Duck hunt
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

KIRISTANCI CIKIN JAWABAN AYATULLAH SAYYID ALI KHAMENE'I

Ali Khamenei5

FASALI NA FARKO: ANNABI ISA AL-MASIHU (A.S)

Annabin Allah Mai Girma

Ko shakka babu matsayin Annabi Isa al-Masihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, a wajen musulmi bai gaza irin girma da matsayin da Annabi Isan yake da shi a idon kiristocin da suka yi imani da Kiristanci ba. Wannan babban Annabin Allah, tsawon rayuwarsa ya kasance tare da jama'a wajen gwagwarmaya da zalunci, wuce gona da iri, fasadi da mutanen da suke amfani da karfi wajen bautar da sauran al'umma da jan su zuwa ga jahannaman (wahalhalun) duniya da lahira. Irin wahalhalun da wannan Annabi mai girma ya sha tun daga lokacin yarintarsa - saboda Allah Ya aiko shi a matsayin Annabi ne tun yana karami – ya sha wadannan wahalhalu ne saboda wannan tafarkin.

Annabi Isa, Manzon Allah Mai Girma

Musulmi su ma suna ganin Annabi Isa a matsayin annabin Allah mai girma – kamar yadda mabiya addinin kirista suka yi imani da shi – su ma sun yi imani da hakan. Yahudawa ba za su iya cewa annabi Musa na mu ne kawai, ba shi da alaka da sauran mutane na daban ba; a'a. Dukkanin kiristocin duniya sun yi imani da annabi Musa; kamar yadda dukkanin musulmi suka yi imani da shi. Shi ma annabi Isa haka yake; wato ba wai kawai na kiristoci ba ne; face dai yana da alaka da musulmi. Al'ummar musulmin Iran suna son wannan ma'abocin girma sannan kuma suna girmama shi sosai da sosai. Kiristocin Iran – shin Ashuriyawa ne ko kuma kiristocin da suke yankin arewa da Urumiyeh – sun yi imani da cewa asalin Kiristanci daga can ne. Suna cewa cibiyar Annabi Isa ta kasance a wajen ne sannan kuma Kiristanci a hakikanin gaskiya daga can din ne ya yadu. Mai yiyuwa ne a bangaren tarihi gaskiya tana tare da su.

Maryam Abar Koyi Ce Ga Bil'adama

Alkur'ani mai girma, a lokacin da yake son ambaton ababen koyi ga mutane masu imani, ba kawai cikin mazaje ya ambato hakan ba; ya ambato (misalai) daga cikin mata ma. Allah Madaukakin Sarki Ya ambato sunayen mata guda biyu a matsayin wasu misali biyu na fitattun mutane kuma muminai – ba wai daga cikin fitattun mata ba - . Wato a fagen dan'adamtaka da kamala ta ruhi, a lokacin da Allah Ya ke son yin bayani kan wasu misalai masu kyau, ba ya magana kan annabawa da manyan mazaje da fitattun mutane na ilimi da addini; face dai ya yi magana ne kan wasu mataye guda biyu wanda daya daga cikin wadannan mataye, ita ce matar Fir'auna. Daya macen kuwa, ita ce Maryam mahaifiyar Annabi Isa kuma 'yar Imran. Maryam mace ce matashiya wacce ta tsaya kyam tamkar dutse a gaban irin mummunar tuhumar da ake mata da mummunan aiki da kuma irin wannan mummunan kallo da dukkanin mutanen yankinta suke mata, sannan kuma ta dauki Kalmar Allah da kuma Ruh (Annabi Isa), wanda Allah Madaukakin Sarki cikin karfi da ikonsa Ya sanya mata shi, a hannunta sannan kuma ta gabatar da wannan da nata a matsayin wani haske ga duniyar wancan lokacin da ta cika da duhu.

Sayyida Maryam, Mazharin Tsarki

Akwai wani batu da ke cikin wannan lamari na Maryam wanda kuma a cikin Alkur'ani mai girma ya janyo hankulanmu kansa. Musulmi a mahangarsu suna ganin Sayyida Maryam a matsayin wata alama da mazhari ta tsarki – wato wata mace wacce take tsarkakakkiya dari bisa dari – a cikin Alkur'ani mai girma a wajaje daban-daban an yi magana dangane da Sayyida Maryam: "Da Maryama diyar Imrana wadda ta tsare farjinta, sai Muka hura a cikinsa da RuhinMu" (Suratut Tahrim 66:12). A cikin (wannan ayar) an yi tsananin jaddadawa dangane da batun tabbatar da ismar mace da tabbatar da tsarkin mace dangane da Sayyida Maryam. Wani irin yanayi ne ake ciki? A ganina wannan lamari ne mai tsananin muhimmanci. Na'am; wannan budurwa ta dauki wannan jariri ta shigo da shi cikin wajen bauta don kuwa har zuwa lokacin samartakanta ta kasance ne a wajen. Da wani dalili ne sannan kuma me ya sanya Maryam da dukkan karfinta, da wani karfi wanda ya dara na dan'adam – idan da a ce bai dara irin karfi na dan'adam ba, to da Alkur'ani bai ta jaddada wannan batu ba – ta tsaya kyam a gaban wannan waswasi ta yadda hatta Alkur'ani mai girma yana cewa: "ta tsare farjinta" Ta ci gaba da kiyaye mutumcinta da kare tsarkinta. Wannan lamari ne mai tsananin muhimmanci; darasi ne ga kowa da kowa.
Sayyida Maryam a wannan yanayi mai tsananin muhimmanci ta samu dama ta hanyar irin wannan tsayin daka da gwagwarmaya nata wajen yin tasiri da kuma sauya tarihi; kamar yadda lamarin ya yi kama da wannan a wani wajen na daban, dangane da wani saurayi namiji – wato Annabi Yusuf – kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani mai girma.

Siffofin Da Kissar Isa Dan Maryama (a.s) Ta Kebanta Da su

Ni din nan a duk lokacin da na karanta Suratu Maryam mai albarka ko kuma na saurara – tun daga lokacin samartaka ta har zuwa wannan lokacin haka lamarin ya ke – lalle na kan tasirantu sosai; don kuwa lamarin, lamari ne wanda ya saba wa dabi'a. Lamarin haihuwar Annabi Isa a wancan yanayi na waje da lokaci da hakan ya faru da kuma irin abin da ya haifar cikin tarihi da kuma irin al'ummar wancan lokacin; a lokacin da aka hada dukkanin wadannan abubuwa sannan kuma aka kalle su sosai, za a ga cewa yana da irin wannan girma da daukaka da babu wani bayanin da zai iya siffanta hakan, in ba bayani na fasaha ba.
Lamarin, yana daga cikin lamurra masu tsananin ban mamaki wanda kuma da wuya ake samun irinsa; (wato) rawar da Sayyida Maryam ta taka, rawar da mai girma Zakariyya ya taka, yanayin zamantakewa na wannan lokacin, bayyanar wata rana mai haske a sararin samaniyar samuwar dan'adam da tunanin dan'adam da kuma rayuwar dan'adam – wanda ita ce koyarwar Annabi Isa – sannan kuma bisa la'akari da cewa koyarwar Annabi Isa da koyarwar Annabi Musa babu wani bambanci a cikinsu; wato sun kasance masu kammala junansu da junansu ne. Da dama daga cikin wadannan koyarwar maimaici ne na hakan, to amma ala kulli a wancan lokacin da aka gabatar da ita (koyarwar annabi Isa) mabiya Annabi Musa sakamakon irin gurbata addinin Annabi Musan da aka yi don haka suke ganin hakan a matsayin wata bidi'a kuma kafirci, alhali kuwa daga cikin wannan mabubbugar ce ta fito, tsari da yanayinta duk dai tsari da yanayi ne na koyarwar annabi Musa; wato wahayi ne na Ubangiji. A cikin wannan kissar, a fili ana iya ganin rawar da irin wannan gurbatawa da aka yi da kuma irin amfani da karfi da karkatacciyar fahimta da son kai suka taka a cikinsa.

