar wasu kuwa zalunci ne shi kuwa zalunci haramun ne. Saboda haka babu wannan irin jari hujjar a Musulunci. Wannan shi ne ma’amar jari hujja kamar yadda ya ke a wannan lokacin a duniya. Idan har mallaka ta kashin kai za ta zama sanadiyyar fasadi da zalunci da nuna bambanci, to a karkashin mallaki na gwamnati ma za a iya samun haka. A cikin kasashen da ake da mallaka ta gwamnati ana iya samun fasadi da zalunci da nuna bambanci, sai dai ta wani yanayin ne kuma a tsakanin wasu mutanen ne na daban.
‘Yancin Tattalin Arziki A Karkashin Tsarin Jari Hujja Na Yammacin TuraiA karkashin tsarin yammacin turai wanda a zahiri bisa dokoki suke riya cewa akwai 'yancin gudanar ayyukan tattalin arziki, amma a hakikanin gaskiya wannan 'yancin bai shafi kowa da kowa ba. Wannan dimbin dukiyar da ake da ita da wadannan koguna da cibiyoyin albarkatu na dabi'a da dausayin kasar noma da ma'adanai da dukkan wadannan kayan aikin da suke a matsayin wani bangare na dukiyar al'umma, ba a cikin sauki za su ba da su ga dukkanin mutane ba, kuma kowa da kowa yana da damar da zai iya amfana da shi da samun riba ba. Hakikanin wadanda suke da 'yanci su ne ma'abota tarin dukiya, wadanda suke rike da bakin zaren tattalin arziki da ma bakin zaren siyasa a cikin al'umma. Su ne wadanda suke da iko akan dukiya da kuma sarrafa ta da amfanuwa da ita; suna takure kofar duk wata dama ga sauran mutane. Saboda haka a cikin al'ummun jari hujja - a cikin 'yan jari hujja da suka ci gaba ne ko kuma cikin 'yan jari hujja masu koma baya - kamar mafi yawancin kasashe masu tasowa da mutanen su suke fama da matsanancin talauci. A daidai lokacin da wani sashe mai yawa na al'umma suke fama da talauci da rashin aikin yi da rashin matsuguni da rashin abin da rayuwa take bukata, wasu tsiraru suna fadi tashi cikin 'yanci, suna ta tara dukiya, suna da ma'adanai amma kuma suna sake tara wasu ma'adanai din. Suna da kamfanoni suna kuma sake bude wasu kamfanonin, suna da fili amma suna sake samun karin wasu filayen, suna amfani da koguna suna yin amfani da dukkan albarkatu, a hakikanin gaskiya wasu tsiraru ne cikin al'umma suke amfanuwa; sauran mutane kuwa - wadanda suke kasawa da sayarwa ne, da ma'aikata, da 'yan kwadago masu hako ma'adanai, ko masu aikin noma, ko masu aiki a kamfanoni - a hakikanin gaskiya duk suna karkashin danniyar wadancan ne, kuma su ne ke amfana daga ribar da ake samu da jin dadinta. Su da kansu ba su da ikon yin wani kokari ko ikon samar da wani abu ko ikon amfana da wani abu, ko ikon wani aiki mai amfani da samar da dukiya bisa cikakkiyar ma'anarsu.
Tattalin Arziki A Kasashen Da Suke Bin Tsarin GurguzuA bisa tsarin tattalin arziki na gurguzu da akidojin da suka samo asali daga markisanci, da akwai iyaka a cikin mallaka ta kashin kai, amma wadannan iyakokin sun sha bamban da na Musulunci. Ga misali a can an hana mallakar hanyoyin samar da abin bukata, wato babu wani mutum guda da ya ke da hakkin mallakar hanyoyin samar da abubuwan bukata kamar kasa da kamfani da makamantansu. A bisa tsarin Markisanci da tsarin tattalin arziki na gurguzu saye da sayarwa wasu abubuwa ne da ake Allah wadai da su a matsayin masu cin karo da abubuwa masu kima. A karkashin wannan akidar sayarwa domin amfanin kai, domin mutumin da ya ke da dukiya, wannan dukiyar ta karu ko ta ragu, abu ne da aka hana. A karkashin akida da tunanin markisanci saye da sayarwa da mu'amala suna a matsayin wani dillanci ne mummuna wanda ba a son shi.
A kasashen da suke bin tsarin tattalin arziki na gurguzu - da dukkan cibiyoyin samar da abubuwan bukata da dukkan kamfanoni da kasa, sannan su kuma mutane suna a matsayin ma'aikatan gwamnati ne - ba a tsammanin mutane su yi wani abu idan wani abu ya faru kamar yaki da barna ko wata cuta. Wane abu ma'aikatan gwamnati za su iya yi? Sai dai idan za su ba da gangar jikinsu ne.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved