XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

SAMAR DA DUKIYA CIKIN TSARIN TATTALIN ARZIKI NA MUSULUNCI

Ali Khamenei5

Samar Da Dukiya A Musulunci
A mahangar Musulunci samar da dukiya ta hanyar halal wacce kuma doka ta tanadar babu wata matsala cikin hakan. Wajibi ne jami'an gwamnati su samar wa mutane da kuma gaya musu hanyoyin da za su iya yin tarayya cikin ayyukan tattalin arziki. Wannan siyasa tana nufin samar da dukiya ta gaba daya ga dukanin al'umma. A mahangar Musulunci babu wani hani wajen samar da dukiya. Akwai bambanci tsakanin samar da dukiya da kuma sace dukiyar (al'umma). A wani lokaci a kan sami wani mutum ya sace dukiyar al'umma, wani lokacin kuma a kan sami wani mutum ne ta hanyar da ta saba wa doka ba tare kuma da bin dokar ba ya kan sami wani abin duniya; dukkanin wadannan hanyoyi haramun ne (an hana su). Amma ta hanyar doka kan, to samar da dukiya a mahangar shari'ar Musulunci mai tsarki da kuma mahangar addinin Musulunci, abu ne abin so kuma ma mai kyau. Mutane su samar da dukiya, to sai dai bai kamata ya zamana akwai almubazzaranci tattare da hakan ba. Saboda kuwa Musulunci cewa ya ke yi ku samar da dukiya amma kada ku yi almubazzaranci. Wuce gona da iri wajen sarrafa abubuwan da ake da su, ba karbabben lamari ba ne a wajen Musulunci. Duk abin da kuka samu a tafarkin samar da dukiya, to ku yi amfani da shi wajen sake samar da wata dukiyar. Bai kamata ku ci gaba da ajiye dukiya haka kawai ba - abin da Musulunci ya kira shi da sunan tattara dukiya - sannan ba kuma ku ta kashe ta ta kowace hanya haka kawai ba gaira ba dalili ba cikin abubuwan da ba wai wajibi ba ne na rayuwa; don haka bisa la'akari da wannnan, ku samar wa kanku da dukiya. Dukiyar daidaikun al'umma, dukiya ce ta kasa, kowa da kowa yana amfanuwa da ita.

Sharuddan Karin Dukiya Ta Kasa
Saboda a sami damar isar da kasa zuwa ga yanayin da za ta wadata da kanta ba tare da neman taimakon wani ba a fagen samar da dukiya ta kasa, wajibi ne hannayen jari da ayyuka na tattalin arziki da samar da dukiya su zamanto a gaban dukkanin masu gudanar da ayyukansu a fagen tattalin arziki na kasa; wato kowa da kowa ya zamana yana da damar ba da tasa gudummawar a wannan fagen. Wajibi ne gwamnati ta goyi bayan hakan; wajibi ne doka ta goyi bayan hakan.

Abin Da Koyarwar Tattalin Arziki Na Musulunci Ya Ginu A Kai
A cikin tattalin arzikin Musulunci ana iya ganin wasu tushe na asali guda biyu. Duk wata hanya ta tattalin arziki, duk wata nasiha da kwafi na tattalin arziki da za su iya lamunce wadannan tushe guda biyu, abin a ba shi muhimmnaci ne. Duk kuwa wani salo, duk kuwa yadda zahirinsa ya kasance na addini ne amma ya gagara tabbatar da wadannan tushe guda biyu, to ba na Musulunci ba ne. Daya daga cikin wadannan tushe guda biyu shi ne "Karin Dukiya Ta Kasa". Wajibi ne kasar Musulunci ta zamanto kasa ce ma'abociyar dukiya; bai kamata ta zamanto fakiriyar kasa ba; wajibi ne ta zamanto ta iya ciyar da manyan manufofinta na kasa da kasa gaba ta hanyar dukiyar da take da ita da kuma karfin tattalin arzikinta. Tushe na biyu kuma shi ne "Rarraba abubuwan da ake da su cikin adalci da kuma kawo karshen rashi cikin al'ummar musulmi". Wajibi ne a samar da wadannan abubuwa guda biyu. Tushe na farkon kuwa sharadi ne na (tabbatar da na) biyun). Matukar dai ba a samar da dukiya ba; matukar dai kima da girman hakan bai tashi ba, to kuwa babu yadda za mu iya kawo karshen rashi da talauci a cikin al'umma. A saboda haka dukkanin wadannan abubuwa biyu wajibi ne.