Madaukin Tutar Shiriya

Wannan kalma ta Ubangiji (Annabi Isa Al-Masihu) a lokacin bata da jahilci da rashin adalci da rashin damuwa da ababe masu kima na dan'adam ya dauki tutar shiryarwa da kuma 'yantar da bil'adama sannan kuma ya ba da dukkanin kokarinsa wajen yada adalci da rahama da tauhidi. A yau wadanda suka yi imani da wannan Annabi mai girma – wato kiristoci da musulmi – idan suna son tabbatar da tsarin da ya dace da duniya, wajibi ne su yi riko da kuma aiki da koyarwar Annabawan Allah sannan kuma su yada falaloli na dan'adam daidai da koyarwar wadannan malaman bil'adama.

Mai 'Yantarwa Daga Zalunci

Annabi Isa Al-Masihu ya kasance ma'abucin mu'ujizozi da kira ta Ubangiji wajen 'yantar da bil'adama daga duhun shirka da kafirci da jahilci da zalunci da kuma isar da shi (dan'adam) zuwa ga hasken masaniyar Ubangiji da adalci da bautan Allah Madaukakin Sarki. Sannan kuma tsawon rayuwarsa bai taba yin kasa a gwuiwa ba wajen fada da munanan abubuwa da kira zuwa ga aikata kyawawan ayyuka. Wannan darasi ne da ya kamata kiristoci da musulmi wadanda suka yi imani da annabcin wannan ma'abocin girma su dauka. A yau bil'adama sama da sauran lokutan da suka gabata suna bukatar wannan koyarwa sannan kuma addinin Musulunci a matsayinsa na mai cika koyarwar Al-Masihun ya sanya kira zuwa ga alheri da kamala a matsayin tsare-tsaren da ya sa a gaba. Batattun mutane sun kasance suna amfani da karfin ilimin da Allah Ya ba su wajen fuskantar wadannan koyarwa ta Ubangiji da sanya ayyukan Annabawan cikin karin wahala. Manyan kasashen duniya da gwamnatocinsu sun kasance suna fakewa da koyarwar Kiristanci, duk da wace babu abin da ya hada su da wadannan koyarwa ta Annabi Isa (a.s), wajen takura rayuwar al'ummomin da ake zalunta, da ci gaba da makure su da hana su numfasawa.

Kira Zuwa Ga Farin Ciki

Wannan annabi zababben Allah, ya kasance yana kiran mutane zuwa ga tafarkin Ubangiji wanda shi ne tafarkin farin cikin bil'adama sannan kuma yana jan kunnensu daga bin soyace-soyacen zuciya da dauda ta zuciya da zalunci da dagawa. Lalatattun masu karfi, masu son amfani da karfi da kuma bautawa zinare da karfi, sun cutar da wannan Manzo na Ubangiji da tuhumarsa sannan kuma suka so kashe shi, to bayan da Allah Madaukakin Sarki Ya kare shi da tabbatar da shi cikin tsaronsa, sun ci gaba da azabtar da Hawariyawa da mabiyansa na tsawon lokaci don su kawar da koyarwarsa da take fada da fasadi da zalunci da shirka da son zuciya da neman tsakona (haifar da yake-yake) da kuma yaudarar mutane. Wadannan mutane wadanda sun kasance lalatattu, azzalumai, masu son zuciya, neman yaki da yaudarar mutane, ba za su iya ci gaba da ganin addinin Allah, annabin Allah da masu bin tafarkin Allah suna ci gaba da wanzuwa ba.

Haihuwar Annabi Isa Al-Masihu

Shekaru aru-aru kenan ake gudanar da bukukuwan haihuwar Al-Masihu (a.s). Me ya sa ranakun haihuwa suke da muhimmanci da kuma kima? Saboda zamantowarsu wani lokaci mai muhimmanci wanda yake ayyana makoma sannan kuma wani lokaci ne mai jan hankali da kuma sauya tarihi. Wato tarihi yana tafiya a kan wata hanya ne, amma a wannan lokaci sai ya kama wata hanya ta daban. Wannan waje da ya kauce da mararraba zuwa ga wani yanki ne na daban.
Mu dai a kowace shekara mu kan aike da sakon taya murnarmu ga kiristocin kasarmu da sauran kiristoci na duniya saboda zagayowar haihuwar Annabi Isa al-Masihu (a.s), to amma da yake bisa ra'ayin mafi yawa daga cikin kiristocin da suke kasar mu na cewa ranar haihuwar Annabi Isa (a.s) ba ita ce ranar 25 ga watan Disamba ba (kamar yadda sauran kiristoci suka tafi a kai), face dai a ranakun goma na farkon watan Janairu – wanda Armaniya ma suna cikin wannan kungiya – a saboda haka ba ma bin hakan, ba ma aikewa da sakon taya murnarmu; mu kan jira har sai watan Janairu ya shigo daga nan sai mu aike da sakon taya murnar don ya yi daidai da kusan dukkanin kiristocin da suke kasarmu. A saboda haka muna fatan zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa al-Masihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, za ta zama mai albarka ga dukkanin kiristocin duniya da kuma dukkanin musulman duniya, insha Allahu. Ala kulli hal, wadannan ranaku goma, ranaku ne na haihuwar mai girma Al-Masihu. Muna fatan dukkanin musulmi da kiristoci za su yi koyi da ayyukan wannan mai girma, su fahimci mai girma Al-Masihu da kyau, sannan kuma su yi riko da shi da bin tafarkinsa.

(Allah Madaukakin Sarki Yana cewa):

FASALI NA BIYU: MUSULUNCI DA KIRISTANCI

Girmamawar Da Annabin Musulunci (s.a.w.a) Yayi Wa Wani Sarki Kirista

Ya zo cikin wani hadisi cewa wata tawaga daga wajen Najashi – wato sarkin Habasha – sun zo wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) a Madina da wani sako; kamar yadda dai aka saba tsakanin gwamnatoci. Najashi ya kasance sarki ne a kasar Habasha, kamar sauran sarakuna da masu mulki na kasashen duniya daban-daban na wancan lokacin, kiristoci da sauran wadanda ba musulmi ba ne; to amma a lokacin da tawagar mutanen Habashan ta iso, sai suka ga shi kansa Annabi (s.a.w.a) ya mike daga wajen da yake zaune ya tafi ya tarbi wannan tawaga da kuma gabatar musu da abin da ya sawwaka na abin ci da abin sha. (Ganin haka) sai sahabbai suka ce: Ya Rasulallah! Ai ga mu nan, ka bari mana mu yi musu maraban. Sai ya ce: a'a, a lokacin da musulmi suka yi hijira zuwa Habasha, sarkinsu ya girmama musulmi da karrama su sosai; ni ina so ne in saka irin wannan karimcin. Wannan ita ce fahimtar gaskiya.

Ibadun Da Aka Yi Tarayya Kansu Tsakanin Musulunci Da Kiristanci

(Allah Madaukakin Sarki Yana cewa): "Hakika an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku"mu dai mun san cewa azumi da zakka ba kawai ta musulmi ba ne, face dai akwai azumi da zakka cikin hukumce-hukumcen annabawan da suka zo kafin Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa).
"Ya yi min wasicci da salla da zakka matukar dai ina raye"wannan magana ce daga wajen Annabi Isa (a.s) da yake fadi wa masu saurarensa cewa: Allah ya yi min wasicci da salla da zakka. Ana iya fahimtar wannan ma'ana ma cikin wasu ayoyin Alkur'anin na daban. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: Azumi tamkar salla da zakka, suna daga cikin ibadun da ba su kebanci musulmi kawai ba; face dai al'ummomin da suka gabata da annabawan da suka gabata ma an yi musu umurni da azumi.

Jawaban Annabi Isa (a.s) Da Suke Cike Da Hikima

Daga cikin ruwayoyin da aka ruwaito su daga wajen Ahlulbaiti, amincin Allah ya tabbata a gare su, akwai wadansu wajaje da suke nakalto maganganun annabi Isa al-Masihu. Wadannan bangarori suna nan cikin dukkanin littafan hadisan Musulunci kuma suna daga cikin bangarorin da suka fi hikima cikin ruwayoyin musulmi. Wadannan maganganu suna cike da hikima da karfi. Kiristoci ba su yi da'awar cewa maganganun Annabi Isa (a.s) su ne kawai wadanda suke cikin Linjila ba. Baya ga Linjilolin da suke hannu, akwai wadansu Linjilolin da yawa, kai maganganun da suke cikin ruwayoyin Musulunci, suna daga cikin bangarori da aka rasa na Linjila. Ala kulli hal maganganun da aka ruwaito su daga wajen Imaman Musulunci, kiristoci su dube su da idon girmamawa; su kasance a wajensu sannan kuma su yi amfani da su. Hakan ma yana iya zama wata hanya ta kusantan juna tsakanin mabiya addinai. Musulmi, suna iya daukan wani bangare na sakon Isa Al-Masihu su mika su a matsayin kyauta ga dukkanin bil'adama. Maganganun Annabi Isa da suka zo cikin ruwayoyin Musulunci, maganganu ne da suke cike da hikima da madaukakan batutuwa. Ko da yake ni dai a shekarun da suka gabata na kan yawaita karanta Linjila; cikin wadannan Linjiloli da suke nan - Linjiloli guda hudu na kiristoci – akwai maganganu da suke cike da hikima a cikinsu. Na'am da gaske ne cewa musulmi a bangaren imani ba su yi imani da wasu akidojin da suke cikin Linjila ba; to amma mutum ya kan yarda da maganganun da suke cike da hikima.

Gano Ababen Da Musulunci Da Kiristanci Suka Yi Tarayya A Kansu

Kokarin soka cikin matasa da tasirin hakan cikin al'umma, tunani ne mai kyau. Addini wata kyauta ce ta Ubangiji, duk kuwa wata al'ummar da za ta iya kusantan mutanenta da wannan kyauta, to kuwa za ta samu abubuwa masu kyau da yawa. Ko da yake mu'amala da matasa, aiki ne mai kyau kuma mai kyakkyawan sakamako.
Akwai abubuwa masu yawa da aka yi tarayya cikinsu tsakanin Musulunci da Kiristanci da kuma tsakanin dukkanin addinan Ubangiji. Ana iya bincike da tattaunawa kan wadannan bangarori da aka yi tarayya a cikinsu yayin gudanar da tarurrukan tattaunawa tsakanin musulmi da kiristoci a wani taro na bangarori biyu ko kuma na bangarori daban-daban. Ba dole ne ya zamanto mahangar wadannan addinai biyu su zamanto kusa da juna, haka nan kuma mai yiyuwa ne ma ya zamanto cewa a gano wajajen da suka yi kusa da junansu. Manufar wadannan tattaunawa ba ita ce tabbatar da gaskiyar wannan addini ko kuma rashin gaskiyar wancan ba; manufar ita ce isa ga inda aka yi tarayya da juna wanda daga dukkan alamu wadannan wajajen da aka yi tarayya din za su hada batutuwa mafi muhimmanci ga batutuwa na rayuwa.

Mahangar Da Aka Yi Tarayya Tsakanin Musulunci Da Kiristanci Kan 'Yanci

Batun 'yancin dan'adam yana daga cikin matsalolin da a ko da yaushe suke fuskantar bil'adama. Mene ne wannan 'yancin sannan kuma ya zuwa ina ne iyakansa yake? A wannan bangaren, addinai suna da abubuwan fadi da yawa, a yau daya daga cikin batutuwan da za su iya zama abin ba da muhimmanci ga addinai – Musulunci da Kiristanci - shi ne dai wannan batu. A yau muna iya ganin wuce gona da irin da kuma gazawa wajen isa ga inda ake son isa a wannan bangaren. A wasu bangarori na rayuwar mutum, 'yan mulkin kama-karya da irin kutsawan da ake iya ganinsu da wadanda ba a iya ganinsu su na hana mutum irin wannan 'yancin da yake da shi. A wani bangare na daban kuma, irin 'yanci masu yawa – wadanda sunansu ba 'yanci ba ne; tashanshi ne kawai – da aka ba wa mutane. A mahanga ta addinai, dukkanin bangarori biyu abubuwa da ake ganinsu a matsayin kauce wa hanya. Dukkanin wadannan addinai na Musulunci da Kiristanci, wajen kore dukkanin bangarori biyu na ‘yanci na hakikan suna da mahanga da suka yi kama da juna. A yau daya daga cikin muhimmin nauyi da aikin da ke wuyan dukkanin mutanen da suke da alaka da kuma kyakyyawan fata ga makomar bil’adama, shi ne su yi fada da fasadi da lalatar da ta zama ruwan dare gama duniya; musamman ma cibiyoyin Kiristanci da suke kasashen Turai – suna da gagarumin nauyi a wuyansu. Da dukkan karfinsu suke yadawa da kwadaitar da fasadi, a saboda haka akwai gagarumar bukatar cibiyoyin coci – musamman cocin mabiyar darikar Katolika – da irin karfin da suke da shi su yi fada da wannan bala'i, wanda ba wai na yau ba ne. Matukar dai cibiyoyin kiristoci da suke Turai suka yi fada da fasadi, to mafi yawa daga cikin mutanen kasashen da ba na Turai ba za su gode muku; saboda wasu daga cikin fasadin su kan tashi ne daga wani waje zuwa wani waje na daban.