Muhimmancin Samar Da Dukiya Da Kuma Raba Ta
Bai kamata a hada wadannan abubuwa guda biyu waje guda ba. Na farko, samar da dukiya. Wajibi ne wani mutum ya gudanar da ayyukansa ta hanyar da ta dace wajen samar da dukiya. Dayan kuma shi ne yadda ake samar da dukiyar da kuma amfani da ita. Bangare na farko na lamarin, abu ne abin bukata; don kuwa duk wata dukiyar da aka samar da ita a cikin al'umma, hakan yana nufin samar da dukiya ga dukkanin daidaikun mutanen wannan al'ummar ne. Bangare na biyu wanda bangare ne mai matukar muhimmanci shi ne yadda za a samar da abin da ake bukatan; bai kamata ya zamanto ta hanyar da ta saba wa doka ba sannan kuma ba ta hanyar magudi da almundahana ba; haka nan kuma wajen amfani da abin da aka samar din bai kamata ya zamanto ta hanyar da shari'a ta hana ba; wajibi ne ya zamanto tamkar yadda jini ya ke yawo a cikin jijiyoyi. Kada a yi amfani da shi wajen yada fasadi.

Samar Da Dukiya
Wajibi ne taken al'umma ya zamanto shi ne samar da dukiya ta fadaddiyar hanyar. Samar da aiki, samar da ilimi, samar da fasaha, samar da dukiya, samar da masaniya, samar da dama, samar da girma da daukaka, samar da kayayyakin da ake bukata da kuma samar da mutane masu kwazo da aiki tukuru. Dukkanin wadannan samar da abubuwa ne wadanda ake bukatarsu.
Tsarin Musulunci yana ganin asalin batun zuba jari da muhimmancin hakan da kuma tunanin samar da dukiya ta hannun masu kudi na cikin gida a matsayin wani lamari mai kyau sannan kuma yana ba da cikakken goyon baya ga hakan. Saboda kuwa hakan zai taimaka wajen ci gaba da daukakar tattalin arziki da samar da aikin yi a cikin kasar nan. Nauyi ne da ke wuyan cibiyoyin gwamnati wajen su tsara siyasarsu ta yadda asasin samar da dukiya - kamar yadda wasu daga cikin ‘yan'uwa suka fadi cewa taruwar dukiya - ta kasance a bangarorin da ake samar da ababen bukata, sannan kuma a tabbatar da adalci ta zamantakewa. Matukar aka rasa ci gaban dukiya a cikin al'umma, matukar dai aka rasa samar da aiki da kuma dukiya, to kuwa daga cikin mutanen da a matakin farko za su fuskanci matsaloli su ne dai bangaren masu rauni da marasa abin hannu musamman ma dai bangaren ma'aikata. Wannan shi ne abin da makiya suke son gani.
Jami'an gwamnati dai su ne suke da nauyi a wuyansu. A wani bangaren wajibi ne su ba da dama ga mutane wajen su gudanar da ayyukan tattalin arziki ta ingantacciyar hanya wacce kuma doka ta amince da ita - saboda kuwa samar da dukiya a mahangar Musulunci ba abu ne abin kyama ba - to sai dai wajibi ne su hana amfani da hanyoyin da suka saba wa doka, amfani da hanyoyin magudi da yaudara da makirci da kuma yin ta'annuti wa dukiyar al'umma. Wadannan abubuwa ne da aka haramta.