Masu Rike Tutar Goyon Adalci Da Wadanda Aka Zalunta

Matukar mazhaba (addini) ta shigo fagen goyon baya da ba da kariya wa adalci da kuma wadanda aka zalunta, to kuwa za a lamunce wani bangare mai muhimmanci na irin wannan jan hankali (na adini). A dukkanin bangarori na duniya matasa sukan ji dadin ganin wani yunkuri na tabbatar da adalci. Tabbatar da adalci lamari ne da ya shafi addinai. Mafi girman jaruman duniyar bil’adama a fagen tabbatar da adalci, jarumai ne na addini. Annabi Isa al-Masihu (a.s) ya gudanar da dukkanin rayuwarsa ne wajen kokarin tabbatar da adalci. Haka shi ma Manzon Musulunci (s.a.w.a) ya gudanar da dukkanin rayuwarsa ne wajen gwagwarmayar tabbatar da adalci. Manyan kiristoci a farko-farkon zuwa addinin Kiristanci, wani irin sadaukarwa ce suka yi wajen tabbatar da adalci. Littafan addini – shin Attaura ce ko Linjila ko kuma Alkur’ani – suna cike da abubuwan da ke kwadaitar (da mutane zuwa) ga neman tabbatar da adalci a cikinsu. A yau ma idan har wannan lamari ya zamanto shi ne taken malaman addini – shin malaman addinin Kirista ne ko kuma na musulmi – ko shakka babu hakan zai janyo hankula. Su ma yahudawan da suke riko da Attaura – ko da yake ba wai muna magana ne kan sahyoniyawa ba; don kuwa su sahyoniyawa ba sa riko da wani abu – su kan su masu neman tabbatar da adalci ne.

Alaka Da Ubangiji Lalura Ce Ta Rayuwar Bil’adama

Dan’adam dai ba zai iya rayuwa ba tare da samun alaka da Ubangiji ba. Misalin hakan kuwa ita ce duniyar ‘yan kwaminis. A wata rana da tsarin markisanci da babu ruwansa da Ubangiji ya rasa irin karfin da yake da shi a tsohuwar Tarayyar Sobiyeti, cocuna sun cika da mutane. Suna tunanin cewa idan har suka dage irin wannan matsin lamba da suka sanya wa mutane, bisa la’akari da farfagandar shekaru saba’in da suka ta yi, to su kansu mutanen ba za su ma nufi inda coci yake ba. Wannan shi ne kuskurensu. Mutane bayan gushewar shekaru saba’in, sun sake komawa coci da riko da shi. A yau idan ka tafi kasar Rasha ko kuma kasashen gabashin Turai, za ka ga cewa cocuna a cike suke da mutane. Kai yunkurin mutanen Poland ma wajen fuskantar markisanci, yunkuri ne na Kiristanci da kuma addini.

Addinan Ubangiji Sun Yi Tarayya Cikin Ababen Da Ke Gyara Ruhi

Addinan Ubangiji, duk kuwa da cewa suna da ‘yan bambance-bambance a tsakaninsu, to amma suna da wasu abubuwa da suka hadu kansu da kuma yin tarayya cikinsu. Mafi muhimmancin abubuwan da addinai suka yi tarayya cikinsu shi ne riko da ababen da suke raya ruhi mutum (wadanda suke kusata shi da Ubangiji); abin da shi ne sakon addini na farko ga bil’adama. Addini shi ne ya kirayi bil’adama cewa kada su takaita kansu ga abubuwan da idanuwansu suke gani ko kuma kunnuwansu suke ji ko kuma jikinsu ya ke tabawa kawai. Ya nuna musu cewa lalle akwai wata hakika da samuwa wacce ta fi dukkanin abubuwan da suke gani ko kuma suke tabawa girma.
A yau ana iya ji da ganin kasantuwar ababen da suke da alaka da addini da kyautata ruhi a cikin al’umma; sai dai mafiya yawa daga cikin abubuwan da suke gudana a duniya suna gudana ne akasin hakan. Idan ya zamana mutanen da suke riko da addinai za su iya kawar da irin wannan gafalar ko da kuwa dan kadan ne, to lalle sun yi gagarumar hidima; nan ne wajen da addinin Musulunci da Kiristanci suka hadu. Tattaunawar da ake yi tsakanin malaman addinai daban-daban ta fi ba da muhimmanci ne kan wannan batun.
Addinai na hakika ba sa kokari wajen nesantar da mutane daga duniya; to sai dai sun yi kokarin fahimtar da su ne cewa dukkanin irin wannan kokari na duniya suna iya zama ne wajen isa ga wani matsayi na ruhi da addini; a saboda haka ne suka juyar da zukata da hankulansu zuwa ga wata hakika mai haske. Gafalar mutum daga wannan hakikar, za ta iya cutar da shi ne, kuma wannan cutarwar ba za a iya kwatanta ta da wata cutarwa ta daban ba. A yau bil’adama suna tsananin fuskantar matsalar wannan gafalar; wato irin gagarumin yunkurin da ake yi a duniya wajen riko da abin duniya, su ne suke gafalar da mutum.

Rikici Tsakanin Kiristanci Da Musulunci

Babu wani rikici tsakanin Kiristanci da Musulunci sannan kuma a nan gaba ma ba za a samu ba. Idan har abin da ake nufi da rikici tsakanin Kiristanci da Musulunci yana nufin rikici ne tsakanin gwamnatocin da suke da musulmi da kuma kirista, to a nan wajibi ne mu fadi cewa ai wannan rikicin ya fi yawa tsakanin gwamnatocin da dukkanin bangarorinsu biyu kiristoci ne. Ko da yake akwai ruhin son haifar da yaki a duniya, wanda hakan abin bakin ciki ne. Sai dai tsawon wadannan shekaru saba’in na baya-bayan nan an gudanar da manyan yakukuwa guda biyu a duniyar kirista, wanda cutarsu ma ya shafi musulmi.
Tsarin Musulunci na Iran yana kiran musulmi zuwa ga hadin kai, wannan hadin kan kuwa ba wai saboda cutar da kiristoci ko kuma sauran mabiyan sauran addinai da sauran al’ummomi ba ne, face dai saboda fuskantar masu wuce gona da iri da ‘yan mamaya da masu son haifar da yaki ne, don gudanar da kyawawan halaye da ababe da suke kyautata ruhi da rayar da amfani da hankali da adalci na Musulunci da ci gaban ilimi da tattalin arziki da tabbatar da daukaka ta Musulunci. Tsarin Musulunci na Iran yana tunatar da mutanen duniya ne cewa a lokacin da Kudus take hannun musulmi a lokacin halifofi, kiristoci da yahudawa sun kasance cikin cikakkiyar kwanciyar hankali da tsaro. To amma a halin yanzu da Kudus ta kasance a hannun yahudawan sahyoniya ko kuma kiristocin sahyoniya, me ya sa suke halalta zubar da jinin musulmi?

Addinin Rahama Da Tausayawa

Musulunci ba ya da nufin fadawa sauran addinai. Musulunci shi ne dai wannan addini wanda a lokacin da ya samu iko kan yankunan da ba na musulmi ba, mutanen wajen sun nuna godiyarsu sakamakon rahama ta Musulunci da suka gani suna masu cewa ku din nan kun fi shugabanninmu na baya rahama da tausayi. A wannan yanki na Shamat, a lokacin da musulmi suka shiga wajen, yahudawa da kiristocin da suke wajen sun gaya musu cewa ku din nan kun fi nuna tausayawa a gare mu. Sun yi mu’ala ta tausayawa da jin kai da mutanen da suke wajen. Musulunci addini ne na rahama da tausayawa; rahama ce ga dukkanin duniya. Musulunci yana gaya wa Kiristanci cewa: “Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitawa a tsakaninmu da ku”(Suratu Al Imrana 3:64). A yi dubi cikin ababen da aka yi tarayya a kansu. Musulunci ba yana fada ne da sauran al’ummomi ba, haka nan kuma ba yana fada ne da sauran addinai ba. Yana fada ne da tursasawa, yana fada ne da zalunci, yana fada ne da girman kai, sannan kuma yana fada ne da neman iko da mamaya. Masu neman iko a kan al’umma da kuma azzalumai da ma’abota girman kai (na duniya) suna kokarin juya hakan ne da nuna sabanin hakan wa duniya. Suna amfani da dukkanin karfin da suke da shi; kama daga (kamfanin shirya fina-finai na) Hollywood har zuwa ga sauran dama da karfin da suke da shi, har zuwa ga makamai da sojojinsu, don su isar da sabanin hakan ga duniya.


FASALI NA UKU: KIRISTANCI A SABON ZAMANI

Al-Masihu A Tsakaninmu

Idan da a ce Annabi Isa Al-Masihu (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana tare da mu a yau, ba zai taba barin fada da azzaluman shugabanni ma'abuta girman kai na duniya ba. Sannan kuma babu yadda zai zuba ido yana ganin wadannan ma'abota girman kai suna bautar da biliyoyin al'ummomin duniya ba.

Hanyar Kutsawar ‘Yan Mulkin Mallaka

Daya daga cikin mafi girman ayyukan ‘yan mulkin mallaka da ma’abota girman kan duniya da ‘yan amshin shatansu shi ne su kawar da akidar fada da gwagwarmaya daga zukatan al’ummomi. A lokuta da dama sun so su kashe wannan fitila mai haske; to amma sun gagara. ‘Yan mulkin mallaka da ma’abota girman kai, sun yi gagarumin kokari a wannan fagen – ba wai kawai a Iran ba, face dai a duk fadin duniyar musulmi – wajen ganin sun kashe wannan fitilar. A cikin wani rahoto mai tsananin muhimmanci da ya shafi shekaru aru-aru da suka gabata, ba wai sabo ba ne, an yi nuni da irin kokarin kiristoci ‘yan Mishan-Mishan din da ake tura su zuwa arewacin Afirka daga kasashen Turai don su je can su share musu hanyar mulkin mallaka. A yankuna daban-daban na Afirka wadanda ma can cikin daji ne mai nesa, amma ‘yan Mishan sun tafi can sun zauna a wajen na tsawon shekaru. Don me suka ci gaba da zama a wajen? Da wani dalili ne suke kokarin kiristantar da kabilun Afirka? Wane ne bai san cewa wadannan mutane su ne masu share fagen mulkin mallaka ba. Sun tafi wadancan wajaje ne suka mayar da mutanen wajen suka zama kirista, don wadannan ‘yan mulkin mallakan su sami damar zuwa wadancan wajajen don gudanar da ayyukansu. Su kansu wadannan fada-fada sun san dalilin da ya sa suke gudanar da wannan aikin na su – lamarin ba wai shi ne cewa ba su san me suke yi ba ne – to amma ku duba ku ga irin wahalhalun da suka sha don cimma wannan manufar, wahalhalun da ko da wasa kudi ma bai isa ya biyan su ba; a matsayin misali mutum ya tafi wani waje da ke makwabtaka da yankin da ake cin mutane ya zauna a wajen na tsawon shekaru bakwai. Mutum ya kan karanta irin wadannan abubuwa cikin littafa, ya kan ga hakan cikin wasu rahotanni, cikin wasu fina-finai da littafan kagaggun labarai, ina da labarin hakan kuma na san hakan da abuwan da suka faru cikin wadannan shekaru a lokacin mulkin mallaka.
Daya daga cikin ababen bakin ciki ga ma’abota addini na duniya shi ne cewa masu karfi da suke iko a kasashen kiristoci shi ne yadda suka dauki tafarkin yada addinin Kiristanci a zahiri a duniya a matsayin wata hanya ta ciyar da yunkurinsu na mulkin mallaka, sannan kuma sun zamanto wasu kayan aikin share fagen mulkin mallaka ga ‘yan mulkin mallakan. ‘Yan misha-mishan wadanda suke tafiya da sunan yada addinin kirista – wanda a zahirinsa yada addinin Kiristanci ne; to amma badinin lamarin shi ne su share fage wa ‘yan mulkin mallakan Turai su taso daga kasashe daban-daban na Turai zuwa kasashen musulmi sannan kuma su kama madafan iko na wadannan kasashen - an tura su zuwa bangarori daban-daban na duniya kuma abin bakin cikin shi ne cewa a fagage daban-daban sun sami nasara.

Karshen Masaniya Ta Addini, Farkon Masaniya Ta Ilimi

A kasashen Kiristanci na Turai, mafarin yunkurin masaniya ta ilimi ya yi daidai da karshen masaniya ta addini kuma a lokaci guda suka kasance tare; wato mafarin wannan marhala yana nufin karshen wancan marhalar. Mai yiyuwa ne ma hakan ita ce gaskiya; don kuwa masaniya ta addini a yankunan kirista masaniya ce da aka gurbata ta, yanayi da ke fada da ilimi gaba daya. A wancan lokacin da a Turai a kan daure wani masani ko kuma a yi masa bulala ko kuma kona shi saboda ya gano wani lamari na ilimi, lokaci ne da ya yi nisa da wannan lokaci na mu. Karnoni da dama an kasance a kan kona masana da sunan mayu ne, a fili a ke iya ganin hakan cikin tarihin ilimin kasashen yammaci. A lokacin da yanayin al’umma da kuma shugabanni da masu gudanar da addini suka kasance suna irin wannan mu’amala da ilimi, to a fili yake kuma a dabi’ance a irin wannan yanayi da kuma al’umma a duk lokacin da ilimi ya samu daukaka to kuwa masaniya ta addini za ta fadi kasa sannan kuma wannan yanayi zai kawo karshe gaba daya; wannan wani lamari ne da yake a fili.
Ko da yake addinin da masanan kasashen Turai suka yi adawa da shi ba, addini ne da bai dace da rayuwar mutane ba; addinin da ke cike da camfe-camfe, wannan addini wanda ya yanke wa Galeileo hukumcin kisa, wani kuma ya azabtar da shi, don kawai sun gano wani sabon abu na ilimi! Ba Kirisanci na hakika ba ne, addinin Kiristanci ne da aka gurbata shi. Babu wata matsala wajen nesantar irin wannan addinin; matsalar tana cikin nesantar ababen da suke kyautata ruhi ne da kusata mutum zuwa ga Allah da kyawawan dabi’u daga ilimi da siyasa da tsarin rayuwar mutane ta daidaiku da kuma ta al’ummance.