Samar Da Dukiya Ba Tare Da Adalci Ba
A kasashen da suka ci gaba ta bangaren masana'antu da dukiya, muna iya ganin cewa ba a iya kawar da talauci ba, ba a iya tabbatar da adalci ba haka nan kuma ba a iya tabbatar da kyawawan halaye ba. Duk kuwa da cewa an iya samar da gagarumar dukiya, to amma an rusa kyawawan dabi'u. A duniyar ‘yan jari hujja, tushen aiki da kokari na tattalin arziki sun ginu ne bisa asasin samar da dukiya ne kawai. A irin wannan tsarin, abin da aka fi ba shi muhimmanci shi ne karfafar tattalin arziki da fadaduwarsa da kuma ci gaban hanyoyin samar da dukiya. Duk yadda za a yi a kara yanayin samar da abubuwan da ake bukata da kuma dukiya, to wannan shi ne abin da aka fi ba shi muhimmanci. A wancan wajen lamarin ba shi ne batun nuna bambanci da samar da tazara tsakanin al'umma ba. Tazarar da ake samu cikin kudaden shiga da kuma rashin yanayin jin dadin da dama daga cikin mutane, wadannan ba abubuwa ne da wannan tsari ya damu da su ba. A tsarin jari hujja, hatta ma a yi batun tsara yadda za a raba irin dukiyar da ake da ita, ba abu ne da ake maraba da shi ba. Tsarin jari hujja yana cewa ne: "Babu wata ma'ana cikin mu ce ku tattaro dukiyar da ake da ita sannan kuma mu raba ta. To ai hakan ba zai tabbatar da ci gaba ba".

Raba Dukiya
Wadanda suke cewa tabbatar da adalci yada talauci ne, kwakwalwa da ruhin wannan magana ta su shi ne cewa kada ma mu yi wani abu wajen tabbatar da adalci; kawai mu ba da himma wajen samar da dukiya, ta yadda abin da za a raba din ya zamnato dukiya ce. Ba da himma wajen samar da dukiya ba tare da adalci ba, to abin da zai haifar shi ne dai wannan abin da a yau muke ganinsa yana faruwa a kasashen ‘yan jari hujja. A mafi arzikin kasashen duniya - wato Amurka - akwai mutanen da suke mutuwa saboda yunwa da sanyi da kuma zafi; wadannan ba wai take ne ba, hakikanin lamari ne da ake ganinsa a kas.
Abin da yake da muhimmanci a wajen tsarin Musulunci a matakin farko shi ne cewa a cikin kasar nan, kowa da kowa ya samu damar amfanuwa da ni'imar da ake da ita. Kada a samu talauci; kada a samu rashi; kada a samu nuna bambanci da wariya; kada a samu rashin daidaito cikin amfani da damar da ake da su; kada a samu rashin daidaito cikin gudanar da doka a tsakanin al'umma.

Ma'aunin Raba Dukiya
A lokacin da batun samar da dukiya ya yi hannun riga da mahanga ta adalci, to kuwa za a kai ga yanayin da a cikin al'umma, mutanen da suka fi wayo a rana guda kawai za su sami dukiya mai dimbin yawan gaske; mutanen da suka fito daga iyalai masu dukiya, akwai su da dama wadanda suke gudanar da rayuwarsu cikin nadama, wasu kuma suna rayuwa mai tsananin wahala. A saboda haka, abin da wasu suke cewa kada ma ku kawo maganar adalci, ku dinga maganar samar da dukiya kawai; su kan fake da cewa bayan an samar da dukiyar sai mu fara maganar tabbatar da adalci, to ai hakan ba abu ne mai yiyuwa ba. Adalci shi ne a raba irin damar da ake da su a cikin kasa cikin adalci da kuma rabon da ya dace da hankali - ba wai adalcin da babu lissafi a cikinsa ba - sannan kuma a yi dukkanin kokari wajen ganin an kara irin wadannan dama da ake da su don kowa da kowa ya kara samun abin da yake samu.