Wadanda Ba Su Yi Imani Da Kiristanci Ba

A yau bai kamata wani yayi shakka kan yadda mafi yawa ko kuma dukkanin manyan kasashen yammaci suke kokarin yada wannan akida ta salibanci (adawa da Musulunci da kokarin yakansa) a duniya ta hanyar fakewa da demokradiyya da hakkokin bil'adama ba. Wauta ne ma idan muka yi tunanin cewa irin rashin imanin da ake yi a Bosniya (a nan Jagoran yana ishara ne da irin ta’addancin da ‘yan ta’addan kiristocin Sabiyawa masu makami suka yi wa musulmi a kasar Bosniya ne a wancan lokacin) da sauran wajaje da cewa ya samo asali ne daga irin koyarwa ta annabi Isa. A yau a fili yake kuma kowa yana ganin yadda wadannan mutane suke adawa da kuma gaba ta koli da duk wata alama ta Musulunci da duk wani ci gaba da musulmi za su samu, ko shakka babu wadannan mutane ba su yi imani da Annabi Isa al-Masihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma koyarwarsa ta hakika ba. Abin da suka yi imani da shi shi ne kawai tabbatar da karfinsu da biyan bukatun bakaken manufofinsu na zalunci, da kuma adawa da duk wani karfi da zai yi wa irin zaluncinsu barazana, da wadannan abubuwa ne suka yi imani, bayan haka babu wani abin da suka yi imani da shi. Amma hannayensu da suke jike da jini sun shirya sahun fada da Musulunci, sannan kuma sun daga tutar fada da Musulunci a matsayinsa na wani addini da akida da kuma imani.

Tushen Adawa Da Ababe Na Addini

A irin wannan duniya da take da irin wannan siffa (ta riko da abin duniya da kuma watsi da ababe na addini da lahira), ne aka samar da tsarin jamhuriyar Musulunci da ya ginu bisa tushen ababe na addini. Wannan shi ne abin da ke da muhimmanci. Kai hatta ma batun cewa wannan tsari na Musulunci ne ko kuma na Kiristanci wannan lamari ne da ke a mataki na biyu. Abin da ke da muhimmancin shi ne tushen adawa da addini da rashin imani, wanda dukkanin matakan da ake dauka a duniya – hatta matakin da malaman duniya suke dauka – a wannan fage ne, a kawar da shi. Hatta malaman duniya sun kasance suna tafiya ne a kan tafarkin rashin imani da addini! Ku dauka a matsayin misali majami’a ta yi wani irin tsari wanda zai ja hankulan matasa, ko da kuwa ta hanyar samar da wani gidan rawa ne da ke da alaka da cocin kuma tare da cocin, wani irin abu ne zai fado cikin zuciyar wani kirista a duniya da jin cewa ya ya za a yi malaman coci su aikata irin wannan aikin sannan kuma yanayin ya zamanto haka?
Daya daga cikin sanannun marubutan kasashen larabawa ya rubuta cewa: “Da idanuwana na gani a wata rana da dare a wani gidan rawa da take da alaka da coci, na ga wani fada ya zo wajen. A lokacin ma’aurata matasa suna ta taka rawa. Sai ya duba ya ga shin komai yana bisa tsari ko kuma a’a? A matsayin misali shin fitilun da aka sanya a wajen suna da yawa. Da hannayensa ya dinga tsara wadannan fitilu don rage irin haske da yake shigowa wajen. Daga nan kuma sai ya gaya wa mai kula da cocin cewa a duk lokacin da kowa ya tafi, ya rufe kofofin wajen. Daga nan kuma sai ya kama hanyar wajen kwanansa don ya huta”.
Wannan marubucin larabawan sai ya ci gaba da cewa: “Washegarin wannan dare ko kuma washegarin washegarinsa, sai na tafi wajen wannan malamin kiristan na ce masa Ya kai wannan fada! Tamkar dai yanayi ya sauya? Sai ya ce a’a. Kai aikinmu ma ya zamanto na siyasa ne don mu janyo hankulan matasa zuwa ga coci ne! shin ba ka ga irin adadin matasan da suka zo cocin ba ne? Da kyau, hakan yana nufin komawa ga tafarkin nesantar ababe na addini, hatta a fagen malamai. Wannan malami, malamin kirista ne. Akwai yiyuwar a samu irinsa cikin malaman Musulunci ma – shin Shi’a ne ko kuma Sunna –.
A cikin irin wannan yanayi da lokaci na tarihi, kwatsam wani lamari ya kan iya faruwa sannan kuma a samar da wani tsari wanda ya ginu bisa asasi na addini. Wannan tsari, ya kawo addini a fagen rayuwa, sannan kuma hukumarsa, yakinsa, kasafin kudinsa da siyasarsa duk sun fito ne daga tushen wannan addini. Mai yiyuwa ne ana iya cewa: Bayyanar irin wannan tsarin, in ba a dan wani lokaci ba, ba a taba ganin irinsa ba a duniyan nan. Ko da yake hukuma ta addini da ma’ana ta musamman ta hukuma ta addini, a ko da yaushe a kan samu irinta a bangarori daban-daban na duniya – mafi yawansu a duniyar Kiristanci ne. To amma tsari da hukuma ta Musulunci ta Iran ba irin wancan tsarin ba ne. Wadancan hukumomi, a hakikanin gaskiya hukumomi ne na masu addini da malamai, amma ba hukumomi ne da suka ginu bisa koyarwa ta addini da ababe da suke da alaka da addini ba.

Halin Ko In Kular Majami’a Ga Rashin Adalcin Da Ke Faruwa A Duniya

A yau cibiyoyin Kiristanci sun zamanto masu nuna halin ko in kula dangane da batutuwa masu muhimmanci na bil'adama. A yau akwai rashin adalci a fagen duniya; wani abu Kiristanci yake yi wajen fada da hakan? Suna magana kan sulhu! Suna rera taken sulhu ga bil'adama, to wannan take ne mai kyaun gaske, to amma hakan bai isa ba. Wajibi ne gefen irin wannan take na sulhu, a samu taken tabbatar da adalci a tare da shi. A yau bil'adama sun kasance fursunonin rashin adalci. Akwai manyan kasashe masu karfi da suke zaluntan mafi yawa daga cikin bil'adama.
Turawan kasashen turai su da kansu sun haifar da manyan yakukuwa, daga nan kuma suna rera taken sulhu! A halin yanzu ba a wuce 'yan wasu gomomin shekaru ba da gama wadannan yakukuwa, amma suna amfani da taken sulhu a matsayin abin fakewa (don cimma manufarsu). Alhali kuwa taken da bil'adama suke bukata a halin yanzu shi ne adalci! Amma ko da wasa ba sa ma rera wannan take, haka nan kuma cibiyoyin Kiristanci da shi kansa Paparoma suna ci gaba da ganin hakan, ba sa yin wani abu. Ko da wasa tsarin Musulunci na Iran bai yarda da irin matsayar da shugabannin coci-coci suke dauka dangane da kasashen yammaci da ma'abota girman kai na duniya ba; nauyin da ke wuyansu ya fi abin da suka yi girma. Ni dai na aike wa Paparoma da sako ina gaya masa da ya yi riko da adalci. A yau sakon addinai, shi ne tabbatar da adalci; kamar yadda take da sakon Annabi Musa da Annabi Isa da Manzon Musulunci ma su ne wadannan.


Sakamon Nesantar Koyarwar Al-Masihu

Turawan kasashen turai dai ba kasafai suke magana kan addini ba amma Amurkawa kan suna yawan nuna riko da addini da zahiri na addini da sunaye na addini da ambaton addini, sun yi imani da coci; to amma suna da wata alaka ta amawa da rashin tunani da wani irin kallo wa addini. Wadannan mutane ba sa ganin akwai wani karo da juna a matsayin misali tsakanin ko su yi tawassuli da annabi Isa ko kuma Sayyida Maryam su nemi bukatarsu; amma a bangare guda kuma suna aikata gomomin zunubai da suka saba wa koyarwar Kiristanci. Bugu da kari kuma, babu wata hikima ko wani dalili na irin wadannan neman taimako da dauki da suke yi. Tushen Kiristanci – bisa ga abin da ya shahara – ya ginu ne bisa tushen soyayya da sulhu. Amma ku duba ku gani a kasashen yammaci mafi yawan yakukuwa, kiyayya, rashin kaunar juna, ha'inci, kisan bil'adama da munanan laifuffuka suna faruwa; ala kulli hal kuma akwai imani da Kiristanci a wajen. Mai yiyuwa ne tushen irin wadannan al'adu sun ginu ne bisa rabuwa da addini da ta faru a baya. Bisa ga kididdigar da su kansu suka fitar, suna bayyana cewar shekarun mutanen da suka kamu da dabi'ar shan muggan kwayoyi sai kasa suke yi – a wani lokaci a baya shekarunsu sha takwas ne, daga baya kuma ya zama shekaru sha biyar, a halin yanzu kuma sun zamanto 'yan shekaru sha uku – da irin wannan nisabi, muggan laifuffuka da nuna halin ko in kula da rashin damuwa da gidajen iyaye da al'adu suke faruwa. Wannan sakamako ne na wannan rabuwa da addini. Abu ne mai yiyuwa a matsayin misali wadanda suka mallaki karfi ilimi da fasaha ta nukiliya amma su zamanto ba su yi wani amfani mai cutarwa da shi da kashe jama'a ba. Matukar dai wadannan mutane da suke da irin wannan karfi da kwarewa sun yarda da kuma girmama tushen kyawawan dabi'u da addini sannan kuma suka zamanto ma'abota imani, haka lamarin zai kasance; amma sakamakon rashin hakan wani irin bala'i ne zai fada kan al'ummomi. Tun daga kirkiro da kuma amfani da makamin nukiliya a duniya kimanin shekaru hamsin kenan; to amma har ya zuwa yanzu tsoron kasantuwan makaman kare dangi a duniya ga wadanda suka fuskanci cutarwar wadannan makamai har ya zuwa yanzu yana nan a raye a zukatansu, a nan gaba ma hakan zai ci gaba da karuwa; daga dukkan alamu ba zai ragu ba.
A nan baya kadan daya daga cikin cibiyoyin kiristocin duniya ta gabatar da wani rahoto da kididdiga da ke nuni da cewa an fi kashe kiristoci cikin wannan karni na baya-bayan nan, sama da dukkanin lokutan Kiristanci da ya gabata. Ni dai ina son in gabatar da wannan tambaya ga wadanda suka gabatar da wannan kididdiga cewa waye ya kashe wadannan kiristocin? Shin musulmi ne suka kashe su? Shin 'yan Budha ne suka kashe su? Ko kuma su kansu kiristoci ne suka kashe su? Wasu mutane ne suka kashe mutanen Turai a yakin duniya na farko da na biyu? Su kansu kiristocin ne suka kashe su. Su kansu mutanen Turai din ne, su kansu mutanen yammaci din ne suka kawar da su sannan kuma sun kashe da dama daga cikin wadanda ba kiristoci da wadanda ba turawa ba.
Nesantar abubuwa masu kusatar da mutum zuwa ga Allah a wajen bil'adama lamari ne mai cutarwa sosai. Tsarin Musulunci na Iran yana so ne ya gabatar wa duniya da misali da a aikace zai tabbatar wa duniya cewa ana iya neman ilimi da kuma samun ilimi sannan kuma a amfana sosai da kyaututtuka ta Uabngiji ga duniya da kuma samuwar dan'adam sannan kuma a ci gaba da riko da addini da ababe masu kima na kyawawan dabi'u.

Da'awar Karya

A yau da dama daga cikin mutanen da suke da'awar bin Annabi Isa, amma suna tafiya a kan tafarkin da ya saba wa na Annabi Isa din. Shiryarwar Annabi Isa dan Maryam amincin Allah ya tabbata ga annabinmu da kuma a gare shi, shiryarwa ce zuwa ga bautar Allah da kuma fada da fir'aunanci da girman kai. A yau mutanen da suke ikirarin bin wannan babban Annabin Allah mai girma, suna zaune a kujeran fir'aunanci da girman kan da Isa dan Maryama ya yaka.
Masu karfi na duniya suna ambaton sunan Kiristanci sannan kuma a zahiri suna bayyanar da imaninsu da Kiristanci; amma babu wani labarin ma'anar Kiristanci da matsayinsa na addini na Ubangiji da kyawawan dabi'u na Ubangiji cikin cibiyoyi na siyasa masu mulki a kan duniyar girman kai - duniyar zalunci, duniyar girman kai da ma'anarsa ta hakika, duniya wuce gona da iri da kuma duniyar da ake amfani da ilimi wajen aikata dukkanin irin wannan munanan ayyuka da laifi - . A yau ilimi yana hannu wasu mutane ne da ba su ma shaki kamshin dan'adamtaka ba. Ilimi da fasaha suna biyan bukatun wasu manufofi ne wadanda dari bisa dari suna cutarwa ne ga al'ummar bil'adama da kuma amfanar 'yan jari hujja da masu kudi da ma'abota karfi.