Raba Dukiya A Tsarin Musulunci
Tsarin Musulunci ya yi amanna da a samar da wata al'umma ma'abociyar dukiya, ba wai wata al'umma ma'abociyar talauci da koma baya ba. Ya yi imani da ci gaban tattalin arziki; to sai dai ci gaban tattalin arziki ba shi ne lamari na farko ba wajen tabbatar da adalci na zamantakewa da kuma jin dadin al'umma ba. Abin da ya ke a matakin farko, shi ne cewa kada a samu fakiri a cikin al'umma; kada a samu wanda ba shi da shi; sannan kuma kada a samu wariya da nuna bambanci wajen amfani da damar da ake da ita. Duk wani mutum da ya samar da wata dama, to ta kansa ne. To amma duk wani abin da yake na al'umma ne gaba daya, kamar damar da ake da ita wacce take na dukkanin kasa ne, bai kamata a samu nuna wariya a cikin hakan ba. Bai kamata a dauka cewa manufar tsarin Musulunci ita ce kara irin dukiyar da ake da ita ba, wato wasu mutane su zamanto suna da hanyoyi daban-daban na samar da dukiya, irin abubuwan da kasa take da su su rubanya ba ko kuma dukkanin abin da ake samarwa a kasa su tashi daga mizani kaza zuwa ga wani mizani na daban ba. Ko da yake wadannan wasu siffofi ne, a wani wajen su kan iya zaman abin da zai nuna cewa an kama hanyar isa ga adalci; to sai dai ba haka lamarin yake a ko da yaushe ba.

Asusun Ba Da Lamuni Na Duniya
Bai kamata mutanen da suke cibiyoyin tsare-tsare na kasa ko kuma cibiyoyin ilimi da bincike sannan kuma suke gudanar da ayyukansu a fagen tattalin arziki, siyasa, siyasar kasa da kasa da kuma sauran bangarori daban-daban da suka shafi rayuwar wannan kasa, su sanya hanyoyin kasashen yammaci, hanyoyin tattalin arzikin kasashen yammaci da na bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya a gaba da kuma kokarin tabbatar da su a wannan kasar ba. A'a, wannan mahanga ba mahanga ce da za ta amfani kasar Iran ba. Ko da yake ana iya amfani da iliminsu, a duk inda aka samu ci gaban ilimi da kwarewa za a iya amfani da shi; to sai dai dukkanin abin da za a tsara ya zamanto ya yi daidai ne da tunani da kuma bukatu na kasa.
Mahatir Muhammad, tsohon firayi ministan kasar Malaysiya - wanda mutum ne mai tsananin kwazo da aiki tukuru da kuma kula da doka - ya zo nan Tehran inda ya zo nan muka gana da shi. A lokacin kuwa ya yi daidai da lokacin da abubuwa daban-daban suka faru a kasashen gabashin Asiya; a lokacin girgiza ta tattalin arizki ta faru a kasashen Malaysiya, Indonusiya da kuma Thailand. Wato wadannan yahudawan sahyoniya masu dukiya da sauran masu hannun jari na daban sun gudanar da wasu makirce-makirce na bankuna da kudi inda suka sanya wadannan kasashe cikin mawuyacin hali. A wancan lokacin Mahatir Muhammad ya gaya min cewa: Abin da kawai zan iya gaya maka shi ne cewa a lokacin mun zamanto tamkar almajirai. Ko da yake a duk lokacin da wata kasa ta zamanto mai dogaro ta bangaren tattalin arziki sannan kuma suka yi aiki da irin tsari na tattalin arzikin bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya, to wannan shi ne abin da zai same su.
Shi kansa wannan banki na duniya da asusun ba da lamuni na kasa da kasan wani bangare ne na irin wannan makirci mai girma. Wannan wani lamari ne mai hatsarin gaske a ce asasin sauyin da ake samu a duniya suna hannun ma'abota karfi na duniya ne; wanda haka lamarin ya ke a yau.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din