FASALI NA HUDU: JAMHURIYAR MUSULUNCI TA IRAN DA KIRISTOCI 'YAN TSIRARU

Tasirin Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ga Duniyar Kiristanci

Juyin juya halinmu, ba wai kawai ya janyo musulmi zuwa ga tunani kan Musulunci ba ne, face dai ya kasance abu mai kyau ga Kiristanci ma. Kasashen da shekara da shekaru suka nesanci addinin Kiristanci duk kuwa da cewa addininsu ne, sun komo bangaren ababen da suke kyautata ruhi da kuma addini. Hakan shi ne ya zamanto share fagen faduwar mulkin mallakan gabashi da tushen hukumar markisanci a duniya. Wannan wani irin lamari ne mai ban mamaki sannan kuma wasu irin bangarori masu girma yake da su.
Irin matsayi na musamman da jamhuriyar Musulunci take da shi saboda irin tsayin dakan da ya yi ne a gaban ma'abota karfin da suka dogara da karfi na duniya – wadanda babu ruwansu da wata hakika ta kyawawan halaye da addini – sannan kuma ta yi nasara a kansu.


Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Tsakanin Mabiya Addinai A Iran

Abin farin ciki shi ne cewa akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin mabiya addinai daban-daban a cikin tsarin jamhuriyar Musulunci ta Iran; yahudawa, kiristoci, mabiya addini Zoroasta; dukkanin wadannan suna rayuwa tare da musulmi karkashin inuwar tsarin Musulunci; suna mu'amala da kuma ba da hadin kai wa wannan tsari sannan kuma suna ba da tasu gudumawar. Ko da yake suna da wani nauyi da ke wuyansu; ita ma gwamnatin Musulunci tana da nata nauyi a kanta dangane da su a matsayinsu na 'yan kasar Iran, wanda wajibi ne a sauke wannan nauyi da kuma yin aiki da shi, kuma tana yin hakan. Gwamnatin Musulunci (ta Iran) ba ta da wani korafi dangane da 'yan kasar mabiya sauran addinai. A duk lokacin da makiya suke ta yada wata farfaganda don bakanta Jamhuriyar Musulunci ta hanyoyi daban-daban, mabiya sauran addinai sukan fitar da sanarwar (yin Allah wadai da hakan). A wasu batutuwa da suka taso Armaniyawan Iran ko kuma wasu kungiyoyi na kiristocin sukan fitar da sanarwa da kuma nuna goyon bayansu ga Jamhuriyar Musulunci. Hakan kuwa yana daga cikin abubuwan alfahari na Jamhuriyar Musulunci.

'Yan Kasarmu Kiristoci

Wannan jawabi ne da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i ya yi a yayin ganawarsa da Babban Fadan Armaniya da Wakilan Armaniya a majalisar shawarar Musulunci ta Iran.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Bisa la'akari da cewa 'yan'uwanmu kiristocin da suke kasar nan suna da kwanciyar hankali da farin ciki sannan kuma suna ci gaba da zama cikin 'yan'uwansu da kuma gudanar da aikinsu (cikin kwanciyar hankali) hakan yana faranta mana rai kuma hakan ne muke so. Mu dai muna so ne mabiya sauran addinai da suke kasarmu, da suka hada da kiristoci da yahudawa da mabiya addinin Zoroasta su ji cewa lalle suna da kwanciyar hankali da kuma samun hakkokinsu na 'yan kasa; kuma alhamdu lillahi hakan ya samu kuma kuna ganin hakan. Muna nuna godiya da kuma farin cikinmu saboda irin nuna damuwa da alhinin da kuka yi dangane girgizar kasar da ta faru a garin Bam. A dabi’ance haka lamarin yake. A lokacin kallafaffen yaki na shekaru takwas, kiristoci Armaniyawa sun taka gagarumar rawa a bangaren taimako na kayan aiki, saboda kuwa Armaniyawa na Tehran da sauran yankuna suna da kwarewa a fagen makanikanci da kere-kere. Ni dai a kurkusa tun ma kafin nasarar juyin juya halin Musulunci ina da masaniya kan ayyukan Armaniyawa, ina sane da cewa suna da kwarewa a fagen gyaran motoci da kayayyakinsu. A lokacin yaki ma sun zo suka ce mana, mu dai a shirye muke mu gudanar da aiki. A shekarar 1359 ko kuma 1360 sun zo sun kafa sansani a Ahwaz; ni ma na tafi na gudanar da rangadi a wajen. A wani lokaci ma mun kasance mu kan taso daga Tehran mu tafi Ahwaz, na ga kimanin Armaniyawa dari sun zo suka ce mu dai a shirye muke mu tafi fagen daga; ku dauke mu ku kai mu fagen daga. Na ce a sanya su cikin jirgin sama a kai su fagen daga. A saboda haka ba abin mamaki ba ne a wajen don kun nuna irin wannan damuwa taku dangane da girgizar kasar da ta faru a (garin) Bam. Ko da yake ni dai ina da alaka ta kurkusa da wasu daga cikin iyalan (kiristocin) Armaniya da Ashurawa a Tehran sakamakon shahadar ‘ya’yansu a fagen daga, na kan tafi gidajensu, mun san juna; na san irin shu’urin da suke da shi, shu’uri ne mai kyaun gaske.
Muna rokon Allah da ya ba ku da kuma mu dacewa wajen tafiya a kan hanyar da ta dace. Muna fatan Allah zai sanya dukkaninmu cikin rahama da shiriya da tausayawarsa. Ku isar da sakon taya murnarmu ga sauran ‘yan’uwa Armaniyawa saboda shigowar sabuwar shekara da kuma haihuwar Annabi Isa Al-Masihu, amincin Allah ya tabbata a gare shi. Ina rokon Allah da ya ba ku dacewa.

Nuna Kauna Da Kusanci

Ni dai ina nuna kauna da kusanci na ga Armaniyawan Iran. Mu dai muna son kiristoci. Kiristoci Armaniyawa a lokacin juyin juya hali da kuma yaki, sun taimaka mana sosai. Tabbas kun ji hakan; to amma ni a kurkusa na ga hakan. Ni a fagen yaki – a fagen daga – na ga Armaniyawa da yawa wadanda cikin tsarkakkiyar zuciya da nuna kauna cikin ruwan bama-bamai da igwa-igwa suke taimaka mana. Ko da yake hakan, bai hada ne da mutanen da suka kasance masu bautan kasa ba; wadannan mutane na gari wadanda cikin radin kansu suka kai kansu (fagen dagan).
Mu dai muna mu’amala ne da sauran mabiya addinai ‘yan tsiraru tamkar ‘yan’uwanmu (musulmi). Kai ba ya ma zuwa mana cikin tunaninmu cewa wane – a matsayin misali – yana bin wani addini (ko mazhaba) na daban ne wanda kuma a bisa al’ada bai yarda da addininmu da Musuluncinmu ba! Kai mu kan je gidajensu ma. Ni dai shekara da shekaru kenan a lokacin bukin sabuwar shekarar kiristoci, a mafi yawan lokuta na kan tafi gidajen shahidan kiristoci. Shi kuwa wanda nake zuwa gidan nasa Ba’armane ne ko kuma Ba’ashure. Mu kan tafi gidajensu; mu kan zauna tare da matayensu, ‘ya’yansu da matasansu; mu kan tattaunawa sannan kuma mu ci kayayyakin zaki da na marmarin da suka kawo.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din